← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 113

Sashe 47

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........Suna fita daga VIP lounge ɗin Nimrah duk tana jin kanta a daburce. Dan har yanzu hannunta na cikin na Dadah tamkar yana tsoron ta gudu masa. Ƙofar gilashi ta buɗe a hankali.
Iskar dare mai sanyi ta bugi fuskokin su. A tare zaratan mazajen dake gaban baƙar ƙaramar mota ta musamman alamar su suke jiran suka shiga gyara tsaiwar su kawunan su a sunkuye.
        Cike da girmamawa ɗaya daga cikin su ya ɗan matsa gaban motar ya buɗe da sauri yana faɗin “Sir.”
    Dadah bai ce komai ba. Sai dai ya matsar da Nimrah jikin motar. A hankali ya furta, “Get in..”
          Nimrah dake jinta kamar tana cikin mafarki ta sauke nannauyan ɓoyayyen numfashi. Da ƙyar ta ɗaga ƙafarta da tai mata nauyi ta shiga. Ganin tanan zai shigo shima ta matsa can ƙarshen bangon waccan ƙofar. Sai da ya zauna, zama irin na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan aka rufe murfin. Da sauri drivern ya shiga da security guard ɗin daya buɗe musu motar. Motar ta tafi a hankali cikin runway area ɗin.
       A gaban private jet ɗin ta tsaya cak. Yanzu kam driver ya buɗe mata side ɗin da take, guard ɗin kuma ya buɗe ma Dadah. Nimrah ta ɗan saci kallonsa sanda wasu mutane biyu ke isowa inda yake. Wani ƙyau taga ya mata, musamman yanda hasken fitilun wajen suka haskaka shi, yana tsaye cikin girma da iko, ga yanda yake magana cikin natsuwa da wani tsaftataccen turancinsa abin ba'a magana..
      Kusan mintuna uku ya baro mutanen zuwa inda take. Baiyi wani magana ba ya kama hannunta kawai suka ƙarasa gaban jirgin. Ba yau ta fara shiga jirgi ba, amma kasancewar da Dadah a yau sai take jinta tamkar sabun shiga. Matakalar jirgin da aka sauke ta ɗan zubama ido.
      Ko jin gaisuwar da wani flight attendant ke tsaye a gefe ke musu batai ba. Sai da ya sake furta kalmar, “Please, sir.” san ta dawo hayyacinta.
       Dadah ya ɗan kalleta, murya a ƙasan maƙoshi ya furta, “Go.” yana sakin hannunta.
     Kanta kawai ta iya jinjina masa. Zuciyarta na bugawa ta fara hawa matakalar a hankali. Ji take ƙafafuwanta kamar ba nata ba. Dan Dadah yana biye da ita a bayanta gab. Duk da ba taɓa ta yay ba tana jin kusancin nasu sosai.
        Suna gama shigowa ta tsaya cak. Komai ya yi shiru da tsari. mai kyau, mai tsada. A ranta take raya dama haka privet jet ɗin yake? Dan duk shiga jirginta da tai a commercial plane ne. Dadah da yaga bata da niyyar cigaba da tafiya hannunta ya sake kamawa zuwa gaban kujeru masu laushi dake fuskantar juna. Ƙaramin table a tsakiya. Ga wani haske mai armashi na fitilu.
       Kasa haƙuri tai ta juya a hankali ta kalle shi. Yana tsaye a bayanta. Shanyayyun idanunsa a kanta. Da su yay mata nunin ta zauna. A zuciyarta ta furta (Miskili kafi mahaukaci ban haushi kenan). Zaunen ta kai duk da zuciyarta fal addu'ar ALLAH yasa ba sit ɗin dake facing nata ɗin zai zauna ba. Addu'ar tata kam bata ci ba. Dan inda bata son anan ya zauna, ya wani yi crossing ƙafafu cike da barazana irin ta hamshaƙan ƙasa. A dai-dai nan cikin guards ɗin nan data fahimci da su za'ai tafiyar ya ajiye laptop bag ɗinsa a kusa da shi. Bai ce komai ba ya risina sannan ya juya ya fita daga inda suke. Shi ko Dadan ko kallonsa ma baiyi ba.....

