← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 113

Sashe 41

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

.........Rayhana na cikin ƙyalƙyala dariyar mugunta sai ganin Nabeeha tayi ta dawo. Cikin sauri ta shanye dariyar tana kallon ta. Sai kuma cikin dauriya ta ce, “Naga kin dawo Aunty?”.
Murmurshi Nabeeha tayi, tare da miƙama Rayhana key ɗin. Ƙasa amsa tayi, sai ma kallonta da take ita da key ɗin. Hakan ya saka Nabeeha ɗora mata key ɗin a hannu tana faɗin, “Rayhana babu amfani rufe Haysam, dan idan nayi yau gobe ma nayi zan iya jurar cigaba da yi ne har ƙarshen rayuwarmu?.”
“Amma Aunty....”
“Rayhana!”.
Nabeeha ta katseta ta hanyar ɗaga mata hannu. Sai kuma ta dafata tana mai ƙoƙarin shanye hawayen dake ƙoƙarin ciko mata ido. “Rayhana mutane da yawa sun bani shawara daban-daban a wannan daren, na gwada wasu a ciki amma banga wadda keda hanyar ɓillewa da ni ba, sai guda ɗaya tak. Kin san daga bakin wa ta fito?”.
Kai Rayhana ta girgiza mata. Nabeeha tai murmurshi tana barin wajen. Sai dai taku ɗaya biyu ta tsaya cak, hannayenta ta harɗe a ƙirji, batare da ta juyo ba ta cigaba da faɗin, “Haysam, Rayhana. Kuma tabbas ya kamata ace na gwada tashi shawarar shima kamar yanda na gwada na sauran, dan tasha banban da taku gaba ɗaya. Dan haka kije kawai, kije ki min addu'a, nagode da ƙoƙarin ku, ku barni nima na gwada nawa a wannan gaɓaar tamkar yanda Momy ta faɗa, lokaci yayi da nima zan yi yaƙin kaina”.
Tana kaiwa nan ta wuce bathroom tabar Rayhana datai sumar tsaye anan zuciyarta na hanƙoro a ƙirji.......

★==========★

Da kallo Nimrah tabi bayan Dadah dake ficewa, wasu irin hawaye masu zafi suka ciko mata idanun. Tabbas gaskiya kowa ke gaya mata, Dadah yana mata kallon ƴar yarinya ne sa'ar su Aheel har yanzu. Babu kuma wasu alamu dake nuna zai canja hakan anan kusa. Dubeta a yau ita amarya ce a ranar da kowace mace ke jin alfahari, take samun kulawa da tattali na musamman a wajen mijinta. Ko miji baya sonka a randa aka kaika gidansa yakan maka abubuwa ne tamkar sarauniya kodan amfanuwa da baiwar, amma ita Dada sai yay mata tarba irin ta uba da ƴa. Murmurshi mai ciwo ya suɓuce mata tare da hawaye a lokaci guda. Hannu takai ta share su, sai kuma ta ɗan taɓe baki da faɗin,
“Zaka canja Dadah. Dole ne ma ka canja a yanda nake fata da buƙatar mijin aure na. Ina son soyayya, ina son kuma a nuna min soyayya. Tunda har ka kasance a cikin ƙaddarata koda ace ina tuhumarka da wani laifi dole ne ka bani wannan soyayyar nima naji yanda ake ji. Dan wlhy bazan yarda na zama cikin ƴan rakkiyar mata ba. Sannan matarka bazata yankeni nasha zafi a banza batare da na amshi sakamako itama ta amshi na ba. Ni da kai da ita dolene mu zuba”.
Tana kaiwa ƙarshe ta kaɗa kanta zuwa bathroom. Wanka tai da alwala ta fito. Ta gabatar da shafa'i da wutri ta haye gadonta ta kwanta kewar Ruky na dawo mata. Sai kuma ta hau murmurshi da tunanin ko yanzu yaya Buddyn tata ke ciki da Uncle Ammar? Da wannan tunanin barci mai nauyi ya kwasheta kasancewar akwai gajiya sosai a jikinta, sannan duk yanda abu yakai ga damun zuciyar Nimrah bata cika zafafa shi da tsananin da har zaka iya karantar shi a zahirinta ba...
Chapter 41 · 0% Book details