← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 69

Sashe 21

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zai dawo! Kuka take yi tana godewa Ubangiji tana sake godiya A hankali Madu ya shiga lallashinsu yana cewa Su yi shiru Da kyar ya samu Shuwa tayi shiru saannan ta tayashi lallashin Mama tukunna itama aka samu tayi shirun. A hankali tasa hannayenta ta kamo nasu sanann tace Abba Hajiya Dan Allah nima kuyi hak uri akan yadda na gudu na bi Abba, ku yafe min dan... Da sauri Abba Madu ya d aura yatsanshi akan bakinta yace Ba komai Maryam, komai ya wuce, Allah yayi miki albarka. Juyawa tayi ta kalli Shuwa, a hankali tana murmushi Itama ta d aga mata kai tace ya wuce! Allah yayi miki albarka. Sannan ina neman alfarma nima a wajen ki, kamar yadda Ummi ta fad nima In ba gani nayi kin koma gidan Abba ba to ba zan samu peace of mind ba, Ina so in gyara abunda muka taru ni da dangisa da su Usman muka lalata. In dai kin yafe min da gaske to inaso ki yi hak uri ki koma gidan Abba, hakan shine abunda zai sanyani farin ciki shine abunda nake so da burin gani a rayuwata Cikin sheshshek ar sabon kukan da ya tahowa Maman tace Amman Hajiya.. Da sauri Hajiya Shuwa tace Ba zan miki dole ba, ba zan tilastaki ba amman inaso ki sani Hakan shine zai sanyani farin ciki hakan shine abunda nake so hakanne zai tabbatar min na gyara abunda na b ata ya kuma taimakamin wajen sanyani in yafewa kaina. Ki daure, ni Shuwa Ina rok on ki ki koma gidan Abba, na san har yanzu kina k aunar sa. Sunkuyar da kai Mama tayi tana wani gunjin kuka mai d aci... A hankali Shuwa ta share hawayenta sannan ta sa hannu ta shafa kumatun Mama kafin ta mik e ta bar wajen da sauri. Muryar Madu Maman taji yana cewa Kiyi hak uri ki bi shawarar da duk wani masoyinki yake baki Abba har yanzu yana k aunarki kema kuma na san kina sonshi. Ki duba kiga ko kwana biyun nan da suka wuce sai da suka zo nan shi da d an uwansa akan maganarki Maryama a zamanin nan ba lalle a samu mutumin da zai yiwa wata kwatan kwacin k aunar da Abba yake yi miki ba. Kamar yadda Mahaifiyarki tace to haka nima ba zan yi miki dole ba amman zan baki shawarar ki bari ki yarda ki amince a maida aurenku da Abba, hakan zai bashi nutsuwa da farin ciki na har abada dan a yadda na ganshi ranar da suka zo na san ba abunda yake so da buri sama da a maida aurenku, nima kuma hakan nake so Mahaifiyarki itama hakan takeso arki ma hakan take so above all na san kema hakan kikeso achan k asan ranki kawai dai obstacles ne suke son tsaidake ga isa inda zuciyarki take so. A hankali ya shafa kanta yace Ki yi tunani mai kyau amman ina so decision d inki ya kasance abunda kike so ne kuma ki tabbatar zai sanyaki farin ciki har k arshen rayuwarki. Yana gama fad in haka ya mik e ya fice dan lokacin sallah ya gabato A hankali Mama take sauk e ajiyar zuciya, ta dad e a zaune sai da ta fara jin kiran sallah tukunna ta mik e ta wuce d akinta zuciyarta fal sak e sak Ta san cewa yanzu Abba baya tare da Granpa amman fa duk inda aka je aka dawo uba uba ne, ba a chanjawa tuwo suna kamar yadda take da tabbacin k iyayyarta a zuciyar Granpa ba zata tab a chanjuwa ba..... Haka nan, har dare Mama jikinta duk yayi sanyi kamar wata mara lafiya Shuwa da Abba Madu basu sake yi mata maganarba dan basa so suyi ta pressurizing d inta.. haka nan suka yi dinner atare cike da da so da k aunar juna suna hira gwanin ban sha awa Wani kalar farin ciki kawai Maama take ji wanda ta dad e bata yi ba, yana ratsa zuciyarta. A hankali from time to time take d an fakar idonsu ta juya ta d auke kwallar farin cikin da ta k i daina taruwa a idanunta. Da daddare tana shirin kwanciya Huda ta kirata, kamar had in baki itama maganar Abba ce take so suyi, bayan sun gaisa ta gama y an kame kamen ta kafin ta rok eta Allah da Annabi ta dawo gidan Mahaifinta. Cikin son kawar da zancen Mama ta sako wata hirar ganin da Hudan tayi kamar bata son zancen ne ya sanya bata sake mata maganar ba har sai da suka zo sallama, nan d in ma d an shiru Mama kawai tayi, chan kuka tace mata ta gaida Ummi da Aslam tayi mishi godiya sannan ta katse kiran. A hankali Hudan ta gyara kwanciyar ta akan gadonta ta kwanta rigingine tana mai kallon sama ........... AFTER TWO WEEKS. A zaune Ummi ta shigo ta tarar