Sashe 99
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda Dadah ya shigo sai yay tunanin duba Nimrah, dan rabonsa da ganin ta tun da suka fita da su Bilal. Shiru yayi yawa yana ganin ya dace yasan halin da take ciki. Dan yasan kaɗan daga aikinta ma ace bata a sashen gaba ɗaya, duk da ba lallai Mammah ta barta ba. Sashen nata shiru kamar babu kowa kuwa, dan fitulun falo ma ɗaya ce rak a kunne, sai a kitchen ne yake hango haske sosai. Amma duk da haka sai ya nufi bedroom.
Tura ƙofar da sallamarsa duk sun wanzu ne a tare, kasancewar kuma yayi cikin ƙaramin sauti ya saka Nimrah bata jiba har sai da ya maida ƙofar ya rufe. Ɗan juyowa tai kamar wadda ta tsorata, hakan yay dai-dai da saukar idanunsa a kanta. A take wata idea tazo mata. Sai tai saurin maida kanta gefe tana ƙoƙaro kukan ƙarya, cikin sa'a kuwa suka zubo, sai ga hawaye shar. Hannu tasa ta sake barbazasu suka jiƙe fuskar. Amma shi Dadah sai ya ga kamar sharesu take yi ne. Dan har ya ƙaraso gaban gadon yana kallonta ne.
“Dadah sannu da zuwa! Ya jiki? Wani abin kake so?”.
Ta jero tambayoyin tana ƙoƙarin sakkowa ganin yanda ya zuba mata kaifafafan idanunsa masu rikita lissafin ta. Baiyi magana ba, sai dai a karo na farko ya kai hannu ya riƙota dai-dai tana ƙoƙarin miƙewa. Maidata yay a gadon ya zaunar, kafin shima ya kai zaunen kusa da ita. Ƙoƙarin sinne kanta take, amma ya hana hakan ta hanyar kamo haɓarta ya ɗago fuskarta yanda zai iya kallo da ƙyau.
“Kuka ki ke yi?!”.
Kanta ta shiga girgizawa da sauri, ga kuma hawaye na ciko idon.
“Dadah ba kuka nake ba. Attaruhu ne ya faɗa min a ido ɗazun ina kitchen zan dafa noodles, shine har yanzu yake hawaye bai baje ba.”
Sai kuma tai shiru hawayen na sakkowa sharrr saman fuskarta. Ta taɓe baki da yanayin kuka irin na mai shagwaɓa idanunta na kallon cikin nashi. Sai ta fashe da kukan sosai. Bai sake ce mata komai ba, ya jawota jikinsa kawai ya rungume. Kamar abinda take jira kenan ta ƙanƙamesa tana ƙara ƙarfin kukan na gaske kam a yanzu.
Bayanta ya fara shafawa a hankali, “Faɗa min mi ya saka ki kuka?”.
(Anzo wajen) Cewar Nimrah a zuciya. A zahiri kam sabon kuka ta sake fashewa da shi harda shashsheka. Ta ce, “Dadah dan ALLAH ina son ka kaini bankaura ko akwai sauran ƴan uwanmu da suka rage a raye. Kaga a kwanakin nan sai mafarkin Ummana nake yi tana kallon ka tana kuka”.
Harga ALLAH sai da gaban Dadah ya faɗi da wannan magana ta Nimrah. Dan shi mutum ne mai girmama amana. Ummanta a barcinta tana kallonsa tana kuka ai akwai matsala kenan ko...?
Jin shiru baiyi magana ba, Nimrah ta sake cigaba da faɗin, “Kuma har cewa take (Nimrah kin watsar da zuri'armu. Baƙya zumunci da kowa. Tushena baida muhimmanci a gareki ne)”.
Dadah ya ɗan ja numfashi zuciyarsa na harbawa. Cikin jan ɓoyayyar ajiyar zuciya ya ce, “Ki kwantar da hankalinki kinji. Sannan ki sake ƙara mata addu'a. In sha ALLAHU dama akwai shirin da nake gobe idan ALLAH ya kaimu. Zan kaiki wani waje tare da Mammah”.
