← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 113

Sashe 21

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da sauri Nimrah dake daga balcony ɗin upstairs tana kallonsu tabar wajen, hawaye share-share a fuskarta. Wani ɗan lungu ta samu ta maƙale, har sai da ta ga shigarsa ɗakinsa ta fito ta sauka downstairs. Itama bata kula su Abees ba ta shige ɗakinsu. Ruƙayya dake zaune a tsorace ta tashi zaram tayo kanta tana tambayarta dukanta Dadan yayi? Maimakon amsa sai kawai ta rungumeta ta fashe da kukan.
Ruky tai matuƙar daburcewa, itama tata muryar na rawa alamar zatai kukan ta ce, “Dan ALLAH ki daina kuka Ninah, ki faɗa min miya miki?”.
Yanzu ma bata iya bama Ruky amsa ba, sai da ta tabbatar kukan ya saka zuciyarta rage nauyi sannan ta sanar mata abinda ta gani tsakanin Dada da Nabeeha. Ruƙayya ta dalla mata harara. “Shine kuma abin kuka kamar wata sakarai. Ninah wai miyasa akan matar nan kike son zama wata lusara ne?”.
“To ni ya kike so nayi? Kawai fa kaina ya kama ciwo ya barni a ɗaki barci ya ɗauke ni sai yanzu na farka. Na leƙa ta window ɗin ɗakinsa na hangota ta fito a sashen ta, shine na fita balcony ashe shine tsaye tare da Uncle Haydar......”
“Kema gashi kin faɗa ita ta kawo kanta. Ninah itafa matarsa ce. Banda ma sun sami matsala daba wannan maganar ake ba. Ni ba wannan kishin irin nata nake so kiyi ba, kishi irin na kwatar ƴanci zamuyi. Dan haka al'amarinsa da matarsa yama daina damunki. Mu zauna mu tsara abinda ya dace kin fahimta”.
Kai ta jinjina mata, itama sai ta rungumeta tana faɗin, “Uhmmm my Trouble Queen na tsoron kishiya. Wlhy kin fara son Dada”.
Karamin dundu Nimrah tai mata a baya. Ruky ta sanya dariya.....

(+++)+(++++)+(+++)

Anan kam Biebah na zubama Faro abinci shi ko ya zuba mata idanu. Komai tayi ƙyau take masa. Ji yake a ransa anya zai iya dannewa kuwa. Shifa sai yanzu ma yake ji kamar Haysam bai kyauta masa da batun a ɓoye auren nan ba. Koba komai inda ta sani ai ya ɗan rage zafi. Amma yanzu komai yayi zata iya kallonsa a baibai ne. Haka dai dole ya shanye maitarsa yaci abincin.
Yana kammalawa kaɗan suka ƙara taɓa hirar ya miƙe akan zai wuce. Tayi mamaki, dan kafin yazo yace mata sai irin tara ɗin nan zai tafi. Dan haka ta kallesa cikin damuwa da ƴar shagwaɓa ta masoya. “Yaya amma cakai bazaka tafi da wuri ba. Miyasa ka canja kuma?”.
Gaba ɗaya sai lissafinsa ya nema ƙwacewa da salon nasa. Ya haɗiye busashen yawu, tare da runtse idanunsa da launinsu ya canja. Tsawon sakanni kafin ya buɗe ya ɗan tako kusa da ita gab har sai da ta motsa zata ja baya saboda kusancin nasu. Yay wuf ya taro ƙugunta. Ta waro idanunta sosai, sai kuma lips ɗinta ya kama rawa tana son yin magana.
Yatsarsa ya saka a lips ɗin nata yana sake kusanta fuskarsu gab da juna. Hakan ya sake daskarar da jinin Biebah data shiga tsilla-tsilla. Shi ko ko'a jikinsa. Saima nasa idanun da suka rine sosai ya riƙe natan da shi. Miryarsa na wani kalar komawa ƙasan maƙoshi ya furta. “Idan kika hanani tafiya zan aikata ba dai-dai ba. Dan wannan sojan naki bai san ya taɓa ya bari ba”.
Received at 6:24 AM Yana kai ƙarshen zancen ya wani irin janta ya saka a jikinsa gaba ɗaya yay ma bayanta zobe da hannayensa. Idan Biebah bata suma ba a wannan lokacin to ina tabbatar muku numfashinta ya tafi yawon duniya na wucin gadi. Dan numfashinta bai dawo da ƙarfinsa ba sai da ya sumbaci idanunta, tai wata zaburar da ya saka shi sakin dariya. A rikice ta kwace jikinta kawai ta nufi hanyar fita. Yana kiranta amma ko waiwaye.
Ya ƙara ƙarfin dariyarsa yana cizar lips. Dan harga ALLAH dariyar ta bashi. Ga wani shauƙi dake ɗawainiya da shi. Ai dolensa yay nisa da Biebah har tarewar nan. In ba hakaba ya rantse sai ya aikata ba daidai ba. Dama a yanayin mai son yin kuka an jefe shi da kashin awaki yake a halin yanzu.........✍️KIƊA A RUWA 3

