← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 69

Sashe 15

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a toilet ko wayar tata bata d auka ba! Tana shiga ta banko k ofar!. Sai a lokacin Aslam ya bud e idanunsa, yana wani sassanyan murmushi mai had e da dariya Ta jima a toilet d in kafin ta fito. A zaune ta sameshi this time around da waya a hannunsa, a ranta tace sai kaje garin daddanna na ura ka lalata idon Wucewa tayi ta d au hijabinta ta zura ta fara k arin gabatar da nafila shi kuma ya mik e ya nufi band akin da gudu ta k arasa ta shige toilet d in kafin shi ya shiga ta rufo k ofar! Chaan, ta bud e ta fito ta wuce ba tare da ta kallesa ba.. Bayanta ya bi da kallo kafin ya girgiza kai kawai yana murmushi ya shige toilet d in, kamar ance ya d aga kai, yana kallon wajen dariya ta kufce masa, abunda bata sani ba shine jiya already ya rigada ya gani dan kafin ya kwanta sai da ya shigo yayi alwala.. Yana dariya yana murmushi shi kad ai haka yayi wanka cikin farin ciki da annashuwa dan shi kam Hudan already made his day yau before it even begins. Da towel ya fito d aure a k ugunsa lokacin ita kuma juya baya tana sallah. Cikin nutsuwa ya hau shiryawa, tana cikin sallar hancinta ya fara jiyo mata wannan azababben k amshin turaren nasa yana k aruwa akan wanda already ya riga kama d akin. Tana idarwa tayi addua ta shafa, ta gyara zamanta a nan gaban gadon kan kafet ta na jira a kira sallah. Takun sa ta ji a hankali yana k arasowa inda take.. Lumshe idanuwanta kawai tayi tana shak ar k amshinsa tana kuma sauraron yadda bugun zuciyarta yake k aruwa dede da takun nasa. A hankali taji yace Gyara in yi nafila agowa tayi suka had a ido.. Sanye yake cikin jallabiya bak a mai shek i amman ta k asan jallabiyar tana iya hango dogon wando bak kamar na suite saboda jallabiyar bata ida rufe duk k aurinsa ba. Da sauri ta mayar da kanta k asa ta mik e ta koma kan gado. Yana idar da nafila ana tadaa iqama a masallaci dan haka ya mik e ya nufi k ofa.. Har ya kama handle zai murd sai kuma ya juyo ya kalleta, yace Zan fita yau da wuri. Ina da bak i tun jiya cikin dare suka zo kuma yau da safe suke son komawa.. Get me something simple to eat, please. Kafin in dawo a masallaci. Bai jira jin me zata ce ba ya murza handle d in ya fice. Shiruu, tayi na y an mintuna chan kuma ta mik e ta tada sallah. A nutse ta gabatar da sallarta. Sai da ta idar ta yi azkar tukunna ta mik e ta d au wayarta ta fita a d akin. Tana shiga kitchen d in ta nemi globe ta kunna, ta fara k arewa kitchen d in kallo dan ita bama ta san ta ina za ta fara ba. Ganin babu lokaci yasa kawai ta soya omelet ta a salad ta d auko bread da kifin gwangwani ta had a masa sandwich da tea. Tray ta d auko ta jera akai ta d aura cup da tea flask d in da su madara da sugar da teaspoon ta ajjiye dik a kai sannan ta d au tray d in ta fita. Tana fita ta gansu akan dining shi da Abba duk sun shirya, da wasu takardu suna dubawa. A hankali ta k araso ta ajjiye tray d in sannan ta d an rissina tukun tace Abba Ina kwana Tunda ta fito Abban yake kallonta yana murmushi, ba k aramin dad i yaji ba Lafiya Alhamdulillah Yace da ita yana murmushi yana kallonta. A hankali ta d an kalli Aslam tace Ina kwana Sai da ya d ago ya d an kalleta tukunna yace Lafiya Sai kuma ya mayar da kanshi kan tray d in yace Thank you Daga nan ya maida kallonshi ga takardun Abba ne yace Princess yau abun son kai ne? Ina nawa cup d in? Da alama ma breakfast d in baku yi da ni ba Gaba d aya kunya sai ta rufeta cikin shagwab e fuska tace Abba ai ban san kaima zaka fita da wuri ba Tana gama fad in haka ta koma kitchen ta d auko cup ta kawo da tea spoon. Har zata sake komawa sai yayi sauri yace No wannan zai ishemu, wasa nake miki Murmushi tayi daga nan ta juya ta wuce d akin nasu. Tana cikin karatu taji fitarsu, sai da ta ida tukunna ta tashi dukda cewar d akin bai yi wani datti ba amman sai da ta goge ta share ta wanke toilet, ita kad ai tana ta mitar Aslam bashi da kunya wai k ato da shi amman ya wani shanye mata boxes tazo ta gani ma shi bai damu ba kenan! Sai wajen 9:00am sannan ta fito, lokacin gidan ba kowa daga ita sai Ummi. A cikin parlourn ta hango ta amman da alama ma bata san ta fito ba! Ta rafka tagumi