Sashe 107
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........Kansa ya jinjina mata. Yayinda ƙamshin turaren data baza ke shigar masa har ƙarƙashin zuciya bama hanci ba. Amma da yake mazan fama ne bazaka ce wani abu ya tsikare shi ba. Ko kallon da yake mata a ƙasan ido ne. Hatta ita ma tana jin idanun nasa a jikinta amma data kallesa sai taga hankalinsa ba'a kanta ba.
Ganin yanda tai wani tsamm kamar wadda take a tsorace da shi ya sa shi ɗan sassauta gizagon fuskar. Cikin zurfin murya ya furta, “Zo nan”.
A ɗarare ta ɗago ta kallesa, ganin ita yake kallo tai saurin maida idanunta ƙasa. Da ɗan raɓe-raɓe irin na yaro mai tsoron shiga gida idan yayi laifi ta tako inda yaken. Sai kawai ta tafi zata duƙa. A hankali ya riƙota, batare da yayi magana ba ya sanyata a jikinsa kawai ya rungume.
Wata irin silent bahaguwar ajiyar zuciya ta saki a cikin ƙirji. Sai dai da yake a jikinsa take shi sai yaji yanda ƙirjin nata ya harba.
“Mike damun ki?”.
Cikin sanyin murya da ƴar shagwaɓa ta ce, “Ba komai”.
Bai yarda ba, dan haka ya cirota daga jikin nasa yana kallon fuskarta. Sai ta sake tura bakin.
“Shi bakin nan bai san yana tada rikici bane?”.
Ya faɗa a hankali yana tsareta da shanyayyun idanunsa. Zuwa yanzu ta fahimci abinda yake nufi da kalmar rikici. Dan haka kunya ta kamata. Sai ta wayance da faɗin, “Dadah bari na kawo maka ruw....”
Kamata yay ya maidota gaban nasa. Yana ɗan buɗe ido da lumshewa ya furta, “Barshi kawai. Wannan kwalliyan fa?”.
Cike da ɗan zumuɗi ta ce, “Yawo zamuje da Mammah”.
“Da iznin wa?”.
“Dadah na mana”.
Ta faɗa tana shigewa jikinsa.
Karo na farko yay mitsilin murmurshi. Tsawon mintina uku suna a haka. Kafin ta fito da kanta ta nufi kan mirror ta ɗakko ɗayan ɗan kunneta da sarƙan ta dawo inda yake. Sarƙan ta miƙa masa a marairaice ta ce, “Dadah samin”.
Sarƙan ya ɗan zubama ido na sakanni. Harta ɗago ta kallesa. Suna haɗa ido ta janye nata. Shi kuma sai ya kamo hannun nata ya ɗauki sarƙan. Gaban mirror ɗin nata ya matsa, itama sai ta ƙaraso da sauri. Tana tsayawa suka haɗa ido ta ciki. Murmurshi ta sakar masa mai ƙyau. Shi kuma sai ya ɗaga mata gira kaɗan.
Kanta ta duƙar, dai-dai yana duƙowa shima ya zuro hannunsa ya ɗora sarƙan a wuyanta. Koda ya maƙala a bazata taji saukar lips ɗin sa akan wuyanta. A hankali ta lumshe idanunta, tare da jan numfashinta yay sama sosai. Sai da ya ƙara mata ta biyu ta sake shi da ƙarfi. Sai dai ta kasa buɗe su saboda yanda hucin numfashinsa ke saukar mata a wuyan. Cikin kasa jurewa dan wani yammm take ji ta ce, “Dadah kana samun kiyashi a jiki”.
Yanda tai maganar a cikin maƙoshi sosai, ga numfashi na gargada ya sashi motsa lip kaɗan kamar wanda ke son yin murmushi. Sai dai bashi yayin ba. Ya dai koma kan ƙafafunsa da ƙyau yana kallon ta ta cikin mirror ɗin. Bai kuma ce komai ba game da abinda ta faɗa. Hannu ta saka ta rufe fuska, dan in yana mata irin kallon nan kunya take ji.
