Sashe 49
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zo za a kai Huda. Barka Alhamdulillah. Auwal sai ya warke ai yanzu iri mai ciwon so. Dariya duk suka yi har da Granpa kafin Granpa d in ya ce Yanzu abunda zai faru shine.. Ku fara shirye shiryen visar har da na ita matar Auwal d in, Yahaya ka kirawo Kakan ta ka sanar da shi cewa Duba da yanayin halin da Mijinta yake ciki muna so mu tura mishi ita da wurwuri! At least a samu ya warke da wuri ja irin. Dariya duk suka yi nan ma kafin Granpa ya ce Sai ta wuce as soon as possible mu kuma idan mun yi welcomin Maryam sai mu wuce da washe gari ko? Ya fad i maganar yana dafa kafad un Gramma. Murmushi kawai ta yi ta sunkuyar da kanta dan duk sai ta ji ya bata kunya. Daddy ne ya ce Inyeee.. Grand honeymoon za..... Bai k arasa ba Gramma ta d auko throw pillow ta buga mishi! Da sauri suka mik e suka fita shi da Dad suna dariya. A hankali Gramma ta kwanta a jikinsa tana sauk e ajiyar zuciya kafin ta ce Thank you Daddie Murmushi kawai yayi yana me shafa kanta a chan k asan zuciyarsa kuma yana regretting abubuwan da ya yiyyi.. ashe haka happines d in frank family life yake amman ya dinga depriving kanshi da zuri arsa ba tare da ya sani ba? Tabbas miskilanci da mugun hali bashi da rana.................... BULAMA Bismillahirrahmanirrahim So da Buri Free Book Barkanmu da sallah Al ummar Musulmi Allah ya maimaita mana, Ameen. Abba Madu yana gama waya da Dad Motar su Baban Sakina tana yin parking. Sai da Baban Sakina ya raka su har ciki tukunna ya ce Bari ya je ya samu d an uwanshi ya sanar da shi halin da ake ciki. Yana fita su kuma suka fara korawa Shuwa bayani Har ga Allah Shuwa ta ji dad in hakan..at least su duka ukun za su zauna a family d aya. Basu damu da gyangyad i da jirin da take yi ba (dan allurai da abun da Ashraff ya shak a mata masu k arfi ne sosai) Haka suka duk ufa wajen gyarata Ita kam anayi ma tanata baccin ta. Sai dare tukunna Huda ta samu ta kira Mama Gramma Ummu da Abba ta gaidasu. Suna gama waya da Abba ta fara jiyo motsi dan haka tayi sauri ta runtse idanuwanta kamar mai bacci. Dama ya bata dinner ta ci ta yi sallah tukunna ya fita bayan ya ce mata bara ya je ya d an yi aiki Dan in dai yana gabanta to ya san ba abunda zai iya tab ukawa. Yana ganin yadda ta lumshe idanun nata ya fahimci ba bacci take yi ba! Murmushi kawai ya yi ya k arasa y an abubuwan da zai yi ya hayo kan gadon. Tashi d aya ya lura da yadda jikinta ya hau b ari dukda kuwa baccin k aryar da take shararawa amman he cant help it! Ba k aramin k ari ma ya yi aka kawo yanzun ba. Addua ya yi ya tofa ya shafa mata shima ya shafa. Jin an shafa mata addua ya sanya hankalinta yad an kwanta a tunaninta kyaleta za ayi amman inaa nan take ta ji sabon labari Babu daman kwacewa dan yau ma Aslam d in da gaskensa ya zo mata kamar jiya. Babu kalar magiyar da bata yi amman yayi mata kunnen uwar shegu! Ga rad i ga azaba ga ciwon kai ga rashin bacci shiyasa kafin asuba zazzab i ya rufeta, ruf!. Shi ya kira family Doctor ta zo da sassafe ta yi mata allurai harda k arin ruwa tukunna ta d an ji dama dama Ba abunda yafi bata tsoro irin yadda ya sake zuwan mata yauma kamar jiya da shekaran jiya. Ita kam har mamaki da tsoro ya fara bata dan idan yana wani abun kamar wani mai aljanu..yanzun zaka ganshi garau amman yana d aukar hanya zai birkice sam baya ji baya gani. Bashi da aiki sai dai ya bata abinci ya yi ta lallab ata yana faman lallashinta yana kula da ita, ya yi ta gaya mata kalaman soyayya yana lallashinta Idan dare yayi kuma a koma ruwa...... Tun a washegarin ranar aka shirya musu komai na tafiya. Basu wani sha wahalar yiwa Sakina komai ba saboda Dad ne akan komai. Auwal, bai san da labarin ba dan ko da aka gayawa Mom da ta ga jikin nasa yad an nutsu kamar ya sani sannan nan da kwana biyu Sakinar zata zo sai kawai ta barshi akan sai ta zo d in ya ganta kawai a surprise Another thing kuma tana tunanin in dai Auwal ya ji an aura masa Sakina kuma tana Nigeria tou tabbas zai iya tsige oxygen d in ya dawo gida ko bai gama warkewa ba..... Tun lokacin da aka ce visar su ta fito gobe zata wuce Take kuka! Har yau da safe..Shuwa da su Baaba Talatu da Ummu ne sai kuma matar wan Mijin Ummu sai wata