Sashe 11
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kuka yi dan yadda Granpa ya rufe ido ya gurzawa Aslam to wallahi kowa ya kuka da kanshi. Yana gama fad in haka ya wuce ya nufi side d insa Tunda Mom take a estate d in nan bata tab a jin farin ciki irin na wannan ranar ba! Dan har goshinta ta saka a k asa tayi sujjada bayan wucewar Auwal Arshaad ya gudu Aslam kuma sun yi fad a shi da Granpa in sha Allah ll make sure it stays like this har izuwa lokacin da za a mallakawa Auwal d inta MT!.. angaren Jalila kuwa ba k aramin k ari tayi ba wajen hana kanta kurma Ihun murna! Bayan ta doka wani uban tsalle, sannan ta fara juyi tana tik ar rawa. Sai da ta lek a taga Mom bata parlourn tukunna ta fito tab wuce d akinta a ranta tana Wato idan kana da uwa a duniyar nan ba wanda ya kaika gata! Tana shiga d akin bata yi wata wata ba ta d auki wayarta ta fara kiran Umma Tana d aki a zaune tana goge wa Ya Ja afar jiki kiran Jalila ya shigo auka tayi ta saka a speaker ta ajjiye a gefe, za ta cigaba da abunda take yi. Ko gaisuwa babu Jalila tace Ummana albishirinki Da sauri ta ajjiye towel d in hannunta ta d au wayar jiki na rawa tace Goro Nan Jalila ta shiga zayyano mata kaff abunda taji ta gani yanzunnan Shiruuu, Umma tayi, tana shirin yin magana ta yi an shigo ana kuka. Kamar an hankad o Anty Zainab haka ta shiga d akin a hargitse kamar mahaukaciya! A gigice Umma take kallon ta, sai da ta bari ta nemi waje ta zauna tukunna tace Zainab lafiya kuwa?? Cikin kuka tace Ba lafiya ba! Sadiya na shiga uku!! Da sauri Umman tace subahanallah mai ya faru? Ta yi mata tambayar tana me d aukar wayar ta kashe ta ajjiye a gefe. Da kyar Anty Zainab ta d an tsayar da kukanta tace saboda Allah tsofai tsofai da ni amman wai ni Baban Khadija ya rufe ido ya dank ara wa saki har uku! Saboda tsabar idonshi sun rufe ya ma manta da biyun da ya tab a yi mini Da mugun k arfi gaban Umma ya yanke ya fad i! Saboda lokaci d aya kwakwalwarta ta d auki chaji Tabbas ita ce ta tafka kuskure abun kuma ya koma kan Anty Zainab! Wadda daga rakiya gashi yanzu ta janyo mata Tana cikin wannan tunanin Anty Zainab d in ta sauk o ta matso kusa da ita kafin tace Yi maza Sadiya d au waya ki kirawo Jalila mu ji Anya kuwa an yi auren nan? Ko dai zurma mu su Maryam suka yi? Dan wallahi masifarnan tana fad omin maganar Malamin nan na jiya na tuna. Yi sauri Sadiya ki kirata mu ji, ta bincika mana sosai.. In dai maganarshi gaskiya ce to mu samu mu koma mishi a san abun yi tun da wuri! Kin ji Sadiya! Dan Allah kirawo ta mu ji Cikin In Ina Umma tace Tt ta tam! Amman d azun nan ma mun yi waya da ita kuma ta tabbatar min da cewa an yi auren. Hannu biyu Anty Zainab ta d aura a kai kafin tace Innalillahi wa innailaihirrajiun Me ya faru da ni tou??? Ajiyar zuciya Umma ta sauk e jikinta na rawa tace To wai ke me ya had a ku ne? Cikin kuka Anty Zainab tace Aure wai mutumin nan zai yi! Yarinya k arama dan tsabar cin fuska shine bai gaya min ba, sai d azu tukunna Baaba Talatu ta kirani take gaya min, ashe wai ita sun sani ita da Shuwa shine suka b oye min wai dan kar in d aga hankalina inzo inyi wani shirmen.. Sadiya abunda zai baki mamaki wallahi tallahi kawai zuwa nayi nace mishi Ya zai yi min haka? Me yasa ya b oye min? Ai da ya gaya min tun da wuri Kar ki k ara kar ki rage daga haka kawai sai ya hau masifa, arshe yace In tattara in tafi ya sauk e igiyoyinsa na aure kaff ukun da suke a kaina! Wai ya san in dai amaryar tasa tazo ba zan barta ta zauna ba. Ko kayana bai barni na kwasa ba da magariba dan bala i ko kwana bai bari nayi ba ya kad oni har da rufe gidansa. Ita kuma Baaba da na je mata daga jin magana bata tsaya taji ba asi ba kawai ta hau fad a! Wai ai laifi na ne, daman shiyasa suka k i gaya min, ai ba a kaina Miji ya fara k are aure ba, ai yanzu gashi na janyowa su Sadik haka yanzu zai dawo daga boarding ya tarar ba Maman shi a gidan iri k iri Yaro ko secondary school bai gamaba amma ina arin maidashi maraya, har su Khadija ma da suke gidan Miji sai ta shafesu Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, k arshe ma ko zama bata barni nayi ba itama ta koreni! Da sauri Umma tace Yanzu kenan a