Sashe 32
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Buri Free Book Mikiya Writers Association. Direct side d in Granpa aka nufa da gawar Ummi. Kafin zuwa asuba Mommy da Gramma suka yi mata wanka suka shiryata. Haka nan suka sakata a gaba suka dinga yi mata karatu da tofi tun jiyan dama suke yi su biyar har Huda Shuraim da Sudais, suna yi suna kuka. Ana idar da sallah aka sanar jana iza k arfe 9:00am a masallacin estate, daga nan gaba d ayan su kowa ya nufi side d in Granpa. Shiruu! Haka b angaren ya kasance amman kowa da Al quraninsa, masu hawaye suna yi suna karatun Har zuwa lokacin da gari ya waye jama a suka fara taruwa, ofta da suka ji ana ta lek awa estate d in ana gaisuwa, sai k awayensu da family friends da suka ji ta wayoyi arfe tara tana yi mazan suka shigo domin fita da gawar sai a sannan abun ya dawo sabo! Abun tausayi especially yadda Huda Shuraim da Sudais suka k ame gawar suna kuka kamar ransu zai fita! Da kyar Arshaad ya janye Sudais Auwal kuma wanda Daddy yaje ya d auko ba da jimawa ba ya janye Shuraim Aslam kuma yaja Huda! Tukunna su Daddy suka saka gawar a makara aka fita da ita waje domin a sallaceta arfe tara aka gabatar da jana iza aka mik a Ummi gidanta na gaskiya. Ta samu halarta d umbin jama a maza da mata dan kamar yadda mak abarta ta cika haka ma cikin estate d Suna dawowa Granpa ya cewa Abba Su zauna anan (estate d in) ayi zaman makoki ba sai sun koma chan gidansu ba...... Washegari, Sumayya Ummu da Baban su Sakina suka zo suka yi ma Huda da Abba gaisuwa. Ranar sadakar uku, Huda tana d akin Gramma dan a nan take ita da su Shuraim ta ji wayarta tana k ara! Tana d auka Auwal yace Ta yi bak o yana waje a bakin estate, wai ya zo mata gaisuwa, yace sunan shi Junaidu Ta sanshi a barshi ya shigo? Bata san lokacin da ta diro daga kan gadon ba tace Eh Ya Auwal na sanshi sosai yayana ne! A barshi ya shigo. Daga nan ta zari hijabinta ta yi waje tana adduar Allah yasa Ya Junaidun ne da gaske. Bata samesu a compound d in Granpa ba daman bata yi expecting hakan ba! Dan haka ta fice daga gidan ta nufi tsakiyar main compound na estate d in. A inda ake parking motoci ta hango Auwal sanye cikin bak ar jallabiya fuskarsa tayi fayau! Idanuwansa da suka ci kuka sun yi jaa sun k ance yayi tsananin rama sannan kana ganinshi ka san bashi da lafiya A tsaye tare da wani ya juya baya sanye cikin shadda fara d inkin boda da bak ar hula ya jingina a jikin booth d in wata bak ar mota Jeep! Yanayin takalmi da shadda da kuma hular kansa kad ai sun isa su sa ka san cewa kud i sun zauna Da Auwal suka fara had a ido yana shirin yin magana a hankali yaji tace Ya Junaidu Shiruu yayi da maganar da yake yi kafin ya gyara tsayuwarshi daga nan kuma ya juyo gaba d ayanshi yana murmushi Kusan daskarewa Huda tayi, a hankali hawaye na gangarowa akan kumatunta ta ce Ya junaidu Murmushi yayi yace am Huda Cikin share hawayenta tace Where have you been? Yaushe ka dawo? Me ya faru? How have you been.. Murmushi ya saki mai d an had a da dariya kafin ya shafa k asumbar da ya tara tayi mishi tsananin kyau yace Ya muka ji da hak uri? A hankali ta sunkuyar da kanta tace Alhamdulillah Cikin sanyin murya. Ajiyar zuciya ya sauk e kafin yace Allah ya ji k anta yasa chan tafi nan A hankali ita da Auwal suka ce Ameen Kafin Auwal d in ya juya ya yi mishi sallama ya wuce. Gyara tsayuwarshi yayi yana kallonta kafin yace How are you?. Congratulations you have finally found your Dad Jijjiga kai tayi sanann tace Thank you Tana mai d ago da kanta sannan ta sake jeho mishi tambayar Where have you been? Dede nan Arshaad wanda dawowar sa kenan daga airport d auko Aaima suka k araso wajen shi da Aaima. Murmushi Junaidu yayi kafin yace Arshaad! Da sauri Huda ta juya dan ita bama taga tahowarsu ba. A hankali ta k arasa inda Aaima take ta rik e mata hannu tana kallonta kafin ta yi hugging d inta. Bata iya ce mata komaiba Har ta cika ta ta d ago. Ahankali Aaima da muryarta ta d an dishe tsabar kuka tace Ya hak urin mu? Alhamdulillah Huda tace Daga nan Aaima ta d an d ago ta kalli Junaidu wanda ya kafe Arshaad da ido tace Ina wuni Ajiyar zuciya ya sauk e kafin ya juyo ya kalleta a hankali yace Alhamdulillah. Ya hak uri? Alhamdulillah tace, daga nan tace Ya arshaad bara in wuce ciki, thank you. Tana gama fad in haka ta juya ta