distant cousin d insa, suka shirya za su kaita MT. Suna cikin shiri Anty Zainab ta shigo ita da su Khadija waenda zuwansu kenan. Da mamaki Mama take kallon Anty Zainab d in wadda duk ta rame ta lalace jikinta yayi mugun sanyi kamar ba itaba ko dan ta jima bata ganta ba dan ko ranar da Kaka ya kirata ta je bata ganta ba tana d aki wai tana bacci. Inda Mama take Anty Zainab ta nufa tana zuwa ta rungume ta sai kuma ta fashe da kuka!. Duk tsayawa suka yi suna kallonta da mamaki. A hankali Mama ta zaro ta daga jikinta kafin ta ce Haba Zainab kuka kuma? Cikin share hawayenta ta ce Dole in yi kuka Maryam! Dole in yi takaici da bak in cikin abubuwan da na aikata.. Na yi miki laifi na yi kuskure wanda a yanzu nake matuk ar danasani, sam! Na kasa nutsuwa na kasa yafewa kaina. Sai da ta share hawayenta wasu suna sake zubowa tukunna ta d aura da cewa Yanzu haka daga gidan me unguwa nake..na je na fad a masa gaskiyar laifin da na yi miki sharrin da na yi miki wanda yayi sanadiyyar har aka koroki a makaranta.. Na gayawa Kaka shima gaskiya. Ki tayani neman yafiyar Abba dan Allah Maryam kema ki yafe min na yi kuskure Sadiya ta cuceni! Wallahi duk hud ubarta ce ta sanya na juyawa aminiyata baya Ta k arashe maganar tana fashewa da wani sabon kukan. A hankali Mama ta yi hugging d inta tana murmushi kafin ta ce Zainab! Har ga Allah ba zan ce miki zan iya mantawa da abunda kika yi mini ba a lokaci guda ba, dan zan iya cewa ke ce ummulabaisin fad a na da su Abba. Amman maganar yafiya kam wannan na yafe miki Allah ya yafe mana gaba d aya. Sanna ki yi k ari ki yafewa Sadiya itama ko ba komai kar abun ya yi mata yawa saboda ko da bakin y an layi aka barta ya isheta! Dan kowa idan ya tashi magana ita, kowa matsalarsa Sadiya Idan mu bamu yafe mata mun yi mata fatan alkhairi ba wa zai yi? Wani sabon kukan Anty Zainab ta fashe dashi tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Mama. Da kyar su Shuwa da Ummu har Maman suka samu suka lallasheta ta nemi waje ta zauna tana gunjin kuka. Basu kai ga fara magana ba Madu ya shigo ya ce Su fito da Sakina ga motocin MT sun k araso Sai a lokacin ta saki kukanta mai sauti Haka nan tana kuka tana komai Mommy da Mammy suna shigowa aka d auketa aka fita da ita. Tana shiga motar motocin suka d auki hanyar MT. angaren Gramma aka ajjiyeta. Hudan, daman ta san da zuwan nasu dan basu ma dad e da gama waya da Sakinar ba, shiyasa tana jin shigowar motoci ta lek a ta sama da yake gidantane a farko farko yasa ta hango su. Tama manta da ciwon kafa da na jikin da take yi Haka nan tana takawa tana d an d ingishi ta nufi hanya.. Da kyar ta iya sauk a daga benen farko kawai sai ta durk usa a wajen ta saki kuka A haka Aslam ya shigo ya sameta. A rikice ya k arasa ya hau tambayar ta me ya sauk o da ita? Ko kallon sa bata yi ba ta mik e kawai ta fara k arin wucewa wanda sai a lokacin ne ya gane matsalarta Dariya da tausayinta ne suka rufeshi amman ya dake ya b ata rai ya ciccib eta. Duk kalar rigima da yakushin da take yi mishi da kuka bai diretaba sai da ya kaita kan gadon tukunna. A hankali ya zauna ya kamo hannunta tana shirin mik ewa ya ce Ki nutsu. Kin san dai Sakina ba zata tab a wucewa ba tare da ta zo ta yi miki sallama ba ko? Ki kwantar da hankalinki yanzu ma da na ajjiye su na ji suna cewa duk za su shigo miki kafin su wuce Shiru ya yi yana kallonta still kafin ya ce Yanzu ke idan aka barki a haka a wannan yanayin naki za ki je gaban su Ummun? Sai a lokacin kanta ya d an d au chaji. A hankali ta sunkuyar da kanta kafin ta ce Ya Aslam tou dan Allah ka je ka taho da su, kar su k i zuwa. Sai da ya d an yi shiruu tukunna ya kamo hannunta ya rik e ya d anyi kisssing sannan ya ce Okay love, amman ki nutsu kin ji an d aga masa kai ta yi alamun okay Ya d an jima yana kallonta yana murmushi kafin ya sauk e ajiyar zuciya a hankali ya ce Alhamdulillah tukunna ya mik e ya fice a ranshi yana tunanin ta yadda Hudan take so ya je ya sake fuskantar su Ummu! Shi fa da kyar ma ya iya tsayawa suka gaisa especially ma Mama lokacin da ta rako Sakina har k ofa, wata irriyar kunyarsu yake ji gaba d ayansu. Shi kam gaskiya idan Mama ta k araso estate d inma bai san taya za su kaya ba. Cikin ikon Allah yana sauk