Sashe 61
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A nan ƙasar gado kam sai washe gari Nabeeha ta farka. Hajiya Hasiba ce zata kwana da ita. Su Ismat suka koma gida tun a daren. A lokacin kusan sha ɗaya, Ismat da hankalinta ya kawo tai tunanin ya kamata fa ace su sanar da su Mammah. To amma sun dawo late, bata jin basu kwanta ba yanzu duk da gidan da baƙi.
“Bari na duba ko su Mammah basuyi barci ba a sanar musu ko”.
Ta faɗa tana nufar sashen batare da jiran ra'ayin su Rayhana da suka tsaya cak suna binta da kallon mamaki ba.
“Hummm kinji wani sabon munafunci kuma. Wai mike damun Ismat ni kam? In ce yanzu a gabanta Momy ke faɗa...”
“Hummm”.
Amimah da abin yafi ƙulewa ta faɗa tana barin wajen. Dan tabbas ita kam har a zuciya da ruhi bata son su Mammah. Tana kuma taya ƴar uwarta jin haushin abinda shirmensu ke ganin ana mata. Wato ba'a sonta. Har Rayhana zata bi bayan Amima ta fasa. Itama sashen Mammah ɗin ta nufa. Dan gwara taje taga mi za'ayi. Cikin rashin sa'a tana shiga falon suka kusa cin karo da Ismat dake ƙoƙarin fitowa bayan ta bama Kulu dake kimtsa falon saƙon sanar ma Mammah da safe koda basu shigo da wuri ba.
Cikin rashin fahimta abinda ya kawo Rayhana ɗin Ismat ta ce, “Muje kawai sunyi barci ma. Amma Kulu zata sanar musu da safe”. Ganin har zata fita yasa Rayhana bin nata kawai...
....★Washe gari da safe Mammah ta tashi da hidimar wucewar baƙi da ana idar da sallar asuba su Ma'aruff suka kawo motoci dogaye da tun jiya sukai booking ɗin su zasu kwashe su. Wannan haya-haya ta mantar da Kulu saƙon Ismat. Sai da kusan tara gidan ya koma shiru kowa ya fice sai su kaɗai da Gwaggo Khadijah data rage, sannan ne Kulu suna faman aikin gyara da har su Shariffa suka shigo anayi da su Kulu ta tuna.
Cikin dafe baki da sallalami ta zaburo. Lailah ta tambayeta lafiya? Dan yanda tai ɗin harta nema firgita Baby Khadijah ma dake goye bayanta. “Wlhy Aunty nayi mantuwa ne. Jiya ƙanwar Hajiya tazo kusan sha ɗaya da rabi take sanar min wai sun kai Hajiyan asibiti da magriba a jiya, saboda halin da take ciki basu shigo sun faɗa ba, sai a lokacin da suka dawo daga asibitin dan ita an bata gado”.
Sun fahimci Nabeeha take nufi. Babu wani nuna raini ko wulaƙanci suka shiga Jajantawa. Itama Kulu sai ta nufi bedroom ɗin Mammah domin sanar mata. A kuma lokacin ne ma su Ja'afar ke shigowa cikin shirin fita kasuwa. Su Shariffa suka sanar musu. Bakuna suka ɗan taɓe da faɗin, “ALLAH ya bata lafiya” cikin haɗa baki kawai.
Su Lailah suka amsa da amin. Sai kuma cikin ƙarfin hali Shariffa tace, “To ko mu biku a dubata ne?”.
“Wa ɗin?”.
Cewar Ma'aruff yana haɗe fuska.
Shariffa ma sai ta kasa magana. Ya ce, “Tambayar ki nake?”.
“Humm Auntyn mana? Nake ga ya dace hakan ai”.
“To ga hanya”.
Ya faɗa cike da gatse yana wucewa bedroom ɗin Mammah. Da kallo ta bishi, shima Ja'afar sai ya take masa baya. Lailah ta ce, “Humm ke miya kaiki Besty?. Kin fa san hali sarai.”
“Amma Besty ciwo ai ya girmi komai. Sannan koba komai sai ayi mata dan ALLAH kuma dan Dadah. Musamman da suka san yau baya gidan nan. Wai miye rayuwa da zasu dinga biye mata ne. Musamman ma su da suke maza.”
“Matar ce sai a hankali wlhy. Sai dai kawai ai mata dan ALLAH ɗin dan kunyar Dadah kuma. Ki barsu nasan Mammah bazata ƙi zuwa ba, sai mu bita kawai”.
“Shike nan, haka ma yayi”.
Koda Kulu ta sanarma Mammah sai hankalinta ya tashi baiwar ALLAH. Tana cikin jimantawa da jerama Nabeeba ɗin addu'a su Ma'aruff suka shigo rai ɓace. Mammah da bata san sun sani ba ta sanar musu kamar yanda Kulu ta sanar mata.
“Humm Mammah badai zuwa zakiyi ba?”.
“Kamar ya ba zuwa zanyi ba. Halan baku ji da ƙyau bane sunan wadda aka kira?”.
Fuska a kumbure Ma'aruff ya ce, “Mun ji. Kawai munga babu dalili”.