Zaram Nimrah ta tashi zaune. Cikin ƙyaƙyƙyafta idanu ta ce, “Dadah dan ALLAH ina ne?”.
Hancinta ya ɗan ja kaɗan da faɗin, “Bazan faɗa ba, idan munje ƙya gani”.
Taso taji, amma tunda yace gobe sai tace bari ta daure. Tambayarsa ta sake yi batun bankaura ɗin fa.
“Zan yi tunani shima”.
Daga haka ya miƙe yana ce mata bara yaje akwai inda zai je.
“Dadah baka da lafiyar?”.
Murmurshi kawai yay mata batare da ya sake cewa komai ba ya fice...
Tana ganin ya fita ta miƙe ta daka tsallen murna a gadon tare da faɗin, “Yess! Aiki ya fara. Muje zuwa Dadah na, da kanka zaka faɗa tarko na”. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariyar farin ciki.....
£££££££££££££
Koda Dadah ya fito a sashen Nimrah a babban falo ya iske Nabeeha zaune tana cika da batsewa, yaran dake sashen ta kesa baya son shiga sam. Kamar zai yi magana sai kuma ya wuce saboda fitowar Rayhana daga sashen Nabeeha ɗin. Itama baya ta take masa. Yayi zaton zatai masa korafin nata, amma sai yaji shiru. A dai-dai lokacin ne ma Daddy Imran ya kira shi dan yaji yaya jikinsa. Anan ne yake sanar masa abinda ya faru na samun mota da bomb a kusa da fadar shugaban Ƙasa. Sosai abin ya girgiza Dadah, dan ya fahimci mutanen nan fa bada wasa suke ba. Dama zaman gidan ya gundure shi, sai kawai ya tashi ya kimtsa ya fita batare da sanin kowa ba. Dan ko Nabeeha ta sake ficewa ta koma sashensa haɗo masa fruits kamar yanda tasan shine abincinsa na dare. Sai da ta fito kawai taji fitar mota a gidan, bata kawo shi bane sai da ta shiga sashensa taga babu shi, tai saurin leƙawa ta window sai ta hango motarsa daba wani cika hawa yay ba ce ta fita, dan dai-dai Malam Almu na maida gate zai rufe ne. Ranta ne ya sake ɓaci. Cikin takaici ta watsar da bowl ɗin...
Kai tsaye UNIT ZERO Dadah ya nufa, inda ya iske Yusuf kaɗai. Cike da munafunci Yusuf ɗin ke satar kallonsa, a ransa kam yana gulma. Shi kam baima san yanai ba, dan kai tsaye ɗakin sirri ya wuce bayan amsa gaisuwar Yusuf ɗin dake masa bayanin Maina ya kira cewar yaron nan na hannunsa. Dadah ya ɗan tsaya yana kallonsa, kamar bazai ce komai ba, sai da yana gab da shigewa ciki ne yaya magana, “Kaje yanzu nan ka amso shi.”
Da girmamawa Yusuf ya amsa da to yana miƙewa. Dan ya fahimci aiki ne na gaggawa...
Har yanzu jikinsa baya masa daɗi yanda yake so. Zaune ya kai cikin kujera, hakan yay dai-dai da isowar Daddy Imran tare da Dabo gidan. Kai tsaye kuma ɗakin sirrin suka shigo dan Yusuf ya gaya musu zuwansa tun a waje. Imran ya zuba masa ido cike da mamaki, yayinda Dabo ke gaishe shi. Kai ya jinjinama Dabon, ya ɗan harari Imran kuma. Sai kuma ya cema Dabo ya haɗo masa green tea.
Da girmamawa ya amsa yana ficewa. A lokacin ne Imran ke faɗin,
“Kafa harare ni, yanzu kaida baka da lafiya fisabilallihi miya fito da kai?”.
