Sashe 93
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike yake da buƙatar yin wanka. Dan gaba ɗaya kayan jikinsa sun gama takura masa. Ga gajiya da hayaniyar da yasha yau. Bai wani saka al'amarin Nabeeha a ransa ba dan yasan halin kayansa. Ya zare kaya kawai ya shiga wanka bayan ya gama ganin abinda Nimrah ɗin tayi a wuyansa, dan Nabeeha bata goge duka ba. Ya ɗan jima kafin ya fito. Bai yi mamakin samun Nabeeha ta shigo ba. Sai dai yanda ta cika tai fam ya sashi yin murmushi yana kauda kansa.
Sanin zai koma wajen Mammah ya sa ya saka jallabiya a maimakon kayan barci. Kafin ya iso inda Nabeeha take a bakin gado ya zauna kusa da ita. Kai tsaye ya ce, “Bani ruwa”.
Batare data kallesa ba ta ce, “Ka muje falo ga abinci”.
“Kin san bana cin abinci da dare ai. Ki bani ruwan sai ki bani green Apple kawai”.
Miƙewa tai batare da tayi magana ba taje fright ɗin dake ɗakin ta ɗakko masa ruwan da cup ɗaya ta dawo.
Ruwan kawai ya amsa ya barta da cup ɗin. Da yake a buƙace yake da son sha bai ma fahimci a buɗe ruwan yake ba ya cire murfin kawai ya kai bakinsa. Sai da yay bismillah kamar yanda ɗabi'arsa take sannan ya fara sha. Tas kuwa ya shanye shi ya miƙa mata robar kamar ba yanzu yasha ruwa a wajen Nimrah ba.
Koda yake shi mutum ne mai son ruwa sosai. Shi kansa bai san irin adadin ruwan da yake sha ba a rana. Idanunsa a rufe ya dafe jijiyoyin kansa dake harbawa da duka hannayensa. Sai da yay kamar mintuna biyu a haka sannan ya buɗe idanun nasa ya ɗauki wayarsa dake a bed side drawer da tai motsi alamar shigowar saƙo. Waya ce ta aiki mai muhimmanci, kuma yana saka ran su Faro ne, dan haka ya kalla Nabeeha da nufi sakata aikin da zata bashi waje... Sai dai me? Yana motsa lip kansa yay wani ɗan sarawa, hannu ya sake kaiwa yana ƙoƙarin dafe shi saboda nauyin da yake neman fara masa.
Ita ko Nabeeha dama bata lura ba ta miƙe ne kawai ta nufi ƙofa ɗauka masa Apple da yace.
Ganin haka ya sashi yunƙurin sake ɗaukar wayar. Abu kamar wasa yana ƙoƙarin fara duba saƙon da aka turo masa idonsa ya fara juyewa dishi-dishi....
Mamaki ne ya fara kama shi kam, ya shafa idanun tare da buga kan nasa kaɗan amma ina. Karo na farko ya ambaci sunan ALLAH a bayyane. Hakan ne ya saka Nabeeha dake shigowa ta ƙaraso gabansa da sassarfa ta zube tana kama masa kan itama da faɗin, “D. Miya faru? Kanka ke ciwo ne?”.
Kai ya girgiza mata da ƙyar, ya motsa lips da nufin mata bayani amma yay masa nauyi. Sai kawai ya yamutse fuska yana lumshe idanu. Miƙewa tai ƙoƙarin yi zuciyarta na tuna mata batun Nimrah sai dai cikin rashin sa'a yay baya zai zube a gadon shi kuma. Kasancewar tana a jikinsa kawai suka tafi gaba ɗaya.
Duk da a tsorace take da wahalar da tasha ɗazun a hannunsa da safe, ga yanayin da yake ciki. Jinta kwance a jikin nashi ga fuskarta akan tashi tana shaƙar ƙamshin mayen turarentasa na barci da ko'a baya yana da matuƙar tasiri a gareta balle a yanzu kawai ta samu kanta da rungune shi sosai. Duk da kanshi ya fara juyewa irin na wanda yasha ƙwaya saƙon Nabeeha bai gagara tasiri a jikinsa ba, har takai ma ya riƙota shima da irin riƙo na sallamawa. Sai dai ƙarfinsa ya fara rauni. Amma hakan bai hanashi son biyama gangar jikinsa da zuciyarsa muraddinsu ba.....
÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷
Faro daya tabbatar idan Dadah yaga saƙonsa zai kira ya ƙara jujjuya wayar cike da ƙosawa. Tun yana ƙirgen sakanni har ya koma mintina. Ganin fa kamar wasa wankin hula zai kaisu dare kawai ya danna masa kira. Ina harta tsinke babu amsa. Ya sake gwadawa a karo na biyu. Amma nan ma ba'a ɗaga ba.
(Mike faruwa. Yasan Haysam akan aiki. Kuma ɗazun yayi waya da Imran akan yau zasu kama Ojo. Ya kuma san Imran zai sanar masa) Akalar kiran ya maida kan Imran. Cikin sa'a bugu ɗaya ya ɗauka. Faro ya sauke ajiyar zuciya. Ko gaisuwa basu tsaya yi ba ya ce,
“Imran halan ka manta baka faɗama Boss muna bakin aiki ba?”.
“Ah. Na faɗa masa mana. Miya faru?”.
“He didn’t pick my calls seven times.”
“Oh my God. Inaga ciwon kan ne. Dan babu jimawa muka rabu da shi. Yan zu wani abu ya faru ne?”.
“ALLAH ya bashi lafiya, akwai matsala kam gaskiya. Dan guy ɗin nan fa baya gidan nan. Sai wasu mata da muka samu. Sun tabbatar mana kuma ya kai sati biyu ma baya nan”.
“Mata! Su kuma su waye to?”.
“Humm garkuwa yayi da su. Sunce kuma ana fita da wasu ma. Sannan ana shigowa da wasu. Sai dai basu san ina ake kaisu ba.”
“Lallai akwai matsala. Yanzu dai idan kuka bar yaran nan da nufin masa tarko bamu sani ba ko ya gane ana bibiyarsa ne ya bada ƙafa. Idan aka kwaso su kuma nan ma akwai matsala. Tunda zata iya yiwuwa bai sani ba kaga mun bashi haske. Zaɓi ɗaya ne damu yanzu. Idan akwai maɓoya wasu a yaran su nema a dakaci zuwansa. Mu kuma nan ka dawo mu kafa sabon binciken sanin ina yake a yanzu”.
Baza'a rasa mafaka ba, duk da itama zata iya zama mai haɗari. Dan tunda yazo ya kafa wannan gidan a jeji babu yanda za'ai ace bai san sirrin wajen ba. Sai dai bamu da zaɓin daya wuce hakan.”
“In sha ALLAHU mune da nasara”.
“ALLAH yasa. Sai ka jini”.
Daga haka Faro ya yanke kiran.
Imran da zancen Dadah ya tsaya masa a rai shima layin nasa ya fara kira. Dan yasan ƙarfe tara da wani abu baza'a ce dai ya kwanta ba. Dole akwai dalili. Family layinsa ya kira. Ga shi dai tana shiga amma ba'a ɗaga ba shima har sau uku. Sai yaga kawai bari su bashi lokaci zuwa anjima koma safiya....
★___________★
Kuka sosai Nimrah tayi bayan wucewar Dadah. Dan wani irin nauyi taji zuciyarta ta mata. Ga ƙunci daya mamayeta. A sati biyu ya saba mata da abubuwa da yawa da take jin shaƙuwarsu ƙololuwa. A yanzu bata ƙi su yini tare su kwana tare ba tana ganinsa a kusa da ita. Sai dai tasan hakan yaudarar kanta take. Dan dole ta raba shi da wata. Dole akwai ƙa'idar da zata ganshi yanzu. Wataran ma ƙila ta kwana ta yini bata ganshi ɗin ba.
