← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 113

Sashe 15

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

        Ƙarfe biyar aka maido Dada gida kamar yanda aka ɗaukesa. A lokacin su Nimrah na sashen su Lailah da aketa shirye-shiryen suna. Dan haka basu san ya dawo gidan ba ma. Sai su Mammah kawai dake hira a falo da su Gwaggo Khadijah. Uncle Jamilu yana gidan Uncle Nasiru. Uncle Tasi'u kam ya tafi yau da safe maganganun Dada na cigaba da ragargaza zuciyarsa.
      Duk da yanda yake a gajiye sai da ya zauna suka gaisa da gwaggonin nasu. Sukai masa addu'ar ALLAH yasa an fara shiga office a sa'a. Dan da safe sanda ya fita basu haɗu ba. Ya miƙe zai haura sama Mammah ta masa zancen abinci. Duk da yana buƙatar abincin agogo ya kalla. Dan sauri yake zai ƙara fita tun yana office Faro ya tura masa saƙon an kama uku a cikin drivers ɗin nan.
         “Mammah bar abincin nan zan sake fita ne. Idan na dawo zanci. Yanzu kam ina sauri Haydar na jiran mu, yanzu zakiga Imran yazo”.
     Daga shi har Imran ɗin tausayi suka bata. Sunje wani aikin yini guda ba kuma hutu za'a fita wani. Batace komai ba, dan haka shima ya wuce sauri-sauri dan yana son watsa ruwa. Tashi tai da kanta ta nufi kitchen ta shiga haɗa abincin nasa fiye ma da cikinsa a basket, ta fito da shi falo ta ajiye. A mintuna talatin kaɗan ya ɗara sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga. Sai dai daga sama har ƙasa baƙaƙen kayane, amma marasa nauyi. Yanda ya sakko yana gyara bindiga a jikinsa ya saka Mammah kauda kanta. A ranta tana musu addu'ar kariyar UBANGIJI da fatan nasarar kammala wannan aiki mai haɗari lafiya.
        Kaɗan ya rage yay karo da Hanoon data taho akan sani. Dan ta fito a bedroom ɗinsu ita da Biebah ta hango shi yana sakkowa shine ta taho da sauri. Ko kallon inda take baiyi ba yay wucewarsa, zama ka rantse bai ganta ba ne. Suma su Mammah bai tsaya a wajensu ba yay musu sallama ya fice dan Imran har ya zo. Rashin su Nimrah a falon yasa Mammah tace Hanoon tazo ta bishi da basket ɗin abincin. Aiko daɗi kamar zai kasheta. Jikinta har rawa yake tazo ta amsa tabi bayansa. Sai dai yanda yake tafiyarsa har ya mata nisa. Ba arziƙi ta haɗa da gudu.
         Ta iso dai-dai yana buɗe ƙofar gefen driver zai shiga.
     “Dada gashi inji Mammah”.
   Muryarta ta shiga kunnesa. Bai juya ba sai da ya shiga motar, yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kai. Itako ta tsare shi da idanu fiki-fiki. Imran yay ɗan murmushi. Tare da faɗin, “Saka a baya.”
    Ba haka taso ba. Dan haka jiki a sanyaye ta buɗe bayan ta saka. Imran ya tada motar zasu fice cike da tsokana ya furta. “Humm wai kaga kallon da yarinyar nan ke maka? Kodai ƴar gida za'ai mutumina?”.
       Wani kallo Dada ya watso masa. Dan haka Imran ɗin ya kwashe da dariya. Dai-dai suna fita a gate ɗin gaba ɗaya. “Ai gaskiya na faɗa. Kaga Soja a waje soja a gida. Girman ka ne wannan babban kai, saura ta huɗu”.
Received at 5:36 PM       “Hummm”.
   Dada ya faɗa. Imran yasan iya amsar kenan. Dan haka ya cigaba da tsokanarsa. Sai da ya tabbatar ya kaisa bango sannan ya barsa suka koma maganar Office. Sun iso UNIT ZERO ana kiran magriba. Sai suka tsaya sukai salla a farkon anguwar sannan suka ƙarasa gidan. Da su Dabo suka fara cin karo ata ɗayan sashen da aka gyara dama dan ajiye mutane. Cike da girmamawa suka fara gaishesu. Imran kawai ya amsa. Gogan hannu kawai ya ɗaga musu.
      Sun ƙaraso wajen da aka shirya cells da yawa da ƙarfuna. Na can ƙarshe da ihu ke fitowa suka dosa. Faro na tsaye daga ƙofa hannuwa a aljihu fuskar nan babu ɗigon fara'a. Sai wasu jami'ai biyu cikin baƙaƙen kaya fuskar su a rufe idanun su da yankan baki kawai kake iya gani. Suna sakama mutane uku dake a kujera shocking a jiki, shine suke ihu.
     Isowar su Dadan ya saka Faro fitowa. Kauda kai Dada yay daga kallon matasan yaran ya maida kan faro. Dai-dai Imran na faɗin. “Wai sunƙi magana ne?”.
     Faro ya jinjina kansa yana furzar da huci. “Sunƙi. Sun dage akan aiki kawai aka basu basu san masu kayan ba. Sannan basu san minene a motocin ba. Sannan sunƙi faɗa mana inda sauran suke. Sai nake ga kamar da gaske basu sani ɗin ba.....”
           “Ƙarya suke yi. Koda basu san su waye ogannin ba sun san mi suka ɗakko. Sannan su dukkansu yara mutum ɗaya ne. Da ace ba mutum ɗaya ya basu horo ba, dole su samu saɓanin magana.”
     Dada ne mai maganar. Batare da ya jira amsawarsu ba ya tura ƙofar ya shige. Binsa da kallo Imran da Faro sukayi. Sai kuma suka bi bayansa suma cikin wajen.......✍️