Bai bama Imran amsa ba saboda dawowar Dabo. Sai da Dabon ya ajiye masa green tea ɗin a gabansa sannan ya juya ya zubama Imran shi ma ya kai masa.
“Yauwa Dabo thanks”.
Imran ya faɗa yana amasa. Dabo yay ɗan murmushi yana juyawa ya fita.........✍️
114
.........“Jiya bayan rabuwar mu kasha wani abu ne daga hannun wani?”.
Ɗan murmushi Dadah yay na takaici, tare da faɗin, “Doctor yace maka nasha wani abu ne?”.
“Kwarai da gaske. Kenan kasan kasha kai ma?”.
“Humm daga baya ba”.
“Kana neman rikita ni fa? Ya akai hakan?”.
“Yarinyar nan dake tare da Nabeeha ce. Amma ina ƙyautata zaton ba aikinta bane sakata akai. Anyi amfani da shirmen ta ne kawai dana daɗe da fahimta”.
“Eh lallai magana ta girma. Kai amma yarinyar nan bata da hankali ta manta a gidan wa take?. Kuma tabbas na yarda da maganar ka, dan doctor ya tabbatar min badan kana da ƙarfin jini ba zaka iya yin sati a halin barci fa”.
“Humm mutanen nan ko. Idan sukai wani abun nakan ji kamar lokacin suna makaranta na ƙarshe suka dinga ɗauka a aji. Banda ƙarancin tunani kwantar da ni da kayan maye zai hana cigaba da aiki a kansu. Ko kuwa a tunaninsu ban shirya ba kafin na tunkare su?”.
“Suna sane, ruɗanin tunani ne kawai. Dan a yanzu suna a matakin da ko maciji aka jefa musu zasu kama dan neman tsira. Amma ita yarinyar nan ya akai ta samu wannan kusancin da su?”.
“Bana jin itace keda kusanci da su. Dan tsagerancinta bai kai can ba. Wani dai keyin amfani da ita”.
“Wa kake zargi? Dan ni matar nan ce tazo min a zuciya. In-law ɗin ka”.
“Ka saka mata ido dama ai. Sai dai itama bana jin hakan, duk da mayyar kuɗi ce. In kuma har ta kasance ita to ana amfani da ita ne itama. Amma bari muyi wasa da hankalinsu muga.”
“Shawara mai ƙyau. Ya kake jin jikin naka yanzu?”.
“Sai a hankali zai koma Normal. Ciwon kan nan ne dai ma yafi damuna.”
“Kuma doctor yace gajiya ce kawai. A hankali zai barka”.
“ALLAH ya sa. Kira Faro dan ya kamata naga mutum nan”.
“Shi ma wancan mataccen fa ya dawo hayyacinsa jiya. Gum ɗin bakin nasa ma sun cire shi”.
“Na tsani mutumin nan da yawa. Ko ganinsa bana son yi. Ni fa da zaku bi na nawa kawai yayi mutuwar gaskiya”.
“A'a dan ALLAH kayi haƙuri ba yanzu ba”.
“Mtsoww”.
Dadah yaja tsaki.
“Please Zaki na cool down. Idan ba haka ba gaskiya zan hanaka ganinsa gaba ɗaya to, sai nan da kamar wata ɗaya.”
Kafin Dadah ya bada amsa akai knocking ƙofar. Imran ya bada izinin shigowa dan suna ganin Yusuf ta magiji. Yusuf ya turo ƙofar ya shigo bayan ta gama surutan ta.
“Sir an iso da shi. A shigo da shi cikin falon ne?”.
Imran ya amsa masa da, “Eh mana ka shigo da shi”.
“Okay”.
Yusuf ya faɗa yana juyawa ya fita. Duk abinda suke Dadah na jinsu. Sai dai hankalinsa na'a kan screen ɗin makekiyar computer ɗin gabansa dake kusan quieter ɗin bangon. Sai da Yusuf ɗin ya fita sannan ya miƙa yana furzar da iska, shima Daddy Imran ya miƙe suka fice a tare.....
<%>°<%>°<%>