Sashe 4
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
awa su Mommy amanar Huda suka amsa hannu bibbiyu suna masu farin ciki ewa aka fara yi da niyyar tafiya amman Amarya furr! Ta k i mik ewa.. Da kyar Ummi tasa hannu ta d agota sannan ta jawo ta jikinta ta rungume ta shiga lallashinta tana cewa muje mana dota. Yi hak uri kinji, kowa da haka ya fara. Cikin kuka, da muryarta wadda ta dad e da dishashewa ta cewa Ummin Ban yi sallama da Mama ba. Dan Allah ku kaini wajenta. Zan biku amman sai na fara yiwa Mama sallama. Lumshe ido Ummi tayi tana jin yadda k irjinta ya fara bugawa da sauri da sauri A hankali ta juya ta sanarwa su Mommy abunda Hudan tace Murmushi Shuwa tayi kafin ta cewa Ummu ta tashi ta kamata su kaita mota. Za suyi sallamar a waya. Sai da suka yi da gaske kuwa tukunna suka iya janyeta. Tana kuka tana komai haka suka fitar da ita aka sanyata a mota Ummu da Ummi suka sakata a tsakiya Ummi sai faman lallashinta take yi..... Inda Mama take Mommy ta tambaya bayan fitar su. Sakina ce ta kaita har d akin sannan ta juya ta fita dan itama tana so ta raka Amarya. Mota guda suka yi ita da k awayensu su hud u waenda suka zo rakiyar Amarya. A zaune Mommy ta sami Mama a bakin gado tana ta sharar hawaye.. Sai da ta k arasa inda take ta dafa kafad arta tukunna ma Maman ta san mutum ya shigo! Murmushi Mommyn tayi ta zauna a gefenta sannan tace Ai gara da Hajiya tace a tafi da ita ba sai kun yi sallama ba dan na san daa ta shigo ta ganki a haka to da sake tab arewa al amarin zai yi Kukan Mama ne ya tsananta a hankali ta juyo ta kama hannunta tana sheshshek a tace Mommy, ga amanar Huda! Dan Allah ki kular min da ita. Ina tausayawa Huda dan ban san ya zaman nasu zai kasance ba saboda na san duk su biyun basa k aunar juna amman kuma idan na tuna ke ce surukar ta sai hankalina ya d an kwanta na san at least ko da ace bata samu soyayyar Miji ba na san zata samu ta Mahaifiyarshi Hakan zai d an rage mata rad i da damuwa. Naso ace Huda ta auri mai k aunarta amman kuma k addara ta riga fata. Ta k arashe maganar tana mai fashewa da kuka. Murmushi Mommy tayi kafin tace Share hawayenki, ki d ago ki bani hankalinki. Da kyar Mama ta iya tsayar da kukan nata sannan ta d ago tana mai kallon Mommy da idanuwanta da suka k ance sukai jaa. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk e kafin tace Ki daina cewa Aslam ba ya k aunar Huda! Dan zan iya rantse miki ko shi kanshi Arshaad d in ba ya yi mata kwatankwacin son da Aslam yake mata. an zaro ido Mama tayi tana kallonta da alamun mamaki. Kwarai kuwa Shine abunda Mommy tace sannan ta d aura da cewa Tunda na warke, although ban zauna da Aslam ba ban kuma san yanayin shi sosai ba amman tashi d aya na fahimci yana cikin matsananciyar damuwa! Kullum yana fama da zazzab i da hawan jini, anyi anyi da shi akan ya fad i damuwar shi amma yak i fad awa kowa. Sai da yaga yana shirin mutuwa tukunna ya zo ya samemu ni da Dad yace mana yana neman alfarmar mu barshi ya tafi uk ya d an yi y an kwanaki Mu kuma ganin rashin dacewar hakan ne ya sanya muka hanashi tafiya. Bayan Dad ya fita ne na lallab ashi akan ya fad amin damuwarshi.. Da kyar ya iya gaya min dan shi har ga Allah kunya yake ji He knows he s selfish ta ko wanne b angare amma ya rasa yadda zai yi ya yakice soyayyar Huda a cikin zuciyarshi. Yace min tun ranar da ya fara ganinta tun ba yanzu ba Allah ya d aura masa matsannciyar soyayyarta! Kuma dede da rana d aya k aunarta bata tab a raguwa a zuciyarsa ba instead k aruwa ma take yi. Baya iya bacci baya iya yin komai cikin nutsuwa idan ba hotonta ya saka a gaba ba yayi ta kalla. A ranar yace min Muddin muka barshi aka d aura auren Huda da Arshaad a gabanshi tou tabbas zai iya rasa ranshi! Dan haka shiyasa yana ganin gara yayi nesa sosai kuma yana rok ona ko da an d aura auren to kar In fad a mishi, ko ya tambayeni kawai ince mishi nima ban sani ba Naji matuk ar tausayin Aslam a wannan lokacin tabbas, ba na so ya zama coward shiyasa na hana shi tafiya na rok esa Allah da Annabi ya zauna..idan yayi facing ya tabbatar da ta sub uce mishi forever hakan will make him stronger and zai cire hope yayi moving on. Ya yarda zai zauna bayan ya tabbatar min idan bai mutu a ranar ba to zai iya