Sashe 37
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da matar yana tanbayarta lafiya? Dan su da farko ma basu gane Anty Zainba d in ba saboda gaba d aya fuskarta jini ne. Tiryan tiryan matar ta koro musu bayani tun daga kan ihunta da ta jiyo da yanda idanuwanta suka gane mata Sadiya da Jalila a kanta suna jibgar ta. A hankali Shuwa ta mik e ta k arasa ta kamo hannun Anty Zainab ta cewa matar an gode Matar tana fita Baaba Talatu ta rarumi mayafinta! Da sauri Kaka ya mik e yace ina za ki je Fashewa ta yi da kuka cikin kukan tace Kar ka hanani. Na rok eka da girman Allah kar ka hanani ci ma Sadiya yau! Duk abubuwan da take yi bana magana yau kam ta kaini bango wallahi. Kallonta kawai Kaka yake yi kafin cikin b acin rai yace Laifin waye Zainab taje gidanta ta zauna? Ta bud e baki kenan zata yi magana ya d aga mata hannu yace Dan Allah ki barmu mu ji da Usman yanzu! Shuwa ku wuce ciki ki taimaka mata ta gyara jikinta ku kyale Sadiya kawai! Kuna ganin halin da Mijinta yake ciki ai amman wani lokacin sai ta yi kwana biyu ma bata lek o shi ba! Ku zuba mata ido ita da y arta zan samu lokacinsu kwanan nan. A hankali Shuwa ta jaa Anty Zainab suka shiga ciki Baaba Talatu ma tabi bayansu tana sharar kwalla. Kaka kuma da Ya Jamilu suka koma inda Baba yake zaune yanata faman zubar da hawaye. Sai da aka had a da allurai da magungunan bacci tukunna Anty Zainab ta samu ta iya runtsawa a ranar. Washegari kuwa sai da Shuwa ta yiwa su Khadija da gaske tukunna suka hak ura amman da cewa suka yi sai sun je sun samu Sadiya da Jalila sai dai a tashi gidan wallahi! Daman chan ita Khadija basa shiri da Jalila kwata kwata. Da yamma bayan su Khadija sun wuce, Mama da Shuwa suna zaune suna kallo Baaba Talatu ta shigo. Yanayin ta kad ai yasa Shuwa ta fahimci abunda ya kawota a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud e sai kuma kawai ta mik e ta bar wajen. A hankali Baaba Talatu ta k arasa inda Mama take ta zauna sannan ta amsa gaisuwar da Maman take yi mata da fara a, sai da suka gama gaisawa tukunna ta mik a mata takardun hannunta da ta shigo da su. Kallonta Maman tayi kafin ta kalli takardun sai kuma tasa hannu ta karb a ta fara karantawa..... Tabbas ta sha wahala a hannun Baba amman ba k aramin tausayinsa ta ji ba. A hankali tace Allah sarki Ya Usman wasu hawaye suna zubo mata. Hannayen ta duka biyu Baaba Talatu ta kamo kafin tace Dan Allah dan Annabi Maryam Ina neman alfarma a wajenki Usman bashi da lafiya dududu sauran mishi bai kai shekara ba! Ya nemi a maida aurenku dan yanaso ya mace a matsayin Mijinki.. Na san Usman bai kyauta miki ba! am ya yi laifi amman a halin yanzu bashi da maraba da babu. an lokacine wanda ba zai ma kai shekara ba kawai za ku yi tare. Dan Allah Maryam. Kasa magana Mama tayi Sai da Baaba Talatu ta sake cewa Maryam Tukunna ta juyo a hankali tace Baaba dan Allah dan Annabi kar ki rok eki abunda ba zan iya ba! Ki yi hak uri amman a gaskiya wannan alfarmar taki ta yi tsauri da yawa. Bayan kwana biyu, Baaba Talatu ta sake dawowa. Sun dad e suna magana da Mama Haka kurum kamar almara Mama ta samu su Madu tace ta amince da auren Baba! Tunda ya rok i yana neman alfarmar ya mace a matsayin Mijinta to zata yi mishi hakan a matsayinshi na wanda take kallo kamar d an uwa Ba yadda ba su yi da ita ba amman fur!! Tace Ya Usman kamar d an uwa yake a wajenta dan haka zaata zauna da shi na shekara d ayan ba komai. Ba dan sunso ba suka amince saboda sun riga sun yi alk awarin ba za su sake tilastamata ko su sakata tayi abunda bata so ba. Sai dare Shuwa taje ta sameta, cikin son fahimtar da ita ta shiga yi mata nuni da yadda Abba yake ta faman zirya A hankali Mama ta yi murmushi kafin tace Hajiya ni fa dama na gama yanke shawarar ba zan koma gidan Abba ba Da mamamki Shuwa take kallonta. A hankali ta sauk e ajiyar zuciya kafin tace Jin ku kawai nake yi Hajiya, amman yanzu tashi d aya in na koma cewa za ai kamar Ina jira matarshi ta mutu ne. Sanann ko bayaga hakama na riga na gama deciding in dai ba Mahaifinsa bane ya amince da ni to ba zan tab a komawa ba, ina so Mahaifinsa ya nema mishi aurena kamar yadda ko wanne uba yake yi wa d ansa sannan ya yi welcoming d ina cikin zuri arshi, ya karb a matsayin surukarshi kamar yadda ko wanne uban Miji yake yi