tana kallon gefen tv d in da take ta faman aiki ita kad Sai da Hudan ta zo inda take ta ce Ummi ina kwana Tukunna tayi firgigit ta juyo, suna had a ido ta fara murmushi, kafin tace Lafiya, Alhamdulillah daughter. Ya kika kwana? Alhamdulillah itama Hudan tace tana me zama a kujerar gefenta 1 seater. Ki yi breakfast mana Cewar Ummi. kawai Huda tace sannan ta mik e taje tayi, har ta gama ta dawo ta zauna Ummin tana wajen bata ko chanja yana yin zama ba. A hankali ta zauna kafin tace Ummi tunanin me kike yi? Kallonta Ummin tayi kafin ta sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya tace Huda, gaba d aya har yanzu na kasa yafe wa kaina. Sannan guilt yak i barina In samu peace of mind! Ki taimaka ki yafe min sannan inaso ki rakani wajen Mamanki In nemi yafiyar ta na san na zalunceku Da sauri Huda tace Ummi dan Allah ki daina. Ni kam wallahi na yafe miki duniya da lahira Mama itama na san ta yafe miki. Ki kwantar da hankalinki ki daina yawan tunani, please. Ajiyar zuciya ta sauk e kafin tace Huda dukda cewa na san kina da kyakkyawar zuciya ba lalle ki aikata irin abunda na aikata ba, amman still ina me baki shawarar ki rok i Ubangiji ya tsareki daga aikata aikin dana sani Guilt d in bashi da dad i kwata kwata na rasa sukuni, nan san tayaya zan yafewa kaina ba. Ajiyar zuciya Hudan ta sauk e kafin tace Ummi, ki saka a ranki da ni da Mama mun yafe miki har abada! Sannan bamu rik e ki a zuciyoyinmu ba ko kad an! Mun yafe miki har gaban abada kuma ganin ki ne kamar komai bai tab a faruwa ba! Ta hakan ne zaki iya yafewa kanki. Wallahi Ummi kinji dai na rantse miki har k asan zuciyata na yafe miki kuma ban rik e ki a zuciyata ba kwata kwata an guntun murmushi Ummi tayi tana jin k aunar Hudan na sake shigarta, a hankali tace Na gode Huda but some facts will never change, Ina jin kunyar Abba sosai Ina jin kunyar sa Hudan ta bud e baki zata yi magana kenan! Suka fara jiyo kuka a waje Da sauri suka kalli juna sai kuma suka mik e suka yi wajen Kaya suka gani a zuzzube gefe guda kuma ga Jalila tanata kurma kuka tana tattare kayan nata. Tana ganin Hudan tayi saurin k arasawa inda take ta rik e mata hannu tana cewa Huda dan Allah ku taya ni bata hak uri, ni gani nake ma kamar ba ita bace ba ko kuma aljanuntane suka tashi! Lokaci d aya kawai tace wai In fitar mata a gida! Dan Allah Huda kar ku bari ta kore ni Dede nan Mom ta fito ba tare da ta kalle su ba ta k arasa ta finciko hannun Jalila ta wulla ta gefe sannan tace oya! Tattare ki fice kafin In kwace kud in motar da na baki Da sauri ta mik e tsaye ta share hawayenta ta k araso inda Mom d in take tsaye tace Mom dan Allah kiyi hak uri, wallahi ko wanke wanke da shara kika ce zan yi please Mom, dan Allah ki ara min kwana 7 Na yi miki alk awarin nan da sati d aya zan tafi wallahi. Cikin b acin rai Mom tace Nan da kwana bakwai na san me zaki yi??? Na san kalar asirin da zaki k ulla? Na san akircin da zaki shirya? Eh Jalila? Ta yi mata tambayar tana kallonta. Bata jira jin amsarta ba taci gaba Kinga, wallahi tallahi tun muna sheda juna ni da ke! Ki fice mini a gida Da sauri Jalila ta rik o hannunta tace Momina dan Allah dan annabi... Tass!! Mom ta d auke ta da wani gigitaccen mari, cikin fushi tace idan kika sake ce min Momin ki sai na datse miki harshe billahillazi. Ki kwashe tsummokaranki ki kama gabanki tun kafin raina ya ida b aci! Mom d in ta k arashe maganr cikin fushi da tsawa. Tun da ta kifa mata mari ta dafe wajen tana kallon k asa, bata motsa ba! Sai da ta bari ta kai aya tukunna ta d ago manyan idanuwanta da suka yi jaaa tana kallon ta! Cikin dakiya ta b acin rai tace Babu inda zan fita inje Adama. Dariya Mom ta kwashe ta ita kafin tace Perfect! tana me gwadawa da hannunta sannan ta ci gaba Wannan Jalilar dama nake so ta fito ba wachchar ba!. Yanzu zaki ga yadda ake hauka da rashin mutunci a cikin gidan nan! Tana gama fad in haka ta nufi gate Wani christian mai gyaran fulawa ta nemo da wani soja ta had o su su biyu ta dawo. Tana zuwa ta kalli Jalila tace Jalila ba da ni za kiyi wanann rashin kunyar taki ba da waennan za kiyi Tayi mata nuni da k artin bayanta, sannan cikin bada order ta juya ta kallesu tace Mai aikinta ce tayi mata sata, so ta
Chapter 15 · 0% Book details