← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 113

Sashe 73

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........Kamar yanda ya faɗa awanni biyu suka tashi, sai kusan mintina arba'in da suka ɗaukesu tafiya da dawowa. Yau kam bazai ce gajiya bace a tare da shi, sai dai matsanancin ciwon dake ƙulle da shi, ga ciwon kai da wani ɗan zazzaɓi-zazzaɓi. Shi kaɗai yasan a irin azabtuwar da yake daga jiya zuwa yau.
     Dama yau bai fita dako waya ba balle laptop, dan haka bai bar ko ɗaya a cikin guards ɗinsa ya masa rakiya ba. Yana taɓa handle ɗin ƙofar yana sassauta tie ɗin wuyansa. Tura ƙofar da sallamarsa duk sun wanzu ne a tare, kasancewar kuma yayi cikin ƙaramin sauti ya saka Nimrah bata jiba har sai da ya maida ƙofar ya rufe. Ɗan juyowa tai kamar wadda ta tsorata, hakan yay dai-dai da saukar idanunsa a kanta. Tai saurin maida kan nata gefe tana ƙoƙarin share hawayen da suka jiƙe fuskar, sai dai ta makaro tunda ya riga ya gani. Dan har ya ƙaraso gaban gadon da take kwance tun bayan yankewar waya tsakaninta da Ruky.”
     Ganin kallon da yake mata ya sa ta tashi tana murmurshi ita a dole zata basar.
        “Dadah sannu da zuwa! Yau kayi saurin dawowa.”
     Ta jero kalmomin tana ƙoƙarin sakkowa ganin yanda har yanzu yaƙi ɗauke kaifafafan idanunsa masu rikita lissafinta daga kanta. Baiyi magana ba, sai dai a karo na farko ya kai hannu ya riƙota dai-dai tana ƙoƙarin miƙewa. Maidata yay a gadon ya zaunar, kafin shima ya kai zaunen kusa da ita. Ƙoƙarin sinne kanta take, amma ya hana hakan ta hanyar kamo haɓarta ya ɗago fuskarta...
         “Kuka Kiddo?!”.
    Kanta ta shiga girgizawa da sauri, ga kuma hawaye na ciko idon.
    “Dadah ba kuka nake ba. Kawai dai...”
      Sai kuma tai shiru hawayen na sakkowa sharrr saman fuskarta. Ta taɓe baki da yanayin kuka irin na mai shagwaɓa idanunta na kallon cikin nashi. Sai ta fashe da kukan sosai. Bai sake ce mata komai ba, bai kuma cire idanunsa dake cikin nata ba. Har yanzu kuma dai yana riƙe da haɓarta. Sai da ya tabbatar tayi kusan na mintuna biyu kafin ya jawota jikinsa kawai ya rungume. Kamar abinda take jira dama kenan sai ta ƙanƙamesa.
         Bayanta ya fara shafawa a hankali. “Har yanzu ciwon kan ne?”.
     Kanta ta girgiza masa.
  “Mi ya sakaki kuka?”.
Shiru ta kasa magana.
“Da wa kikayi waya?”.
    Gabanta ya faɗi, kanta ta sake girgiza masa tana ɗagowa a jikin nasa. “Dadah ka gaji da yawa kayi wanka. Sai kayi barci ka huta”. Tai maganar tana ƙoƙarin sake miƙewa ita a dole zata masa wayo.
     Bai hanata ba, sai dai ya bita da kallo harta koma can inda kujeru suke ta zauna tana kunna television. Iska ya ɗan furzar a bakinsa kawai ya miƙe. Kayan jikin nasa ya rage, dan yana buƙatar yin wankan kamar yanda ya faɗa.
       “Tashi ki haɗa abinda duk zaki iya buƙata da bazai shafi kaya ba zamuje wani waje kwana uku”.
      Kanta ta jinjina masa tare da miƙewa ta kashe television ɗin. Yana shiga bayin ta ɗakko akwatinta. Sai kuma kamar wadda aka tsikara tai saurin ɗaukar wayarsa ta goge kiran da taima Ruky, tare da tura mata gajeren saƙo shima ta goge, sannan ta maidata ta ajiye. Tunda yace wanda ba kaya ba duk sai ta turesu gefe. Dan haka turarrukanta kawai ta ɗiba sai underwears da tafiya da nata zai fi bata nutsuwa. Wani mitsitsin kwalbar turare bayan wanda ta saka a jiya ta ɗakko, ta ɗan zuba masa ido tana tuna gargaɗin da Ammy (Lailah) tai musu daga ita har Ruƙayya kafin ta basu.
        (Ku adana turaren nan dan yana da muhimmanci. Ana amfani da shi ne kawai a lokacin barci. Kuma ɗan kaɗan ake sakawa a......) Ta lissafa musu duk inda zasu iya shafa shi. A lokacin kunya kamar ta narkar da su ita da Ruky, dan ko juna sun kasa kalla. Washe gari kuma sai ga Mamy (Shariffa) ta sake musu wani gargaɗin akan turaren dai. Ganin abinda suke yi ta ce, (Za ku ci ƙaniyarku, wataran ma da kanku zaku zo nemansa muma sai munyi muku yanga.)
       Tuna wannan abubuwan yasa ta sakashi a handbag shima. Dan ta tabbatar shima yana da nashi amfani, sai dai ƙuruciya tasa bata fahimci na mi ba. Tana gamawa Dadah na fitowa. Bata yarda ta kalleshi ba, shima komai baice mata ba ya hau shirinsa. Yayi ƙyau cikin wandon jeans blue da milk color ɗin riga, sannan ya kawo milk jacket ta gayu itama ya ɗora.
       Tsabar yanda Nimrah ta shagala a kallonsa har ya ƙaraso inda take bata farga ba. Sai da ya kama veil ɗin dake kanta ya hau yi mata rolling ɗinsa sannan ta saki ajiyar zuciya tana sauke kanta ƙasa saboda kunya. Baiyi magana ba shi dai, sannan tsaf ya naɗa mata veil ɗin fiye ma da yanda zatayi. Ya ɗauka ɗan pin ɗin data ajiye a kan handbag ɗinta ya matse mata shi.
     Hannunta ya kama zuwa gaban mirror, shi kuma ya tsaya a bayanta yana kallonta a haka. Hannu ta saka tana tattaɓawa da kallonsa itama ta cikin mirror ɗin. Ya ɗan ɗage mata gira yana tura duka hannayensa a aljihu. Sai tai masa murmushi. Cikin muryarta da tasha kuka tai sanyi ta ce, “Lah Dadah ka iya fa. Kodai shagon naɗa ɗankwali zamu buɗe ne?”.
        Karo na farko ya saki wani sassanyan murmurshi da ɗan kauda idanunsa a kanta. Sai kuma a hankali ya furta, “Muje”.
      Juyowa tai tana kallonsa sosai, shi kuma ya ɗauki laptop bag ɗinsa da ya haɗa nashi abubuwan buƙatar. Itama handbag ɗinta da shopping bag ɗaya data ɗauka ta saka underwears ɗinta ciki taje ta ɗauka a saman gado.....

