← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 113

Sashe 14

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

)))))))★((((((((
Received at 4:41 PM        Tsakanin isowar motocin Dada dana Daddy Imran babu nisa. Sai dai da yake a faɗar shugaban ƙasar ma kowa da fanninsa sai basu haɗu ba. Kai tsaye motocin ɗaukar Dada sun nufi sashen ofishin shugaban ƙasa ne. Wani babban jami’i Chief of Protocol ya tarbe shi. Dan motocin na kammala tsayawa jam'in nan yay wuff ya fita a gaban mota kamar sauran suma yazo ya buɗe sashen da Dadan yake. Sai da yaja fin mintuna biyu, dan sai da ya karanta addu'oi sosai tare da ƙarema wajen kallo sannan ya sauke ƙafarsa ta dama dake sanye cikin haɗaɗɗen takalminsa. A take ƙamshin turarensa ya isa hancinansu, duk da suma ƙamshin nasu turarrukan sun shiga nashi hancin.
        Cike da girmamawa Chief of Protocol ya miƙa gaisuwa. Tare da faɗin, “Ranka ya daɗe Sir. Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin a raka ka kai tsaye ofishin ka.”
         Kai kawai ya jinjina masa kamar na baya, dan tun maganarsa da Mammah a gida bai sake magana da kowa ba. Wannan kuma salon takun manya ne. Jami'an da suka ɗakkosa har yanzu basu ji muryarsa ba, dan haka suka fara tunanin wai kodai bebe ne mutumin nan?. Babu mai basu amsa dan haka sukai gum, saboda kwarjininsa kawai da cikar kamala da kamewarsa ga nutsuwa da gizago ya sakasu jin shakkarsa, tare da yarda da batutuwan mutane a kansa. Dan a weekend ɗin nan babu sunan daya kai sunan sa dana Imran yawo sai na shugaban ƙasa.
       Yanda Chief of Protocol ke gaba, sai jam'in nan dake nuna shine shugaban wannan tawagar a tare da shi, Dada na bayansu, bayansa kuma sauran jami'an nan ne ke take masa baya dole abin ya birgeka. Dan kamar an tsara su ne, suna sauke ƙafa da ajiyeta a tare kaida ka gani kasan rakkiyar ta babban kai ce. Gashi suna tafiya ne ta cikin dogon corridor mai sanyi, shirun da babu hayaniya. Tun fitowarsa motar ƴan median fadar ta shugaban ƙasa suka dasa musu camara kuma. Dan dole ne a saki labaran shigowar Chief Of Staff na farko office ga ƴan ƙasa.
         Ko'a jikin gogan naku. Takunsa yake cike da ƙasaita da mazantaka. Fuskar nan ciɗin-ciɗin yau ta asalin sojan sa a fagen yaƙi. Ga hotunan tsoffin shugabanni da suka cika bangon dogon corridor ɗin suna kallonsa kamar suna tantance shi da masa barhaban. A ƙarshe aka tsaya a gaban wata ƙofa dake ɗauke da baƙin allon rubutu da kalar gold.
     CHIEF OF STAFF TO THE PRESIDENT.
     Shine a rubuce ɓaro-ɓaro ga mai kallo. Chief of Protocol ya danna wani maɓalli dake a bango a take ƙofar ta raba kanta biyu. Makeken Ofishin mai girman gaske ya bayyana a idanunsu. A tsaftace yake, ga ƙamshi na tashi mai ainahin saka nutsuwa. Matuƙar tsaruwa wannan office ya tsaru. Dan kuwa komai na cikinsa yana tabbatar da ƙarfin ikon mamallakinsa .
      Dada ya tsaya na ɗan lokaci yana karanta addu'oi. Kafin ya saka ƙafarsa ta dama batare da ya daina ambaton ALLAH ba. Dan shine cikakken sarki gagara misalin masu misali. Mai cikakken iko da rahama ga jinƙai ga bayinsa. Shike bada dama ga wanda yaso a sanda yaso. Shike daka girma da cikar kamalar bawa a idanun ƴan uwansa bayi badan ya kasance mafifici a garesu ba. Ba'a farautar ɗaukaka ko girma da kuɗi ko ƙarfin ƙwanji. UBANGIJI ne kawai ke badawa kamar yanda ya bama wannan bawan nasa Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi.
        A hankali ya kai zaune cikin kujerar da aka gyara masa idanunsa a lumshe bakinsa na cigaba da ambaton UBANGIJI da neman agajinsa. Dan tabbas yanzu ne wasan zai fara. Farawa irin ta KARE JINI. BIRI JINI. A yanzu yaƙine na kwatar ƴanci da neman tsira. Kuma duk zasu fara ne ta silar wannan kujera....