Baki ya ɗan taɓe kaɗan shima yana barin wajen da faɗin, “Turaren nan yayi yawa. Next a kiyaye har kwalliya ni kaɗai za'a dinga ma banda duniya”.
Daga haka yay ficewarsa. Murmurshi tayi tana ma zancen nasa fashin baƙi a zuciyarta....
....★Kai tsaye sashen Nabeeha ya nufa, dan tunda yaji shiru yasan yaran nata basa nan. Dama suke saka yake ƙin shiga. Duk da ma baida tabbacin tana gidan ko ta sake fitar, yanzu Mammah ke sanar masa Uncle Nasiru ya kirata yake sanar mata abinda ya faru da Mamansu...
Tunda ya turo ƙofar bedroom ɗin ta buɗe idanunta tare da juyowa. Idanunsa suka sauka akan bakinta, sai kawai yaji dariya na taso masa. Amma dai ya dake baiyi ba, fuskar dai ta saki kaɗan alamar murmurshi.
“Kin faɗi ne?”.
Ba ƙaramin haushi wannan tambaya ta bama Nabeeha ba kuwa. Ta kwakuso filos ɗin gadon ƙanana ta fara jeho masa. Murmurshin da yake dannewa ya bayyana. Bai kula jifan da take masan ba ya tsallake filos ɗin kawai ya ƙaraso inda take. A bakin gadon ya zauna. Cike da son zolayarta ya sake faɗin, “Serious na zata kin faɗi ne. Kinga lips ɗinki kuwa kamar na kwakwa”.
Harara ta balla masa. Zata sauka a gadon ya riƙota. Cikin ƴar gyaran murya ya ce, “Shike nan ba ƙwaƙwa ba”.
Zafin da yaji yasa kafin ta bashi amsa ya kai hannunsa wuyanta.
“Wai harda su zazzaɓi?”.
Kuka ta sakar masa. Sai kawai ya jawota ya rungumeta. Ƙamshin turaren Nimrah da taji ya sata yunƙurin janye jikinta. Amma sai ya hanata dan ya fahimceta sarai.
“Kinga abinda ke ɓata min rai da ke. Ki dinga kwantar da hankali akan al'amuran rayuwa....”
“Ni ka ƙyaleni, sai ka dinga ɗakko min ƙamshin turaren wata kana kawo min”.
“Ke sau nawa ina ɗaukar naki nakai mata. Tunda kun auri miji ɗaya dole yayta haɗa ku zuminci da turaren. Sai wace shekara ne zaki san kin girmi waɗan nan abubuwan ne?”.
“Sai randa ka daina zalunta ta”.
“Dama ni ban taɓa zaluntarki ba. Shirmenki ke saki fahimtar hakan. Idan kika nutsu kika bi yanda nake so zaki sameni fiye da yanda kike tsammani. Dan kina da wasu muhimman darajoji a wajena wanda ke kanki baki son da su ba. Wannan hayaniyar ce bana so sam. Sannan ki dinga tuna wacece Mammah a wajena. Badan tsayawarta ba da tuni sunanki ya canja daga yanda yake a yau a gareni”
Daga haka ya sake ta.
Karo na farko ta zuba masa idannunta. Maganganun Jiddah ne suka shiga dawo mata. (Aunty a tunaninki baya hankalce da yanda kike mu'amulantar Mammah ne? Ki farka a wannan barci kibar biyema Momy. Dan wannan ma babban giɓi ne a rayuwar aurenki da zare soyayyarki a zuciyar Yaya Haysam. Sannan babbar dama ce da yarinyar nan zata mamaye shi cikin sauƙi. Dan ita tana mata kallon uwa ne mahaifiya...)
“Kallon fa?”.