da Hudan ta rafka uban tagumi. Murmushi tayi ta k araso inda take ta zauna kafin ta dafa ta. A hankali Huda ta d ago tana kallonta wanda hakan ya sanya Ummin ta fahimci kuka tayi. Karkatar da kai Ummin tayi kafin tace Huda ko nice Aslam fa ba kawo kud i ba ko bikin Sakina za ayi ba zan barki ki je ba, wallahi. Ke kika jawowa kanki dan haka kar ki zauna kina wani kuka, ai baki ma yi kuka ba ki jira sai Abban ku ya dawo gobe, na tabbatar in dai yaji labari wallahi da ni da ke kashinmu ya bushe! Bar ganin yana lallab a ki in dai yaji wannan zance to fa ba zaku kwasheta da kyau ke da shi ba. Kuma yana zuwa zan gaya masa tunda ni kin raina ni Da sauri Huda tace wallahi Ummi ba rainaki nayi ba. Cikin katseta Ummi tace Raini ne mana Huda! iri k iri fa kika hanani number Mama saboda kin san in na kirata na fad a mata zata yi miki fada kuma dole ki yi abunda bakya so d so bama kya so taji ballantana har a kai ga tayi miki magana amma ni Ina kallon ki kina kallona a cikin gidannan yau sati biyu kina wasar y ar b uya da Mijinki kuma ban isa in hana ki ki hanu ba tunda ban Isa da ke ba Cikin kuka Huda tace Allah Ummi kin isa ewa tsaye Ummin tayi kafin tace Idan har na isa to ki tattara kayan ki da kika kwaso da hannunki ki maida ki gyara d akin ki wanke toilet kafin ya dawo. Wallahi na manta yaushe zan ce na tab a ganin Aslam yana gyaran d aki amman jiya dakanshi har mopping naga yanayi kuma ba yadda ban yi da shi akan ya bari a gyara ba amma ya k i yarda saboda ya san nan d in turakarku ce bai kamata a shiga ba. Dan maiyasa shi yana mutuntaki amma ke ba zaki kwatanta ba?. Ki tashi kije ki koma sannan idan ya dawo ki bashi hak uri tare da alk awarin ba zaki sake ba In dai har na isa da ke kenan, kamar yadda kika fad Tana gama fad in haka ta juya ta fice daga d akin. Sai da Hudan taci kukan ta ta godewa Allah tukunna ta tashi ta sauk asan Ta yarda zata zauna a d akin amman tabbas zata cire tsoro kunya da kawaici su yi agreement ita da Aslam! Auren su ba na soyayya bane ba Infact k arin kawo karshenshi ma ya kamata suyi a yanzu so ba zai yiu ya hautsina mata kwakwalwa da zuciya ba bayan ba son juna suke yi ba so gara su san inda suka dosa kowa ya tsaya a iya limit d insa Tana shiga d akin k amshin turarensa ya mata sallama, a hankali ta shak a ta lumshe idanunta! A take wata nutsuwa da kasala suka dirar mata sannan taji zuciyarta tana yin sanyi b acin ran da take ciki kuma yana d an raguwa. e idanuwanta tayi ta shiga k arewa d akin kallo tana ganin fuskarsa a idonta, murmushi ne ya sub uce mata da ta tuna irin uwar hararar da ya zabga mata sannan yace Ba zaki je ba! ya juya ya fice. A hankali tace Dama maza ma sun iya harara? Tana murmushin tana tunani ta shiga gyara d akin cikin nutsawa kwarewa da iyawa. Tana gamawa ta shige toilet ta wankeshi tsaf tsaf. A wajen Ummi taje ta karb o kasko da turaren wuta ta saka a d akin sannan ta shiga kitchen ta had a masa spring rolls da tea, duk dan a barta ta fita. Tana gamawa ta fito ta kai dining ta jera a inda taga yana yawan zama. Tana cikin jerawa Ummi ta sauk o, dariya tayi kafin tace a na ne? Ko kuma biyayyar aure? Ko dai bribe d in a barki ki fita gobe?? Turo baki Hudan tayi sannan ta d anyi murmushi. A hankali Ummi ta k araso inda take ta dafa kafad arta sannan tace Na gode Huda. Kin nunamin nima na isa da ke Ta yi maganar tana murmushi. Murmushi mai had e da dariya tayi sannan ta fad a jikinta tayi hugging nata tace Ummina kin isa mana A haka su Shuraim suka shigo suka samesu, hakan ba k aramin burgesu yayi ba kuwa, dan haka Shuraim ya k araso ya yi joining hug d in Sudais kuma ya tsaya ya fara bubbuga k afa shi ala dole sai dai a cika su a yi mishi nashi special Cika su Ummi tayi yana ganin haka ya k araso yayi hugging d inta. Ahankali ta zaroshi daga jikinta ta kama hannun Shuraim ta rik e da nashi a waje guda sannan ta kamo hannun Huda ta saka mata hannayensu a cikin nata kafin ta fara magana Na san ba wani girman su Shuraim kika yi sosai ba amman dan Allah Huda ko bayan raina ki zame musu uwa ki yi musu dukkkannin abunda zan yi, ba su da kamarki a duk fad in duniyar nan. Da sauri Huda ta toshe mata baki da hannunta Idonta ya cicciko da kwalla tace Ummi ki daina dan Allah kar
Chapter 21 · 0% Book details