       ★))))))))★((((((((★

   First Lady ta jima batai magana ba kan zancen Nana. Sai kuma zuwa can tai murmurshi da faɗin, “Nabeehan ta sani?”.
         “Da wuya gaskiya. Amma dai ban sani ba dan yanzu dai duk suna ciki. Wannan sister ɗin tasu ce tazo”.
      “Jiddah?”.
   “Ban san sunanta ba gaskiya, amma dai suna kama. Sannan ta fisu yanayin nutsuwa”.
       “Itace. Kinga to barsu. Idan ta wuce sai kije ki sanar mata batun tafiyar yarinyar ko ki bari da safe”.
     “Okay Maa!”.
   Ta faɗa cike da salo. First Lady tai murmurshi daga can tana yanke kiran.. itama Nanah murmurshin tayi........

  ÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷

        Shiru ne ya mamaye cikin jirgin. Nimrah na zaune a kujerarta, hannayenta a harɗe a ƙirjinta. Gaba ɗaya ta maida hankalinta a kallon window, amma zuciyarta na wani wuri daban.
        Dadah ma har yanzu yana a yanayin zamansa na ƙafa ɗaya kan ɗaya, fuska a tsare, sai dai yanzu ya buɗe laptop yana aiki.
    A hankali ƙofar cabin ɗin ta buɗe. Wata flight attendant cikin nutsuwa ta shigo, murmushi a fuskarta. Cikin risinawa ta furta, “Good evening, sir. Would you like something to drink?”.
       A yanda tai magana da muryar mai laushi, cike da iyayi da girmamawa. Ya saka Nimrah kallonta a kaikaice. Cikin takaicin yanda taga idonta akan Dada ga wasu shegun kaya a jikinta a zuciyarta ta ayyana (Shegiya, ji yanda take magana kamar albasa mai lawashi).
      Shi Dadan ma batare daya kalleta ba ya ɗan ɗaga kai kaɗan kawai, a taƙaice ya furta, “Coffee.” idonsa akan screen ɗin laptop ɗin sa. Sai kuma ya ɗan juyo gareta.
       Ya ce, “And for her?”.
   Nimrah ta ɗan kalleshi da mamaki, amma da sauri ta kau da kai.
     “Nothing,”
  ...ta amsa a hankali tana hararar matar ta ƙasan ido.
       Flight attendant da bata san tanai ba kuwa ta jinjina kai da faɗin, “I’ll be right back, sir.” daga haka ta juya ta fita abinta tana taku cike da yanga. Ciki-ciki Nimrah tai ƙaramin tsakin da ya saka Dadah ɗago ido ya kalleta. Amma sai ta wani rufe ido kamar ba ita tai ba. Juyawa yay ya ɗan kalla inda yaga idonta na kallon kafin ta rufe, sai ya fahimci flight attendant ɗin take ma tsaki. Mamaki ya kama shi har yana tambayar kansa mita mata to?. Rashin mai bashi amsa ya sashi girgiza kai kawai ya cigaba da aikinsa.
     Shiru ya sake dawowa kamar ɗazun. Amma wannan karon mai nauyi. Dadah ya ɗan sake ɗago idanunsa ya kalleta kaɗan.
         “Kina fushi ne?”
     Tambayar tasa ta fito a sauƙaƙe, sai dai cikin nauyin furci daya saka Nimrah ta buɗe idanunta dake a lumshe. Ganin ita yake kallo tai sauri. Kawarwa. Cikin salon ɗan kumbura fuska a taƙaice ta ce, “A’a.”
     Muryarta da fukarta sun tona masa komai. Dan haka ya ɗan yi shiru kawai yana cigaba da kallonta kamar yana nazarin amsar. Sai kuma ya janye hannunsa daga kan laptop ɗin ya jingina da kujera ya zuba mata ido.