39

.........Tun daga wannan ranar tsakanin Nimrah da Dada aka koma ƴar wasan ɓuya. Dan tun randa ta baro ɗakin nan nasa aka koma ƴar nesa-nesa, ba komai yasa haka ba sai haushin wannan runguma da Nabeeha tai masa. Sanda yake fita basu tashi ba. Yakan dawo daga office late, da taji motsinsa sai tayi yanda tai ta bar falo in har suna zaune anan. Sai kace wadda ta ma haddace lokacin dawowar tasa. Mammah na lure da su. Sai dai bata taɓa nuna ta fahimta ba balle tai magana.
      Shi kuma Ammar ya dage yana jan Ruky a jiki, kamar sakata aiki da wasu abubuwan. Amma baya yarda su keɓe dan zuciyarsa na raya masa abubuwa, ya kuma tabbatar idan ba ƴar nesa-nesa ɗin nan ba za'ai abin kunya. Ita kuma a hankali yanayin nasu ke mata tasiri, duk da tana shiga kunya musamman idan yayi wani abin da a can baya baya musu shi, yanzun ma bayama Nimrah sai ita. Shi kam Bilal yayi ƴar tafiya ne tun monday ɗin bayan ɗaurin auren, sai ta waya yake shoshalewarsa da Asma'un sa, har yanzu ba'a gamu fuska da fuska ba tunda aka ɗaura. Faro ma tun zuwan da yay ya rufama kansa asiri. Sai aka koma ƴar waya kawai da bada uzirin aiki-aiki. Duk da itama ta masa yajin kwana biyu saboda kunyar abinda ya faru.
         Yayinda angwaye keta dauriya anan iyayen biki ne keta shirinsu. Wato su Aunty Ummi da su Shariffa. Suma su Ja'afar cikin satin nan zasu bar ƙasar kawo kaya, daga nan zasu zo da komai na amare in sha ALLAHU. Mammah nata addu'a a garesu, sai in suna neman shawara suzo ta basu, sai dai ita ta maida hankali sosai akan su Nimrah musamman akan abubuwa masu muhimmanci da ya kamata iyaye da kansu su nunama ƴaƴansu game da rayuwar aure ba ko jira ƙawa ta gayama ƴarki ba ko wata. Abun na basu kunya, amma yanda take haɗe fuska ke sakawa su nutsu. Sun fara class ɗin su na Chef Yakudima 08135358038 kullum da safe, da yamma kuma su wuce islamiyya. Mai lassing ma na zuwa, dan sati mai zuwa zasu fara exams ɗin su.
     Su Hanoon dai ba ƙaramin kama kansu sukai a gidan ba yanzu. Dan tunda suka sha jiyyarsu suka tashi kwana biyu sai suka fahimci koma minene su Nimrah ne sukai musu shi. Sun gane hakan kuwa ta dalilin video ɗin da suka ɗauka. Yanzu basu da aiki sai zaman kallonsa suna dariya. Kuma basa yi a gaban Mammah. Kai ko Biebah da su Lailah ma, ita kanta mai wayar bata san ina suka saka video ɗin ba dan sun ɓoye shi. Hakan da sukai ya kawo masalaha sosai, musamman da batun jarabawar su da class ɗin Chef Yakudima 08135358038 ya sake kwashe rabin lokacin su Nimrah ɗin ma.

         ★★★★
Chapter 21 · 0% Book details