      ★A can ma Daddy Imran ya shiga nasa babban ofishin dake da ƙarfin faɗa aji akan tsaron ƙasa. Shima dai an shirya shi da girma da aji tamkar na Dadan. Dan tsarin da akaima offices ɗin duk mai hankali ya tabbatar da gayya shugaban ƙasa yasa akayi su. Ga tsaro mai tsaurin gaske dake tabbatar ma maƙiya koda zasu iya keta wannan alfarmar sai da ƙarfin ikon ALLAH. Sannan The two shadows sun iso FILIN YAƘIN. Yanzu ne za'a banbance MAZAJE DA MAZARE......

=============
Received at 4:41 PM33

........Harara Amima ta wulla mata, cike da wulaƙanci ta furta, “Ke wai wace irin jakar yarinya ce? Kashemu kike son yi, kin saka abu a wuta kinzo kin shige ɗaki uwar uban mi kike yi?”.
       “Aunty kiyi haƙuri dan ALLAH. Wlhy bayi na shiga ne”.
      Mangari Amima ta kai mata, duk da kuwa ba girmarta tai ba. “Bayani zaki tsaya min ko zuwa ki duba dan ubanki”.
    Da gudu Nana ta wuce kitchen ɗin, Amima taja tsaki tana nufar ɗakin Nabeeha. Mamakin ganin Momy tunda safe ya kamata. Ta dai ƙarasa shiga tana gaisheta da kallon Nabeeha dake kuka ga idannunta sunyi luhu-luhu alamar bata samu isasshen barci ba. Zama tai cikin tashin hankali tana dafa ta, dan tabbas Amima nada rashin kunya da rashin mutunci, amma tana da son ƴan uwanta. Musamman ma Nabeeha tana sonta sosai fiye ma da Rayhana da suke uwa ɗaya uba ɗaya.
        “Aunty yanzu saka abin nan kikai a ranki har haka?. Kalla idanunki fa. Dan ALLAH ki kwantar da hankalinki, na tabbatar Dada zai dawo gareki. Kuma idan ya tabbatar miye a zuciyar Adeel zai hukunta shi. Momy dan ALLAH kiyi wani abu. Bana son ganin Aunty Nabeeha a wannan halin. Shiyyasa tun farko ban so kuka amsawa mutumin nan ba, dan Adeel ba irin mazan ƙasarmu bane da suke gane yaren aure.”
         “Ni kaina nayi nadama Auta, dan kuwa a wannan gaɓar Adeel ya zame min gaba kura baya sayaƙi. Na rasa ta inda zan taro al'amarinsa.”
      “Momy kima First Lady magana mana, tunda ta silarta kika sanshi na tabbatar idan tai masa magana zai fahimta. Wlhy koni ina tsoron Dada yasan gaskiyar zancen nan. Dan ba lallai ya yarda Aunty bata bama Adeel dama ba a kanta. Kuma bamu san makircin da Adeel ɗin ke shiryawa ba tunda har gashi yazo gidan”.
      Shiru Hajiya Hasiba tai cike da nazarin kalaman Amima.....