       “Hmm… not convinced”.
    Nan take zuciyarta ta motsa. Ta sake buɗe idanun ta kalle shi. Cikin shagwaɓa har idanunta na tara hawaye ta ce, “To Dadah ya kamata na yi farin ciki ne?”. Yanda tai tambayar a hankali, muryarta na ɗan rawa ga ƙyallin hawayenta na bayyana cikin idanunsa ya saka zuciyarsa motsawa.
      Cigaba tai da maganarta dan tasan ba amsa zata samu ba. “Ka tafi ba tare da ka faɗa min ba… ka kira ni kamar wani abu. Na kira back kaƙi ka amsa, yanzu kuma ka ce in zo ba tare da bayani ba. Dadah why?” Sai ta kau da kai da sauri hawayen da take riƙewa suka zubo.
           Mamaki, al'ajabi suka taru suka nema kashe Dadah da ransa. Wai wannan ƴar abar ce har tasan an mata ba dai-dai ba. A lallai yaga boni ashe ta bakin nata. Iska ya ɗan furzar da sake yanayin fuskarsa. Sai kuma ya ɗan sauke ajiyar zuciya kaɗan sannan ya furta,
      “Amma ai hakan ba komai bane ko?”.
          Shiru Nimrah na sake kallonsa. Ga wani irin nauyi da zuciyarta ke ƙara ɗauka. Baki ta taɓe da yanayin son sakin kuka irin na taɓara ta furta, “Dadah ba komai bane fa ka ce?.”
         Sai hawaye shaaaa da gudu a kumatunta.
      “Na fahimta.”
     Ya faɗa a hankali yana lumshe idanu da buɗewa a lokaci guda.
         Baki ta sake zumɓurawa ta juya gaba ɗaya tana kallon window hawayenta na cigaba da sauka. Dai-dai nan flight attendant ta dawo. Coffee ɗin dake hannunta ta ajiye a hankali gabansa.
      “Here you go, sir.”
   Yanzu ma ta faɗa cike da iyayi. Sai kuma ta kalli Nimrah.
      “Are you sure you don’t want anything, ma’am?”
    Nimrah ta balla mata harara kaɗan. Cikin yamutse fuska ta ce, “No, thank you.”
       Abin ma sai ya nema bama Dadah dariya. Dan ita kanta flight attendant ɗin da alama tasha jinin jikinta. Da sauri ta juya ta fita. Dadah ya ɗan girgiza kai kawai ya ɗauki cup ɗin coffee ɗinsa idanunsa suna kanta. Kamar yana son faɗin wani abu.. amma ya kasa. Bayan ɗan lokaci Nimrah da gajiya, da damuwa duk suka haɗu suka cinkushe mata zuciya idanunta suka fara rufe wa a hankali. Ba ta jima ba kuwa barci ya ɗauke ta. Kanta ya ɗan karkata gefe, hannuwanta data harɗe a ƙirji suka saki kaɗan.
       Dadah daya lura ya ɗan dakata da aikinsa na ɗan lokaci yana kallonta. Launin idanunsa suka ɗan sauya kaɗan. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali. Sai kuma ya ɗan motsa kusa da ita. Ba tare da ya tashe ta ba ya kai hannu ya gyara mata kanta dan kar wiyanta yay sanyi. Ɗan jinginata yay da ƙyau da seat. Tare da jawo ƙaramin throw blanket ya rufe mata jikinta.
        Koda ya koma mazauninsa kasa cigaba da aikin yay, sai ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci. Kamar yana nazarin fuskar tata. A kan lips ya furta “Stubborn girl”. Sai kuma ya murmusa da gyara zaman nasa ya cigaba da aikinsa. Sai dai sau da yawa idanunsa na komawa kanta. Kamar yana tabbatar da tana nan..........✍️
63
Chapter 47 · 0% Book details