nan za ki zauna? Cikin share hawaye Anty Zainab tace To ya zan yi? Ina zan je? Port harcourt ko Ina? Ajiyar zuciya Umma ta sauk e kafin tace Ki kwantar da hankalinki, zai mayar da ke, kin ji ko, In sha Allah. Cikin kuka Anty Zainab tace Baban Khadija fa babban d an ka ida ne ke kin sani ba zai tab a bari mu zauna da saki ukun nan ba Cikin yin k asa da murya Umma tace Ki kwantar da hankalinki, za mu nemi mafita In sha Allah. Sannan ko hauka muke ba zamu bar auren nan ba yasin sai dai in me taurin ruhi ce kamar Maryam wadda ta nace sai da kyar! Tukunna aka samu ta bar gidan nan, to kinga idan irinta ce ba yanda muka iya dole mu barta amman shima sai mun ci ubanta wallahi. Maza basa kyautawa wallahi sam! Saboda Allah Ina ma lefin ya d auko miki mai d an shekaru. Fisabilillahi Ina Baban Khadija Ina sa ar su Khadija?Tsofai tsofai da shi. Da sauri Anty Zainab tace Kuma budurwa! Cikin karb e zancen Umma tace Ba zai ma yiu ba fa Wallahi! Dole mu san abun yi. Ki kwantar da hankalin kar ki saka damuwa a ranki, zamu nemi mafita. Bai isa ba wallahi, kin ji. Su Shuwan nan suna bani mamaki, daga an yi magana suce wani wai kar mutum yayi shirme in za ai mishi kishiya waye waye Bayan su basu san zafinta ba! Tunda duk cikinsu babu wadda Mijinta ya tab a yin koda budurwa ne a waje, sun kafa sun tsare nasu mazajen amman sun iya tak arewa suna yiwa mutum nasiha akan kishiya tsabar renin wayo! Su bar waenda suka san zafin kishiya su yi magana mana ba wai su tsayayyun matan da suka kafe mazajensu ba Ita dai Anty Zainab mik ewa tayi ta isa kan gado ta kwanta ta juyawa Umma baya, dan taga abun nata kamar ya fara zama cin fuska kuma. Tana jinta tana ta bambami daga k arshe ta yi shiru ta gyarawa Ya Ja afar wanda yayi bacci kwanciyar sa ta lullub e sa tazo ta nemi waje gefen Anty Zainab itama ta kwanta .. Ta gama rayawa a ranta gobe zata koma wajen mutumin nan tayi masa maganar Anty Zainab asan abun yi dan gaskiya tayi mugun tausaya mata. Amman kuma abunda yasa tayi shiru bata gaya mata gaskiyar lamarin yanzu ba shine ta lura aikin mutumin kamar yakan iya juyewa kuma waiwaye! Tunda gashi na Huda ya koma kan Anty Zainab d in , dukda ya fad a musu dama amma still kamata yayi ace aurenta da Aslam ne ya mutu ba wai na Anty Zainab ba tunda de Hudan aka yiwa abun so it doesn t matter ko waye Mijin nata ita ya kamata a sako Kanta ya kulle dole ta koma wajenshi amman ba zata bari suje da Anty Zainab ba dan yadda take a rikicen nan haka kurum taje ta tunzura mutumin yayi mata nata aikin aje garin gyara nata a tab o na Jalila da bai gama had uwa ba. Ko da ace zata gaya mata Hudan ba Arshaad ta auraba to sai ta tabbatar Mutumin ya gama yi musu aiki mai kyau! An d aura auren Jalila da Arshaad ta kamashi sosai ta samu fada a wajenshi tukunna, saboda kar aje aiki ya had a masa biyu yak i concentrating akan na Jalila sosai, ko kuma kuma yaje ya gyara na Anty Zainab wani abun ya samu na Jalila A ranar dai haka suka yi bacci duk su biyun rabi da rabi. Su Hudan suna shiga a parlourn suka tarar da Ummi da su Shuraim sunata shirya dining tare da masu aiki. Ummi tana ganinsu ta k arasa inda suke tayi hugging Hudan tana mata sannu da zuwa. Cikin girmamawa suka gaisheta ita da Aslam, ta amsa musu da kulawa, daga nan suka gaisa da su Sudais, murna kuwa a wajen su kamar suyi me tunba ma da suka ganta har da akwati ba Su suka ja mata suka kai mata har d Abba yaso su zauna a sama amman Aslam yace a barsu a d akin bak shi da cewa ma yayi ita akai mata nata kayan sama shi a barshi zai zauna a d akin bak i, shiyasa kawai Abban yace a kai mata akwatin ta nan d akin bak Ita dai Huda so take tace a barta ta tafi d akinta amman bata san ta ina zata fara ba! Ta san a idon duniya da su Abba Aslam mijinta ne amman taya ake expecting tayi sharing d aki da shi bayan ga d akuna birjik kala kala a gidan. Su kuwa su Daddy dama tun kafin su fita daga gidan bayan Gramma ta kirasu suka gama deciding akan zasu san yadda za suyi su taho nan gidan ita da Aslam d daga nan kuma su ajjiyesu shi da Hudan a waje d aya, dan sun lura tabbas sai sun d an taka rawa a relationship d in nasu tukunna za a samu su ma fara magana