Tabbas ta jinjina ma mata masu abokan zama. Dan yanzu ta fahimci abinda ake kira da kishin. Sai ma ta ɗan ji zata iya sassautama Nabeeha dan wlhy tayi namijin ƙoƙari. Sai dai hakan ba yana nufin zata bar mata Dadahn bane. Dole ne su zuba mai sa'a ya ɗauki kambu. Amma in har bata shiga huruminta ba itama zata kauda kanta ta barta da halinta kawai. Idan kuma har ta kasa riƙe girmanta ko tace zata cigaba da raina musu Mammah to anan fa ne tsakaninsu babu ragi babu ragowa. Dan an taɓa abinda bazata iya kauda kai ba............✍️
108
.........Anan ɓangaren Dada kam baida lafiya. Abinda ya sha a ruwan da Rayhana ta ajiye da abinda ya shiga tsakaninsa da Nabeeha ya saka shi a wani hali. Da asuba da ƙyar ya iya yin wanka daya kasa yi tun dare ya fito. Sai dai duk yanda yaso fita sallar asuba hakan ya gagare shi. Dole ya yita a ɗaki yana layi da riƙe kai. Wani irin azababben ciwon kai yake ji tamkar zai iya rasa ranshi. A haka ya sake komawa gadon da ƙyar ya kwanta.
Wajen 7:30 sai ga kiran Imran. Da ya kwana da shi a zuciya, da ƙyar ya iya ɗaga wayar. Koda ya amsa sallamar Imran ɗin daya fara tsokanarsa sai gabansa ya faɗi. A rikice ya shiga jera masa tambaya. Shine yace masa kawai baya jin daɗi, ciwon kan jiya ne bai sake shi ba. Sosai hankalin Daddy Imran ya sake tashi, dan haka ya yanke kiran kawai. Shine yanzu suke shigowa gidan tare da amintaccen likitan Dadahn dake kulawa da case ɗinsa na poising anan gida.
A falon shi suka zauna Imran ya kira wayarsa. Yanzun ma saboda barci daya fara ɗaukarsa da ƙyar ya iya ɗagawa. Dan bai tashi yaga Nabeeha a ɗakin ba. Yasan fushi tayi saboda yazo tashinta salla kawai ya kirata da sunan Nimrah, shi kuma har ga ALLAH an samu matsala ne saboda kwanakin nan na sati biyu da ya samu kusanci da yarinyar sosai. Amma badan ya wulaƙanta ta yayi ba.
“Muna falonka, zaka iya fitowa?”.
Daddy Imran ya katse masa tunani.
Ban san amsar da Dadan ya bashi ba daga can. Yadai miƙe yana faɗin, “Bari kawai mu shigo ciki idan ba damuwa.”
Amsar daya sake bashi ce ta sashi yanke kiran yana cema Doctor, “Ina zuwa”. Daga haka ya wuce bedroom ɗin na shi..
★=========★
Nimrah sarkin nauyin barci da ƙyar ALLAH ya taimaketa alarm ɗin data saita ya tashe ta. A hakan ma sai da ta makara. Tana idar da salla ta zauna shiru zuciyarta na kai-kawo. Yayinda yanayinsu da Dadah a kowacce safiya kamar haka ya fara zuwa mata. Turashi tai da tsiya-tsiya, ta ɗauki Alkur'ani ta hau karatu.
Tayi nisa kamar abin almara taji ringing ɗin waya a ɗakin. Wayar ma irin ƙaramar rakani kashin nan. Mamaki ne ya kamata. Dan tasan ita dai bata da irin wayar. Cikin waige-waigen da take ta fahimci inda wayar take. Alkur'anin ta rufe, tare da miƙewa ta je inda wayar take ta yaye labulen. A jikin window ne aka saƙalata. Ƙirjinta ya ƙara bugawa. Cikin rawar hannu da karato addu'ar da duk tazo mata a baki ta ɗakkota.
Dai-dai nan kiran ya sake shigowa. Ta sake tsirama number ido. Dan number ce da har abada bazata manta da ita ba. Zuciyarta ta shiga raba mata hankali akan ta ɗaga ko ta barshi. Ɓangaren da yafi ƙarfafata tabi, ta dangwarar da wayar ta koma inda take karatun ta ƙarasa. Duk a cikin son ƙarfafa kanta ta sake komawa gadon tai kwanciyarta tana addu'a da fatan barci ya ɗauketa.....
<%><%><%>