← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 113

Sashe 30

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Sai muce Alhamdullah biki kam ya kammala. Dan washe gari aka karasa zuwa gidan Biebah aka ƙarasa komai. Dada yace duk mai zuwa yaje yaga ɗaki dan shi da Imran zasu kai Biebah ɗakinta. Wannan ba sabon abu bane. Dan tun daga kan Aunty Ummi, Mommy, Mimi shi da kansa ya kaisu ɗakunansu tare da Imran. Sai suma su Ja'afar dake yin mota ɗaya subi bayansu. Kuma anayi la'asar suke tafiya.
      Iyaye da yayye sun zagaye Biebah da aka gama shiryawa. Aka fara kaita gaban Uncle Nasiru da Uncle Jamilu, Zubairu, Tasi'u sukai mata nasiha. Sannan aka kaita ga Mammah. Addu'a kawai tai mata dan ita kam duk wani faɗa da nasiha tama yaranta shi. Suma su Gwaggo Khadijah sukai nasu. Sannan aka ƙarasa da ita gaban Dada da Imran, sai su Ja'afar dake tare da su har zuwa Ammar ƙarami.
       Sosai idanun Dada sun juye. Duk lokacin da zai kai ƙannen nan nasa gidan aure kobai fito ya faɗa ba kallo ɗaya zaka fahimci damuwa a tare da shi. Yanzu ma koda Biebah ke durƙushe a gabansu ya zuba mata idanu ne kawai. Sai kuma ya kai hannu ya kamo nata. Hakan yasa ta matso jikinsa sosai ta ɗora kanta a ƙafarsa. Kanta ya shafa a hankali yana murmushin ƙarfin hali. “ALLAH yay miki albarka. Yanda kikai mana biyayya kema UBANGIJI ya baki yara masu albarka da zasuyi miki. ALLAH ya zaunar dake gidanki lafiya kamar sauran ƴan uwanki. Habibah na yarda da mijin da kika zaɓa da kanki ɗari bisa ɗari kamar yanda na yarda dana ƴan uwanki a baya. Kema na yarda da tarbiyyar da muka baki, kije kiyi haƙuri. Shi aure ibada ce. Rayuwa ce ta rabi farin ciki rabi jarabawa. Babu wani bawa da zai iyama ɗan uwansa bawa yanda yake so ɗari bisa ɗari na yau da goben rayuwa. UBANGIJI ne kawai mai wannan ni'imomin a gare mu. Dan haka idan kinga kuskure daga Haydar ki yarda shi ɗin mutum ne kamar ke. Dole yay dai-dai kuma dole yayi kuskure. Ku zauna ku gyara a ɗakin ku basai kin kawo mana ba. Ga ƴan uwanki nan su duka ukun tunda na kaisu gidajen aurensu ban taɓa zama shari'a tsakaninsu da mazajensu ba ko sau ɗaya. Kuma ni shaida ne kin fisu haƙuri. Badan mun gaji dake ba zamu kaiki wani gida, idan so samu ne naita ganinku a kusa dani ina jin daɗi da farin ciki, amma hakan bazai yiwu ba, wannan shine gatan da zamuyi muku muma muyima kammu.
Received at 14:59Kar ai sakaci da ibada, yanzu ne ma lokacin da za'a ƙara dagewa kinji”.
    Kanta ta jinjina masa tana sake fashewa da kuka. Ya kauda kansa gefe yana dauke guntun hawayen da suka taru masa ta gefen ido. Daga nan shima Imran ya sake mata tashi nasihar. Kafin su Ma'aruff, Ja'afar, Bilal, Ammar. Daga haka akai addu'a sannan Dada ya miƙe riƙe da hannunta. ALLAH sarki Small Mom, da gudu su Nimrah da Mu'azz sukazo suka rungumeta, dama suna ɗaki sun haɗe kai sunata kuka. Bintu taje ta kirasu yanzu. Idanu kawai Dada ya zuba musu yama kasa magana. Sai Daddy Imran ne ke lallashinsu. Dan su Ja'afar ma sharar ƙwalla suke. Wato kowane ɗan uwa fa a irin wannan ranar yakan ji wannan damuwar ta rabuwa da ƴar uwarsa. Musamman wannan zuri'ar da suka shaƙu suke matuƙar son junansu. Ƙarshe dai da ƙyar Mammah tazo ta janye su Ruƙayya tai ɗakinta da su. Su kuma suka fice Biebah na jikin Dada...

        //★//★//★//★//

  Ashe wasa farin girki. Sai da suka kai Biebah gidanta daya gama haɗuwa Dada ya kama hannun Faro ya saka na Biebah a ciki. Ya jaddada masa amana ya bashi, idan kuma yaci wlhy bazai taɓa yafe masa ba. Ya tabbatar masa a cikin kaf ƙannensa Biebah itace zuciyarsa. Kar ya bari ya taro faɗan da bazai iya karewa ba.
      Faro yay murmurshi da tabbatar masa zai kamanta in sha ALLAHU. Dan shima Biebah ƙanwace a garesa ai. Shima Imran ya sake jaddada tashi amanar. Su dai su Ja'afar sun barma zuciya saboda matsayin Haydar yaya. Amma yasan kosu kaɗai sun ishe shi gayya idan ya taɓa Biebalo. Zasu tafi fa Biebah ta riƙe Dada tanata kuka. Da ƙyar ya ɓanɓareta a jikinsa. Sai suma su Ma'aruff suka rungumeta suna hawaye. Dan Bilal ma kasa tsayawa yayi, kowa yasan yanda Bilal ya shaƙu da Biebah a rayuwa. Kusan shine yay rainonta, shiyyasa komai nata a gidan nan Yaya Bilal ne gaba.
     Sosai jikin Haydar ya ƙara sanyi, dan soyayyar waɗan nan ƴan uwa bata wasa bace....