wa matar d ansa... ....na san hakan ba zata tab a kasancewaba ni kuma In ba hakan yayi ba to ba zan koma ba! Kinga kuwa babu batun maida auren mu ni da Abba dan na san Mahaifinsa ba zai tab a amincewa ba sannan ba zai yi waennan abubuwan da nake kwad ayin inga yayi min ba. Shuwa za tayi magana Mama tayi saurin d aura hannunta a kan bakinta ta ce dan Allah ta yi shiru, a bar maganar Saboda ita kanta daurewa kawai take yi. CONTINUATION!. Driving Aslam yake yi cikin nutsuwa, har suka isa MT estate ba wanda yace k ala! Dan kowa akwai abunda yake tunani A cikin gidan Granpa ya yi parking, da sauri driver d inshi ya k araso ya bud e mishi motar ya fito cikin kamala suka nufi cikin gidan direct. Ba kowa as usual, har chan sama suka wuce tare.. A hankali Granpa ya d an kalleshi ya ce ka fad awa su Yusuf Ina buk atar ganin kowa da kowa anan after isha Okay Granpa Aslam d in yace daga nan Granpa ya nufi personal parlourn shi wanda zai sadashi da bedroom d insa. Da mugun sauri Aslam wanda yake ta faman kame kame ya na rarraba ido ya fad akin Gramma..... A zaune ya tadda su suna hira su biyu. Da sauri duk suka d ago suna kallon k ofar ganin yadda ya afko. Dariya Gramma ta yi kafin tace araso mana Sannan ta mik e tace Granpa ya dawo ko? Arshaad yace tare kuka fita Eh yana d akinsa ya bata amsa sannan yad an russuna ya gaida ta cike da ladabi. Sai da ta k arasa bakin k ofar tukunna ta d ago kansa ta amsa sannan tace Sannu da zuwa, ya hanya? A hankali yace Alhamdulillah Yana d an satar kallon inda Huda take zaune ta sunkuyar da kanta. Murmushi Gramma tayi sannan ta sa kai ta fice ta ja musu k ofar dan ta lura idan ta ci gaba da zama a d akin Aslam na iya zuwa ya rungumo matarshi a gabanta. A hankali ya ke takawa har ya k arasa inda take ya tsugunna a gabanta. Da sauri ta lumshe idanunta ta fara k arin nemo nutsuwa da lakkar jikinta dan ta gaza samunsu. A hankali ya kamo hab arta ya d ago da fuskarta yana kallon yadda ta runtse idon da k arfi!. Ajiyar zuciya ya sauk e kafin yace I miss you.. Sosai!!! Bata bud e ba kuma bata yi magana ba, tana nan a yadda take. A hankali ya fesar da numfashi yace Ko you still need more time? Sai a lokacin ta bud e idanunta da suka d an tara hawaye tace Moree time for? Ba tare da ya bari ta jaa numfashi ba yace More time for us.. ranakun da na baki sun yi miki kad an ko?. I was so eager to see you amman ke naga ko murna ma ba ki yi da ganina ba A hankali yana kallonta yace ko arzik in sannu da zuwa ma ban samu ba. Ya fad i hakan yana d an cika hab arta sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar ta. Da sauri ta yi k asa da kanta tana jin yadda k irjinta yake dukan uku uku. A hankali ta ji ya ce Umm?? Cikin wani kalar yanayi da siga. Sai da ta sake yin k asa da kanta tukunna tace Ina wuni, ya hanya? Ya aiki? Ajiyar zuciya ya fesar kafin yace Lafiya, hanya Alhamdulillah Aiki kuma, was terrible! Na d an samu matsala har ya kai ga an rufe company d ina na chan. Da sauri ta d ago ta kalleshi kafin tace Subhanallah. Garin yaya? Ya ji dad in yadda ta damu da alamarin ba kad an ba. A hankali ya d anyi murmushi cikin son kawar da zancen company d in yace t worry, ba komai. Ai inada wani ni da Abba.. Daman bawa ya kan samu abu at any time kuma ya kan rasa, wannan yana daga cikin k addarar bawa, fata kawai shine ya zamo mai yarda da k addara mai kyau ko marar kyau A hankali ya sa hannu ya kamo nata yace wata biyu baya!, Ubangiji yayi mini kyautar da sai da na suma tsabar farin ciki! Ya bani abunda na riga na fidda rai da samu, Amma yanzu ace dan na rasa company sai in damu? Yayi mata tambayar yana wani sassanyan murmushi. A hankali k irjinta yana wani mahaukacin racing tun da ta fara jin bayaninsa, ta d ago tana kallonshi. Har yanzu murmushi yake mata. Wasu hawaye ne suka zubo mata dan ta so ta fahimci inda ya dosa! Cikin son fahimtar da shi da kuma kawo k arshen bagwaren relationship d in nasu a hankali tace Ya Aslam shike nan yanzu Granpa zai sake cewa ni bad luck ce kenan Sai kuma ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara share hawayenta. Shi da farko ma bai fahimceta ba saboda yadda ya shagala da kallon lips d inta, sai da yaga ta fara kuka tukunna yad an dawo dede sannan ya fahimceta! Dariya ma shi ta basa dan haka a