Ya faɗa yana kai hannu zai taɓa mata lips da sukai conono. Da sauri ta saka hannunta ta tare. Yay murmurshi kawai yana miƙewa. Hanyar fita ya nufa, sai da ya kama handle ɗin ƙofar ya furta, “Ki tashi kisha magani”. Daga haka ya fice abinsa. Dan in har ba ita ta sanar masa abinda ya faru da mamanta ba babu abinda ya shalleshi. Ai uwa ba tafi uwa ba. Dama yana shareta ne yaga iya gudun ruwanta, amma yanzu zai fara koya mata ladabi da gyara tarbiyyar uwarta datai mata tasiri...
---★★★---
Nimrah na gama shiryawa sashen Mammah ta fice. Ta samu Mammah da Gwaggo Khadijah sun kammala shiryawa suma. Ruky dai da alama Uncle Ammar ya matseta, dan ya dawo lokacin da take shirin wucewa wankan nan.
An ɗan ja lokaci sai ga Dadah. Lokacin Nimrah na cin naman kaza data ɗakko a kitchen. Suna haɗa ido ta kawar da kanta. Shima bai ce komai ba sai mamakin wannan ciye-ciye nata. Ba shi kaɗai ba Mammah kanta hankalinta ya fara komawa kan ciye-ciyen Nimrah ɗin. Dan a baya ba haka suke ba. Su da ma kullum cikin iyayin tsarin cin abu suke, su a dole basa son yin ƙiba.
Sai da taje ta wanko hannunta suka fito, dama Dadah ya riga su fitowa. Ta ɗan saci kallonsa a karo na biyu. Yayi ƙyau sosai cikin yadinsa ruwan ƙasa. Yanda yay masa luff-luff a jiki zaka san mai tsada ne sosai. Da kansa ya buɗe ma su Mammah ƙofa suka shiga. Ta zata da driver zasu fita sai taga shine da kansa zai yi driving ɗin. Tab ɗin abin mamaki kenan. Dan abu ne da bata taɓa gani ba. Kusan a tare suka shiga gaban, shi mazaunin driver ita a gefensa. Sai taji abun wani na musamman. Dadah yau zai tuƙasu a mota ai dole tace na musamman.
Malam Buba dake gate ya buɗe musu. Tunda ya dawo gidan sai yau Nimrah ke ganinsa. Zuciyarta ta harba da ƙarfi kamar yanda take mata a wancan karon. Cikin ɗan yanayi kamar na mai hakki ta kauda kanta. Dadah na lure da ita ta gefen ido. Sai dai bazaka gane hakan ba sam. Sai da suka fice a street ɗin gaba ɗaya ta saki numfashinta. Nan ma dai bai ce komai ba, sai ma amsa daya bama Gwaggo Khadijah dake tambayarsa Uncle Jamel kuwa ya sameshi a waya yau? Shine yace mata sunyi magana da safe...
Tafiya ce mai ɗan tazara, dan ba anguwarsu ɗaya ba. Nimrah dai nata kallon hanya, yayinda Gwaggo Khadijah da Mammah ke hirarsu. Shi ko driving ɗin sa kawai yake baki gum. Ko kiran wayarsa da ake tayi bai ɗaga ba sai ta Daddy Imran. Shima yana ce masa “Gamu nan” kawai ta yanke.
Anguwar da suka iso ɗin ma mai ƙyau ce. Sai dai bata kai tasu manyan gidaje ba. A gaban wani farin gate suka iske Daddy Imran tsaye a jikin motarsa. Dadah ma a kusa da shi ya samu waje yay parking. Shi kansa Daddy Imran yayi mamakin ganin shi ne yayo driving ɗin. Koda yake yasan Zak.. bai haɗa lamarin Mammah dana kowa ba a wannan duniyar. Shiyyasa yake mamakin yanda yake haƙuri da iskancin Nabeeha akan lamarin Mammah a yanzu, koda yake yasan halinsa sarai da iya basar da abu, sai ya tashi hukunci wanda yake hukuntawar ya koma baka tausayi. Shi ne ya buɗe ma su Mammah kafin ma Dadan ya fito..........✍️
122