      ★★★

A ɓangaren First Lady tana yanke waya tsakaninta da Nana babbar aminiyarta data ɗakkota a mota daga gidan Hajiya Hasiba tai ƴar dariya da faɗin, “Anya a kaf cikin yaranki akwai mai sonki kamar Nana? Gata da kishin tsiya. Yarinyar nan ko uwarta kikace ta sallama miki zatayi fa”.
        Baki Firt Lady ta ɗan taɓe. Sai dai fuskata da murmushi ta ce, “Na sani. Dan ki duba randa na fara ganin videon ta a TikTok nasa Ilu ya kawo min ita, yana mata magana ko musu batai ba. A washe gari ya saya mata ticket tazo. Da ƙyar na samu ta koma gida bayan ta min sati, haka kuma ta cigaba da damuna da massages har sai da na sa ta ƙara zuwa daga nan ta maƙale taƙi ta koma. Ita kanta Hasiba yanzu haushinta take ji”.
       Cikin ƙyalƙyalawa da dariya Hajiya Caras ta ce, “Mutuniyar kina basu wuta. Amma nikam miyasa bazaki ƙyale Hajiya Hasiba da ƴarta su huta bane?”.
       “Hummm.... kema kin san bana wasa da ɗaukar fansa. Duk wanda yay min kan kara zan masa na itace. Ai tunda Hasiba ta nuna min ƴarta tafi ƙarfina zama ta iya rabuwa dani a kanta, wlhy sai ta tabbatar tayi dani ƴar halak. Kima shirya a satin nan zamu je wajen mai tukunyar tsafi, dan na fahimci ƙullin dake kan Adeel ya fara hucewa game da Nabeehar. Sannan ina son yamin aiki akan Nabeeha, dan anzo gaɓar da da kanta zata kawo min kanta. Kuma a gaban Hasiba zan yi yanda nake so da ita, dan wannan alwashina ne, sai na kasance da yarinyar nan. Sannan saina kunnama Hasiba wuta tsakaninta da Adeel da bazata iya kasheta cikin sauƙi ba”.
        “Bazan hanaki ba aminiya. Sai dai kiyi a sannu dan kin san wanene mijin yarinyar nan. Ya fimu hauka wlhy tsaf zai ƙarar damu”.
      “Bani da matsalar komai da shi sai ta son matarsa. Amma idan yace zai shiga gonata dai-dai nake da shi. Dan a tafin hannuna yake shima, da yawan masu neman kurwarsa ƴan hannun damata ne. Ko last abinda ya faru nina basu rahoto akansa. Duk da yarinyar da sukai amfani da ita naso ta mutu dan ɗaukar fansar Zahir da suka nema illata min tasha da ƙyar, kuma ban haƙura ba, inada wani sabon shiri, suma yaran sai na girgiza duniyarsu.”
Received at 5:36 PM
reacted with 🔥         “Lallai Hasiba na cikin one chance kenan. Dan naji ranar kina faɗin da taimakon ta aka fita da yarinyar ma a gidan”.
       “Tabbas haka ne. Dan ni suka bama aikin na sakata. Na gaba ma idan ya taso itace zatayi”.
     Dariya sosai Aminiyar tata ta sanya, tare da faɗin, “Aminiya wanda bai sanki ba ya shiga ukun sa, musamman ace ya shiga komarki a gaɓar da yake kallon bashi da masoyiya kamar ki, shiyyasa Hasiba ke ban tausayi. Dan a yanzu duniya ji take bata da kamarki, bata sane kece makashiyarta ba”.
       A tare suka tuntsure da dariya harda tafawa. First Lady ta ce, “Itama ita tajama kanta. Data bani muradin raina tun farko da tasha daɗi. Dan na ɗauketa da muhimmanci amma ta watsan ƙasa a ido ita a dole mai ƴa, mu ko bamu san zafin haihuwa ba ai ko”.
         “Ai gashi nan ta jama kanta.” Hajiya Caras ta faɗa tana saving recording ɗin hirar tasu da duk tayi batare da First Lady ta farga ba. Dan sun riga sun iso katafaren gidan su da suka dawo bayan sun sauka a mulki.....

     🥱🥱Hhhhmm nama rasa abin faɗa. Hajiya Hasiba wannan fa shi ake kira idan bakai sharar massalaci ba zakayi ta kasuwa.

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆
Chapter 14 · 0% Book details