“Oh ni A'isha ALLAH ka shirya min waɗan nan yara masu girman kwabo. Ɗiyar ɗan uwana kuke faɗin ba haɗi. Jinin fa Yaya Nasiru ce ko kun manta ne?”.
“Amma Mammah ita abubuwa nawa suka faru a gidan wanne ta nuna tasan dake a nan gidan kodan miji da kika haifa mata. Kuma tana kwana tana tashi, sannan tana tuna kuna da wata alaƙa ma da Mahaifinta. ALLAH wannan abin da ake mata yake sakawa take ganin ma tsoron ta ake ji. Ai ba ita kaɗai bace jinin Uncle Nasiru ɗin sauran muna son su kamar yanda suke son mu...”
“Wai wai ina baku kuna ƙin ƙarɓa ƴaƴan nan. Shin ita rayuwar nan nawa ma take. Idan ita batayi ba sai mu haɗu duk mu koma kamarta kenan?. Ma'aruff, Ja'afar ku dinga haƙuri da rayuwa, tare da iya sarrafa halayen mutane a yanda suka zo muku. A duk lokacin da bawa yay shirin shimfiɗa maka baƙar tabarma kai shimfiɗa masa fara tas, sai ta haska shi, kaima ta haska ka har a wajen UBANGIJI ka tsira ka zauna lafiya. Ni fa kun ganni nan bana fatan abinda zanje gaban UBANGIJINA ana min dogon hisabi saboda mu'amulata da mutane wajen cire hakkina a gare su, ko cire nasu hakkin a gare ni. Ku barta da halinta, ku kuyi abinda ya dace. Ɗan uwanku fa ke aurenta, idan da kara ubanta amini ne ga ubanku. Ni kuma tamkar ɗan uwa yake gareni na jini......”
“Mammah mu dai wannan lissafin naki kawai a barshi. Yanzu ya kike so ayi?”.
Mammah tasan ba fahimta zasuyi ba. Ta rasa miyasa suka zafafa akan Nabeeha. Eh tasan itama a yanzu yarinyar da al'amarinta sun gama fice mata a rai gaba ɗaya. Dan tayi iya ƙoƙarin ta na janta jiki ko zata canja wasu abubuwa taƙi. Amma hakan da tai ba yana nufin kuma bazata sauke wasu haƙƙoki da suka dace na rayuwar yau da kullum ba da zaman guri ɗaya da suke yi. Ajiyar zuciya ta sauke. Babu wasa a tare da ita ta ce, “Yanzu zan shirya da ku da su Lailah muje a ganta. Suma su Bilal idan sun fito ko zuwa anjima da dare su ɗauki matansu suje. Yanzu ma bazance sujeba dan rana ce za'aita magana. Su mutane basu san uzuri ba”.
Basa ƙaunar zuwan, amma babu wanda zai iya musu da Mammah. Dan haka sukai gumm da bakunan su. Kawai.....
💖💖💖💖
A hankali take buɗe idonta da sukai nauyi irin na mai barci. Ga kumburin kukan data sha suma sun bada gudunmawar saka idon nata zama cikin nauyin. Shiru tsawon mintuna tana kallon rufin gadon. Fara dawowar abubuwan da suka faru a daren jiya tsakaninta da Dadah ya sata saurin sake runtse idanunta tana mai ture tunanin, sam ko tunawar ma bata son yi dan kunya komai ke bata. Dadah fa ba wani ba. Haba wannan lamarin ai bama abin a tuna bane sam.
Idon a rufe ta juya kwanciyarta zuwa kan hannunta na dama. Dan a rigin-gine take da. Numfashi ne mai ɗumi ya buso mata. Babu shiri ta buɗe idanun da sauri. Zuciyarta ta motsa ganin Dadah a kusa da ita. Duk da idanunsa a rufe suke alamar barci yake. Taso miƙewa amma hakan ya gagara, bama tasan ta shagala a kallon kyakkyawar fuskarsa ba. Ma'abociyar iko da cikar kamala. Sosai ta shagala, ta yanda har takai hannunta ta ɗan shafa gemunsa da bai cika tsaho ba. Sosai laushin gashin yay mata daɗi, ga ƙamshi mai sanyi yana yi, tako cigaba da wasa da shi har takai yatsarta ya sauka akan tausasan lips ɗinsa da a yanzu suka tattare kaɗan da yanayin bushewa, sun kuma ƙara zama pink sosai. Fin mintina uku tana ta masa jagule-jagule a fuska kafin ta janye da nufin miƙewa.
Caraf ya riƙe hannun nata a bazata. Sosai ta razana. Ta kallesa da sauri, cikin nasa idanun dake buɗe suka shige. Ba shiri ta wulƙita zata juya kwanciyarta ya saki hannunta ya maida shi a bayanta. Maidota yay a yanda taken, sai kawai ta fahimci bata da zaɓin daya wuce shigewa cikin jikinsa dan bazata iya haɗa ido da shi ba da kunya, ashe idonsa biyu yay likimo tanata taɓa masa fuska..........✍️
77