Received at 5:36 PM
reacted with 🔥
34

.......Isowar sa gaban su ya saka cikin jami'an nan biyu saurin jawo kujera ya ajiyema Dada. Koda ya kai zaune wani kalar zaman ƙasaita yayi tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba musu idanu. Ɗakin yay tsitt, sai nishinsu na wahala kawai kake ji. Mintuna goma cif Dada ya cika yana nazartarsu a haka kafin ya warware hannayensa ya ciro abu a aljihunsa. Wata ƴar mitsilar kwalba ce sai syringe guda uku a ledar su. Baiyi magana ba ya shiga buɗe ɗaya a ciki tare ta ɓalle kan kwalbar dake tabbatar da ruwan allura ne a ciki ya zuƙa a syringe ɗin ya miƙama ɗaya a cikin jami'an. Amsa yay da sauri, batare da ya tambaya ba kawai ya dannama ɗaya allurar. Aiko sai da ya saki wani ihun azaba. Saboda ruwan allurar wani mugun raɗaɗi ne da shi, kuma yana fara shiga jikinka kake jin hakan. Mintina biyar basu cika ba jikinsa ya fara rawa. Ga zufa ta bala'i ta jiƙesa sharkaf. Sai ga shi ya fara rattafo zance sala-sala.
      Cikin razananniyar murya Dada ya jefa masa tambaya, “Kayan miye kuka wuce da shi?”.
         “Mun ɗakko waɗan nan motocin daga gaɓar ruwa. Kuma a haka aka shigo dasu ta kwantaina. Makamai ne a ciki da bama-bamai. Mun kaisu inda aka umarcemu ne kawai”.
        “Waye Ogan ku?”.
    “Oga Jo kawai muke kiransa. Ban san ainahin sunansa na gaskiya ba”.
    “Tun yaushe kuke masa aiki?”.
“Shekara uku ke nan”
“A ina yake zaune?”.
“Bamu san taka maimai wajen zamansa ba. Kawai idan zai sakamu aiki ne yake gaya mana inda zamu sameshi.”
        “Ku nawa kukai aikin?”.
    “Mu goma ne”.

Shiru Dada bai sake tambayarsa komai ba. Sai ma wani ruwan allurar ya sake ɗiba ya miƙa musu. Na kusa da shi shima aka danna masa. Kamar dai na farko shima tuni jikinsa ya rikice. Koda Dada ya tambayesa. “Ina sauran wanda kukai aikin?”.
      Baima bari ya rufe baki ba ya fara bayani. “Akwai aikin da zasuyi ma Oga. Shine suka je ganawa da shi. Amma na tabbatar zasu dawo gida sun kwana a yau ɗin”.
        “Ku miya hanaku zuwa?”.
    “Kowa da aikinsa.”
“Dan ALLAH Oga karku kasheni, wlhy azaba nake ji a jikina kamar ana dafa ni”.
       Dada bai tanka masa ba. Ya bada shima ɗayan akai masa allurar. Shima yana fara nashi vibration ɗin ya jeho masa tambaya.
      “Ina kuka kai kayan?”.
   Tsaff ya bada address ɗin wajen.
“Mi za'ayi da su?”.
“Bamu sani ba muma. Amma mun ji Oga Jo kamar na magana da wani a waya cewar za'a fara kai su jihohi daban-daban, amma bamu san akan aikin minene ba. Dan yanzu haka yan uwan mu akan haka sukaje ganawa da shi”.
        Ba ƙaramin zafi zuciyar Dada keyi ba. Komai bai sake cewa ba ya miƙe ya fice. Bayansa su Faro suka bi suma zukatansu na zafin. Tsumin sojojin na ƙoƙarin tashi. Dan wlhy badan suna da target ba yaran nan bazasu kwana da rai ba yau......

       ★★★
Chapter 15 · 0% Book details