wuce ciki. A hankali Huda ta d an juya ta maida hankalinta akan Arshaad kafin tace Ina wuni Ba tare da ya kalletaba ya ce lafiya Junaidu Hudan ta kalla wanda tun wucewar Aaima ya maida idanuwanshi a kan Arshaad tace Ya Junaidu baka bani amsa ba Ajiyar zuciya ya sauk e kafin yace Actually.. Ni kaina ba zan iya ce miki ga a inda nake ba. Forget all that bana so ma In dinga tunowa Sai kuma yayi murmushi yace Congratulations Na ji kin yi aure! Ya fad i hakan yana kallon Arshaad kafin ya ce And kamar ba Arshaad kika aura ba ko? Mai yasa? Da sauri Huda ta d ago ta kalleshi, ganin ba ita yake kallo ba gaba d aya hankalinshi yana akan Arshaad d inne yasa tace Ya Junaidu Juyowa yayi ya kalleta, a hankali ta jujjuya mishi kai alamun ya bar maganar. Murmushi kawai yayi yana maida idanunsa akan Arshaad still kafin yace No i was just curious ne He has done so much and a lot for and because of you! I wonder why bai samu aurenki at the end of the day ba A hankali Arshaad ya d ago jajayen idanuwanshi wanda har sai da suka so firgita Huda ya watsa su akan Junaidu kafin yace Did you come here to mock me? Da sauri Huda ganin Junaidun yana sake shiri yin magana tace Ya junaidu ka daina mana. Gaisuwa ka zo ko? To kayi iya gaisuwar please. Shiruu yayi ya d an sunkuyawar da kanshi yana kallon k asa kafin ya d ago yace Forgive my manners Yana kallon Arshaad sannan ya juya ya kalli Huda yace Allah ya ji k an Ummi. Bara in wuce, su Umma ma basu ganni ba dan ban je ko gida ba I came here straight. Hudan gaba d aya lamarin Junaidu ya d aure mata kai! Bai je gida ba? Tou a Ina ya san Ummi ta rasu? Sannan waya gaya mishi ta yi aure? Sai anjima Ya ce yana d an murmushi yana kallonta. A hankali tace Na gode ka gaida su Umma daga nan ta juya ta wuce. Wani abun mamamkin.. har ta kai gate Arshaad da Junaidu suna tsaye suna magana kuma da ga yanayin yadda suke demonstrating har da hannayensu zai sa ka fahimci serious magana suke yi. Har ta hau sama d akin Gramma ta lek o ta window sai da ta gansu kafin chaan Junaidu ya bud e motarsa ya shige ransa a mugun b ace ya ja yayi gaba ya bar Arshaad nan tsaye a wajen Tana shirin juyawa sakamokon amshin da k ofofin hancinta suka jiyo mata, ta ji anyi huggin d inta ta baya. Runtse idanunta tayi da k arfi! A hankali dede setin kunnenta ta ji ya ce Haramun kike kalla fa Muryarshi na d an rawa. Da sauri ta d an ture shi kafin ta juyo tana kallonsa sai kuma tayi saurin yin k asa da kanta dan gaba d aya sa taji ba dad especially ma yadda taga kamar ranshi bai so ba! Sannan ba lalle ya fahimci kallon me take yi wa Arshaad d in ba. Tana shirin yin magana ya katseta ta hanyar cewa Who is the other guy? A hankali ta d an sunkuyar da kanta kafin tace Ya Junaidu. Tare muka taso. Ajiyar zuciya ya sauk kafin ya matso kusa da ita sosai kamar zai shige jikinta yayi cupping fuskarta a hankali ya d ago da fuskarta yadda za su kalli juna sosai yana kallon cikin idonta yace Kar ki sake abunda kika yi yanzu, please. Yadda yayi mata magana da yadda taga idanuwanshi sun yi da yanayin voice d inshi ya sanya ta kasa cewa komai ta lumshe idonta kawai tana jin yadda jikinshi yake karkarwa a hankali Ya dad e yana kallon fuskarta kafin ya cikata a hankali ya juya ya fita. Tana jin fitarshi ta bud e idanuwanta tana sauk e ajiyar zuciya a jejjere Bayan rasuwar Ummi Idan akwai abunda yafi damunta ya fi rikitata tou Ya Aslam ne! Kwata kwata ta kasa gane gabanshi ta kasa gane bayanshi ta rasa me yake nufi da ita, sannan ita kanta yanzu ba zata ce ga tak ameme abunda take ji a kansa ba! Adduar ta d aya Allah yasa ba ta yi masa ko da d an mitsitsin so ne Dan in dai haka ta kasance to tabbas ta zama butulu! She is trying very hard ta ga ta yi nesa da shi amman idan yaso ganinta duk inda take sai ya shigo ya ganta ya fita. A ranar sadakar bakwai suka tashi jikin Auwal ba dad i sosai. Daman tun lokacin da aka yi rasuwar dauriya ce kawai yake yi amman sam ba lafiya gareshi ba Tun yana yi a b oye dan baya so a fahimta har Mom ta gano dan haka suka dangatashi da asibiti Ba k aramin tashi hankalin ahalin gidan yayi ba da ga jin Auwal ya kamu da ciwon zuciya! Da farko Daddy Huda ya fara kira yayi mata maganar Sakina dan tashi d aya ana tambayarshi mene damuwarshi ya ce Sakina Tun kafin aje ko ina jikin Daddy ya sake yin sanyi