      .....★★★.....

          Tunda Sanda ya fahimci kwana biyu Dadah baya gidan ya saki jikinsa. Yau ma suna zaune shi da malam Buba suna shan hantsi daya ɗan haska kasancewar yanayin sanyi ya fara tsawaita akai knocking gate. Malam Almu ya miƙe cike da mita dan a zatonsa Rayhana ce da ta fita ne ta dawo. Ya zare sakatar yana leƙawa. Mole dake tsaye daga gefe ya jiyo. Suna haɗa ido malam Almu ya waro idanunsa da faɗin, “Malam Buba. Kaine a gari? Maraba lale marhabun. Ka shigo mana. Ai nama zata shakiyyar can ce shiyyasa nayi jinkirin zuwa na buɗe.”
      Mole yay murmushi da faɗin, “Ba komai malam Almu. Fatan mun same ku lafiya?”.
       “A Alhamdullah sannu da zuwa sannu sannu.”
     Sanda ma da farin ciki ya tari Molen, kai har ma yafi na Malam Almu dan Sanda da Mole sunfi shiri. Hasali ma yasan zai dawo amma bai san yau bane dan ya raba masa dai cewar a cikin satin nan shekaran jiya da sukai waya. Bayan sun gaisa Sanda ke tambaya.
     “Malam Buba amma ka dawo ke nan ko?”.
      Mole yay ɗan murmurshi da bashi amsa. “Eh na dawo. Dama ai saboda mai jiki ne na jima haka. Bari ma naje na gaida su Hajiya dan su san da shigowata ko karna shagala hira.”
      Cikin gamsuwa sukace kwarai hakan yayi. Malam Almu ne dama mai musu irin wannan rakkiyar. Dan haka yanzu ma shine ya rakashi sashen Mammah. Inda ya tadda duk su Shariffa na nan. Harda Asma'u da itama ta shiga sashen Mammah ɗin yau dan jikinta da sauƙi. Ruky ce kawai babu zai mazan gidan, amma har Mu'azz na gida yau. Sai su Abees da ke makaranta kuma.
        Mammah ma tayi farin ciki da dawowar Malam Buba ɗin, sai dai wani abu mai taɓa zuciya ya faru da ita a lokacin da Mole ke matsawa kusa da ita ya ajiye wani ƙaramin buhu acewarsa ga tsarabar ƙauye nan bai sani ba ko zasu so?.
         Mammah dake bin hannunsa da kallo ta haɗiye yawu mai kauri tana sakin murmurshin ƙarfin hali da faɗin, “Mizai hana muso Malam Buba. ALLAH dai ya saka da alkairi. Ya bada ladan zuminci. Sannu-sannu”.
       Kan Mole a ƙasa yake jinjinawa da sakin murmushi. Suma su Lailah sukai godiya haka ma Gwaggo Khadijah. Daga haka Mole da malam Almu suka miƙe. Mammah ta ɗan bishi da kallo har yanzu zuciyarta na kai kawo. Sai dai a fuskarta bazaka taɓa fahimtar komai ba...

       Hummm komi Mammah ta gani?. Mi kuma hakan ke nufi?🤭🏃🏼‍♀️.

    ....Anan kuwa gate zance ne ya ɓarke tsakanin su Sanda da Mole mai amsa sunan Malam Buba a wannan gida. Sanda sarkin zance tuni ya ɓarke bama Mole labarin shagalin biki da suka sha. Da kaji da sukaci kamar ba gobe. Wai ranar har gudawa yayi saboda cin nama. Mole ya dinga dariya Malam Alamu na taya shi. Shi ko sanda ko dariyar ma bayayi saboda tsabar daɗin zance. Zuwa can kuma cikin gulma ƙasa-ƙasa ya ce, “Malam Buba kasan wani abu daya tafi dani? Har nake addu'a ALLAH ya bani kuɗi nima nayi?”.
        Mole dake dariya ya ce, “Sai ka faɗa Malam Sanda.”
      “Abinda babban Ogan gidan nan yayi, ana kai masa tashi amaryar washe gari yay sama da ita ko ina suka tafi oho. Yanzu haka suna can abinsu. Kaji wayon manya.”
     Wata muguwar bugawa zuciyar Mole tayi har tari na sarƙeshi.........✍️

        🤣🤣Sanda zai tayarma Mole hawan ruwa tunkan musan abinda ya kawo shi.
89
Chapter 73 · 0% Book details