     _____

Daga gidan Faro gidan Daddy Imran suka wuce. Zasu ɗakko Asma'u. Sun tadda itama iyaye da yayye zagaye da ita abata nasiha da faɗa. Bayan sun gama aka kawota nan falon Imran gaban Dada matsayin uba. Yanda yay ma Biebah nasiha haka yay ma Asma'u, shima Imran ya ƙara dan daga shi har Ammie sunyi kafin biki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Itama dai ta rungume Daddy Imran da ƙyar aka rabasu. Haka Dada ya ɗakkota a mota da su Ja'afar dan Bilal da Ammar sun wuce gida daga gidan Biebah. Lokacin da suka iso ana magriba. Dada na damƙata a hannun Mammah ya wuce massalaci.
          Anan ɗakin Mammah tai sallar magrib da isha'i, a lokacin kuma suma Ruƙayya da Nimrah an kammala shiryasu tsaff. Ga turaruka sun sha na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ana idar da sallar magriba Mammah tama su Gwaggo Alawiyya maganar su rakasu basai sun kawosu wajenta ba. Dan ta tabbatar baza'a rabu lafiya ba. Haka kuwa kayi. Wasu suka raka Asma'u sashenta. Wasu Ruƙayya, wasu Nimrah..........✍️
Received47

.........“Kana nufin lokacin da zaka bayyana kanka ga Zak-Shadow yayi kenan?”.
     “Tabbas yayi, kuma ya kamata ace nayi hakan saboda wannan shine dai-dai lokacin daya dace. Abinda ya sakani jinkirtawa ya riga yaje hannunsa. Matarsa ita ce babban MAKAMIN da mutanen nan suke riƙe da shi a kasa ta kowanne ɓangare....”
     “Hummm kana ganin dan ta koma hannunsa zai iya tsira? Ka sani na sani mutanen nan nada ƙarfi matuƙa. Dan sun binne mutanen kirki da yawa irin Zak-Shadow a ƙasar nan dama wanda suka fishi gwagwarmaya. Shi kansa UBANGIJI ne bai kawo ƙarshensa ba a hannunsu shiyyasa suka kasa kaisa ƙasa badan yafi ƙarfinsu ba”.
          “Nasan da haka sosai Sir, kamar yanda kace UBANGIJI kuma ai magana ta ƙare. Abinda nake so ka fahimta bana fatan su sami nasarar kai masa hari ta hannun AMANARSA. Dan ita ɗin amanarsa ce......”
       “ƘALUBALENSA kuma a yanzu ba”..
      Mutumin ya faɗa cikin katseshi da takaici da damuwa”.
     “Bazan yi musu da kai akan ita ɗin ƘALUBALENSA bace Sir, dan inada tabbacin a yanzu babu wani tarko mai haɗari a cikin rayuwar Boss sama da ita. Shiyyasa nima na shirya dawowa cikin duniyarsa, kuma nayi alƙawarin bada rayuwata wajen tayashi wannan yaƙin.”
            “Mu ma muna tare da kai a cikin yaƙin, dan Haysam ya cancanci fiye da hakan a garemu. Yanzu miye mataki na gaba?”.
      “Zan cire fuskar bogi, sannan zan fito na daina laɓewa a baya.”
    “Sai nake ganin kamar ka ƙara jinkirtawa da bayyana masa fuskarka, ka dai cigaba da bashi bayanan sirri kamar yanda ka fara. Dan in mutanen nan suka gane kana raye da wahala rayuwarmu tayi tsaho”.
       Murmushi yayi mai ma'anoni da yawa. Kafin ya jinjina kansa da faɗin, “Haka ne Sir. Amma karka manta ai mun jima da mutuwa a duniyar mutane. Har mi kake tsoro a wannan gaɓar? Kai ɗin fa SOJA ne, sojan ma rainon ZAK-SHADOW”.
      Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. Ya ce, “Haka ne na fahimta. Yanzu sai muje next kenan? Amma kafin hakan ya kamata mu nema shawarar Baba”.
     “Wannan shine dai-dai. Amma kafin hakan zan fara aika masa waɗan nan bayanan. Sai ka turama Baban saƙo ALLAH yasa ya bamu damar ganinsa da wuri..”
     Jinjina masa kai yayi. Daga haka suka sallama ya baro wajen. Dama a wani ɓoyayyen waje suka haɗu, yana cikin shiga ne ya ɓoye ainahin kai shiyyasa baka isa gane waye shi ɗin ba kai tsaye.....

••••••••••••
       •••••••••••••
Chapter 30 · 0% Book details