← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 113

Sashe 97

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Yanzu ma dukkan abinda ya dace doctor ya masa. Ya ƙara masa allura guda ɗaya sai magunguna da yazo masa da su yace sai yaci abinci ya sha. Sai ruwan sanyi da yace a ɗan saka masa a jikin dan saukar zazzaɓin. Daga haka ya miƙe. Dai-dai da isowar su Mammah sashen. Dan wayar Nimrah da Imran ya ɗauke a jikin Dadahn ya miƙa mata tana fita falo dan basu damar duba shi kawai tai kiran Mammah tahau yi mata kukan wai Dadah bashi da lafiya. Shine fa hankalinsu ya tashi suka nufo sashen.
        A falo suka iske Nimrah tana kai-kawo. Suna gama hawowa ta gudu wajen Mammah ta rungumeta. Tashi hankalin Mammah ya sake yi, itama ta rungumeta cikin sigar lallashi amma batace komai ba. Sai su Gwaggo Khadijah ne ke tambayar miya same shi??. Bata samu basu amsa ba Daddy Imran da Doctor suke fitowa a ɗakin. Cikin mamaki yake tambayar su, Gwaggo Khadijah tace Nimrah ce ta kira Mammah. Bai ce komai ba face girgiza kansa, sai kuma yace su shiga to shi bari ya raka likita.
      Basu shigan ba kai tsaye, sai sukace Nimrah taje ta sanar masa. Koda ta shiga ta isar da saƙon su yaja sakanni bai buɗe idanunsa dake lumshe ba. Sai zuwa can ya buɗesu ya zuba su a kanta. Ƙasa tai da nata tana wasa da yatsun hannunta.
       “Waye ya faɗa musu?”.
   Yay tambayar a dake. Baya ta ɗan matsa na jin tsoro. Cikin in-ina ta ce, “Dadah kayi haƙuri naji tsoron ganin yanda kake yi ne”.
      Kansa kawai ya girgiza da faɗin, “Zoki gyara min filon nan”.
      A ɗarare ta ƙarasa inda yake, shi kuma ya yinƙura da ƙyar ya tashi zaune. Filon da ya tashi a kai ta ɗauka ta saka jikin fuskar gadon ata bayansa, shi kuma yaja bargon dake gefen ƙafafunsa ya rufa. Sai dai iya ƙugunsa yake. Sannan yace taje ta shigo da su...

       ★Babu wanda tausayinsa bai kamasu ba a cikinsu. Dan kallo ɗaya zaka fahimci baya jin daɗi, duk da kuwa shi mutum ne mai tsananin shanye abu da kame kansa. Amma yanda launin idonsa da jijiyoyin kansa ke miƙe raɗa-raɗa sai kamewar tasa ta gagara shanye komai.
       Addu'a sosai sukai masa, tare da fatan samun lafiya mai ɗorewa. Sannan Gwaggo Khadijah ta fara faɗan miyasa tun daren basu kirasu ba. Ƙaramin murmushi kawai yayi amma bai ce komai ba. Ita dai Mammah batama yi magana ba tun addu'ar da tai masa, tunaninta nakan ina Nabeeha? Dan ita ya dace su gani tare da shi ba Nimrah ba, kar dai Muhammad ɗinta ya zama mai fifita sashe akan sashe a tsakanin matan nasa. Yaje da Nimrah tafiya ya dawo sannan ya cigaba da kwana da ita alhalin Nabeeha ya dace ta amshe shi. Sun ɗan ja mintuna a ɗakin dan har Imran ya dawo abu dai na sukar Mammah a rai, shima sun gaisa sukai masa ya mai jiki, ya amsa musu da cewar da sauƙi ciwon kai ne kawai yay masa tsanani. In sha ALLAHU doctor kuma yace zuwa anjima kaɗan komai zai yi dai-dai, yanzu ma yace a sama masa abinci mai sauƙi yaci ya sha magani ya sake kwanciya.
       Sai a lokacin Mammah tai maganar ina breakfast da aka kawo tana kallon Nimrah dake lafe a jikinta. Nimrah ta ce, “Ga shi nan”. Tai maganar tana miƙewa inda yake.....

         ¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

   Tunda Amimah tazo ta sake sanar mata Dadah ne fa baida lafiya shiyyasa ashe Imran yazo hankalinta ya tashi. A rikice take tambayar miya same shi. Amimah tace, “Ban sani ba Aunty, kece ya kamata kije ki jiyo mana. Dan su Mammah ma har sun zo sun fita, kuma yarinyar nan tun ɗazun tana tare da shi. Kinga sai suma ɗauka ke abin bai dameki ba ko.”
      Nabeeha dake jin kamar zuciyarta zata fito ta nufi sashen Dada, sai dai zuciyarta na'a cikin matsanancin tsoro musamman akan abinda ya faru tsakaninsu asubahin yau. A falo ta samu Imran yana waya, bata tsaya bi takansa ba dan wani jin tsanarsa take a ranta ta wuce bedroom ɗin da suka kwana jiya. Ƙofar kawai ta tura ta shiga batare da neman izini ba balle yin sallama. A dai-dai wannan lokacin Nimrah data gama haɗama Dadah tea ɗin da yace kaɗai zai sha ta isa gaban gadon inda yake. Yanda aka turo ƙofar ya saka zuciyarta bugawa, ta jiyo da sauri tana kallon ƙofar kamar yanda Dadah ya ɗago shima ya kalla wajen. Cikin ido Dadah da Nabeeha suka kalla juna, sai ta tsaya cak gabanta na faɗuwa. Nimrah kuwa kanta ta kawar kamar bataga komai ba. Cike da rashin ji da son ɓatama Nabeeha rai ta canja shawara, maimakon bama Dadah tea ɗin tabar wajen kamar yanda tai niyyasa sai kawai ta kai zaune a bakin gadon kusa da shi, duk da wajen baida yawa saboda yana zaune ne a baki-baki ƙafafunsa a miƙe a yanda su Mammah suka barshi.
      Nimrah ɗin ya kalla, sai ya ga fara'ar fuskanta ta ɓace ɓat, baice komai ba ya ɗan matsa mata danta zauna da ƙyau, dai-dai Nabeeha na ƙarasowa gaban gadon itama ranta a ɓace da ganin zaman da Nimrah tayin, sannan itace da mijin mizai sa ita ta zo, wannan munafunci ne kuma tasan Imran ne ya ƙullashi, zako tayi maganinsa wlhy. Sai dai cikin danne zafin da take ji ta furta,   
       “Subahannallahi My D. Miya faru ne? Yanzu nake ji baka da lafiya, dama ciwon kan bai sauka ba har yanzu?”.
      Tai maganar tana hawowa gadon sosai ta ɗayan ɓangaren, ta kai hannunta a goshinsa, idanun kawai ya ɗan lumshe da ƙoƙarin jinjina mata kan nasa, bata damu ba ta sake sakko da hannun saman wuyansa. Wani irin abu yazo ya tokare maƙoshin Nimrah, sai dai ko kallon inda Nabeeha take bata sake yi ba. Sai ma kofin tea ɗin data miƙama Dadan.
        Nabeeha ta saki ɗan murmurshin ƙeta, dan a safiyar yau ta zauna tama kanta huɗubar shirya abubuwa masu yawa akan Nimrah. Ta saka a ranta zata ajiye shawarar kowa ta gina ra'ayin kanta tunda itama dai ai mace ce, sannan mutum ce ba robot ba balle ta zama abar control ɗin kowa. Tafi kowa sanin wanene Haysam, sannan tace ta zaɓi abinta matsayin miji, duk tsanani kuma ta yarda zata zauna da shi da halinsa. Mizai sa ta cigaba da zaman yin rayuwa a gidan aurenta tare da wata banzar yarinya. Dole ne ta kawar da ita. Dan akan Haysam wlhy sai inda ƙarfinta ya ƙare, ko Mammah data haifeshi dole ta bar mata shi balle wannan shashar yarinyar ƴar cikinta. Badai ita ta aiko Haysam da shatin kiss ba dana turare a jiya. Ta jira nata aiken dan ita a zahiri zata yi.........✍️