samun heart attack! Ni kuma na duk ufa gayawa Ubangiji Ya saka mishi sassauci da dangana sanann ya zab Hudan Arshaad da Aslam dukkan nin abunda yake alkhairi ne a rayuwarsu. Tun jiya na hango silver lining. Shiyasa yau na tilasta mishi yaje d aurin auren! Idan an d aura auren Huda da Arshaad a gabanshi na san hakan zai taimaka mishi akan ace ya gudu daga reality da nauyin hope! Idan kuma an d aura da shi to falillahil hamdu. Ajiyar zuciya ta sauk e kafin ta ci gaba Tunda har Aslam ya iya kawar da komai ya cire kunya ya furta mini cewa yana son Huda to tabbas na san ba k aramin so yake yi mata ba! Ki duba kiga yadda suke shi da Arshaad da kuma kawaici irin nashi amman ya kasa hak ura! Na san Aslam tun yana Yaro k arya ba abunda ya iya baneba besides why will he even lie? All that I m trying to point out miki anan shine Hudan ta tafi gidan wanda yake k aunarta matuk Ki kwantar da hankalinki ki bisu da fatan alkhairi......... Direct MT estate aka wuce da ita... Already Mommy ta saka masu aiki sun share sun goge side d in Aslam sai tashin k amshin turaren wuta yake yi. Ba abunda babu na fannin furnitures, duk ragowar d akuna ukun akwai gadaje masu kyau! Parlourn ma yana d auke da duk wani abun buk ata. Motocin suna gama yin parking aka fara firfitowa. Tun a gate na estate d in Anty Zainab taji inama bata zo ba! Gashi mata y an Maiduguri da suka shigo mota d aya tare da su sai faman zuzutawa suke yi suna Ma shaa Allah! Huda kam Allah ya bata duniya ita kuma tanajin kamar ranta zai fita! Sannan kanta ya d an juye dan cewa aka yi gidanta ita kad ai ce yanzu kuma taga an kawota nan!. A haka dai tana ji kamar zuciyarta zata fashe ta biyewa jamaa akai ta washe baki da ita, ta bari akan In sun koma zata bugi cikin Khadija ta ji komai dan ta san idan ba bugar cikin nata tayi ba to ba zata tab a gaya mata ba! Sun sha yin fad a da ita Khadijar ba sau d aya ba akan su Hudan. Ummi da Ummu ne suka ruk ota, suna zuwa main door na shiga gidan suka umarceta da ta shiga da bismillah da k afar dama, haka ma k ofar side d in Aslam da tazo shiga! Yadda suka ce hakan take yi da fuskarta a rufe cikin laffaya tanata kuka. Sai da suka kaita bakin gadonta sannan suka ajjiye ta da bismillah. Bayan an d an ragu a d akin Ummu ta k ara mata da nitsatsiyar nasiha! Basu wani dad e ba suka fara shirin tafiya hatta gifts da abincin da Dad ya shirya musu ma mota kawai aka kai dan suna idar da sallar Magrib suka fara zuwa suna yi mata sallama suna ficewa Jama a da friends d insu in banda santin estate d in da side d inta ba abunda suke yi, a haka kowa ya watse. Aka barta ita da su Sakina da Khadija da friends d insu guda biyu da suka zauna dan ragowar cewa suka yi za su wuce saboda basa so su yi dare Da kyar da sid in goshi Huda ta d an tsayar da kukan nata, bayan dogon lallashi daga su Sakina ta yi shiru ta bud e fuskarta. Tana jinsu suna ta hira ana shewa amman ta kasa tanka musu Istigfari kawai take tayi saboda sam! Tunanin Arshaad yak i fita daga ranta. Daga masallaci direct gida Aslam da Dad suka wuce side d in Mommy. Suna zaune ita da Gwaggo Asabe da alamun magana suke mai muhimmanci su Dad d in suka shigo. ewa Gwaggo Asabe tayi zata fita Dad yayi saurin cewa ta dawo ta zauna Nasiha za su yiwa Ango! Sun kusan 1 hour suna yi masa Nasihar daga nan Dad ya mik e yayi musu sai da safe. Kana ganin Mommy da Gwaggo Asabe ka san suna cikin farin ciki. Mommy ce tace To ka tashi ka je kuyi siyan bakin mana. awayenta fa kai suke jira su tafi Kamar zai yi kuka yace Mommy siyan baki kuma? Kin san fa a yanda auren nan yazo. Ki barshi kawai su yi tafiyarsu, Ina son ganin Arshaad first. Ya fad a yana mai mik ewa zai fita. Baya nan Yaji muryar Mommy. Da mamaki ya juyo kafin yace Ina ya je? No body knows Mommy ta fad a tana mai mik ewa ta k araso inda yake. Baka farin cikine? Yau? an Satar kallon Gwaggo Asabe yayi yaga hankalinta sam baya kansu . A hankali ya sauk e ajiyar zuciya kafin yace Mommy ba wanda ya kaini farin ciki a kaff fad in duniyar nan a yau! Amman no matter how i tried sam! Na kasa ignoring some facts ne, If I were in Arshaad shoes I would have die by now. Gara ka san abu ba naka bane ba tun farko akan ka saka rai kuma azo baka samuba daga k arshe. Ajiyar