      Ke wlhy ƙawata matsalar ki kenan🥱. Mi kuma ya kawo a zahiri zakiyi🥺? Ai ya hakan ne zaki sa a cimu da yakin🥲🚶.
112

.........Tunaninta ya yanke sakamakon furucin Nimrah da itama taji a ranta lokacin da shirinsu ita da Ruky zai fara akan Nabeeha yayi, sannan huɗubar su Mamy (Aunty Ummi) harma da su Uncle Ma'aruff na nan daram a cikin zuciyarta. Tabbas tana matuƙar jin kunya da shakkar Dadah saboda matsayinsa da kwarjinin sa. Amma tana da makami guda ɗaya a hannunta game da zama da shi da kuma yaƙar Nabeeha kamar yanda Mom (Aunty Mimi) ta faɗa.    
       Murmushi tai daya tsaya mata iya lips, sakamakon tinano kalaman Mom ɗin. Dan haka ta watsar da takaicin da Nabeeha ke shirin cusa mata da makirci irin na tsohuwar mace cike da shagwaɓa ta miƙama Dadan kofin tea ɗin da faɗin, “Dadahhh! Kasan fa idan bamu da lafiya muka ƙi cin abinci ɗura Mammah ke mana”. Tai maganar tana wani kalar waro masa idanu...
     Wannan furuci shi ya katse tunanin Nabeeha itama, sannan ya saka Dadah kallonta har murmushi na son kufce masa ya dai danne. Ganin yaƙi magana yasa Nabeeha fara jin daɗi, a zuciyarta kam faɗi take (Shegiyar yarinya ji bariki.....) amsar Dadah ga zancen Nimrah ya sake katseta daga zagin da take ma Nimrah a zuciya da dariya....
         “Naga takaina kenan. Da alama nima ɗurar za'a min yau Kiddo”.
     Kai Nimrah ta jinjina masa da duƙarwa tana murmurshi, dan a yanda yay maganar da sanyi furuci da kuma dai-dai irin yanayinta ya saka ta jin kunya mai tsanani. Sosai tsigar jikinsa ta yamutsa da salon kunyar tata da murmurshin da tayi, har takai shima ƙaramin murmushin ya suɓuce masa. Dai-dai nan kuma suka haɗa ido da Nabeeha dake masa wani irin kallo. Da yake Dadah ɗan duniya ne na gaske, sannan gogarma sai ya wani fuske abinsa, yanda ma ya tsareta da idanun nasa sai itace ta janye nata dan ta gagara juriyar kallonsa.
        Sosai zuciyarta ke mata zafi da raɗaɗi, ta dai daure domin cimma burikan ta da tsare-tsaren ta, sai dai a kaikaice take watsa ma Nimrah kallo mai zafin gaske da bayyana matsanancin kishinta har tana cije lips. Sarai Dadah yana lure da kallon da take ma Nimrah ɗin, amma sai ya basar anan ɗin ma tare da sakin wani ƙayataccen murmushi yana jan idanunsa daga kanta slowly ya maida kan Nimrah da har yanzu kanta ke a rissine, sai dai itama ya fahimci ranta a jagule yake. Hannunta dake riƙe da mug ɗin tea ɗin ya riƙo, hakan ya sakata ɗagowa da sauri. Kanta tsaye ta ce, “Dadah na baka zaka sha ne?”.
      Kansa kawai ya jinjina mata. A take farin ciki ya mamayeta, ta miƙa masa kofin. Amsa yay ya fara sha. Hakan yasa ɗakin yin shiru. Nabeeha da Nimrah kowa da irin tunaninsa. Shi kam dake nazartarsu ya cigaba da shan tea ɗin badan yana masa ma daɗi ba saboda bakinsa. A haka su Ma'aruff suka zo duba shi suma suka same su.....

          ############
Chapter 97 · 0% Book details