Sashe 74
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
........Anan ɓangaren Hajiya Hasiba cike take fam da ɓacin ran abinda Rayhana tazo mata da shi game da rikicin su da Nabeeha. Zuciyarta ta gama kaiwa wuya da lamarin Nabeeha. Rai ɓace ta tsallake Rayhana ta fita a gidan. Kai tsaye gidan First Lady ta nufa. Kamar koda yaushe bata da shamaki da shigarsa, dan haka securitys ɗin ma na ganin itace suka wangale mata gate.
Koda ta shiga masu aiki sun tabbatar mata First Lady bata nan. Sun fita tare da Hajja Mangu. Ranta ya ƙara ɓaci, duk da tasan alaƙar dake tsakaninta da First Lady ɗin ba itace ta haɗa da Hajja Mangu ba. Hasalima ita bata irin harkasu. Sai dai haka kawai bata ƙaunar matar dan tana mata kalar munafukai.
Wayarta ta ɗauka tayi kiran First Lady ɗin. Har ta yanke bata ɗaga ba. Ta cije lips zuciyarta cike da zargi. Wani kiran ta sake danna mata. Sai da ta kusan katsewa yanzu kam ta ɗauka. Taji ɗan sanyin jin muryar First Lady ɗin raɗam, dan hakan na nufin ba wata tsiyar take aikatawa ba kenan. Dan haka ta sauke ajiyar zuciya cikin sauƙaƙa murya ta ce, “Ranki ya daɗe ina gidanki ance kin fita”.
Daga can First Lady ta ce, “Gani a hanyar dawowa ki jirani”.
“Okay sai kin iso”.
Suna yanke kiran First Lady ta sanya dariya. “Hajja Mangu kinga aikin mutumin nan ko? Ai na faɗa miki mai faɗa da cikawa ne. Kinga dai har mutuminiyar ta isa kafin ma muje”.
“Tabbas na yadda kam. Ai ko dole ma na koma yay min aiki kan ministan nan da nake baki labari nima fa”.
Dariya suka sanya tare da tafawa cikin shewa....
....★A ƙage suka iske Hajiya Hasiba na jiransu. Ko zama bata bari First Lady tayi ba tace suje ciki suyi magana. First Lady bata ƙi ba. Sai dai tama Hajja Mangu signal da ido. Itama ta mayar mata.
Suna shiga ɗaki First Lady ta ce, “Hasiba duk kin wani birkice, wai mike faruwa dake ne?”.
“Ranki ya daɗe bazaki gane ba ina cikin damuwa ne. Nazo ne muyita nikam ta ƙare. Kece kika saka Nabeeha komawa gidan ɗan iskan yaron can badan naso hakan ba. Kuma bazan iya miki jayayya ba duk da ban san dalilin ki ba. Sai dai kin isa da ita kema. Amma a wannan gaɓar wlhy na gaji da wannan auren nasu, sannan karki manta Adeel na nan fa akan bakansa na ko Nabeeha ko kuɗinsa. A yanzu haka dan yana ƙasar turai ne shiyyasa na jishi shiru. Wani staff ɗinsa kuma ya tabbatar min yana gab da dawowa Dubai. Na roƙeki muyi abinda zamu yi Nabeeha ta baro gidan can kafin Adeel ya waiwayeni”.
“Shi ke nan na yarda da zantukanki. Ki bani kwana biyu zanyi tunanin mafita mai sauƙi. Sannan ki kwantar da hankalinki”.
Ajiyar zuciya Hajiya Hasiba ta sauke mai ƙarfi. Sai kuma ta matsa kusa da First Lady, amma sai First Lady ɗin ta miƙe cike da wayancewa tana faɗin, “Bari na ɗan watsa ruwa na gaji. Ko zaki jirani wajen Hajja Mangu dan akwai maganar ma da nake son yi da ku ku biyun duka.”
Ba haka Hajiya Hasiba taso ba. Amma sai ta miƙe dan ba ƙaramin girmama First Lady take ba a rayuwarta. Hajja Mangu dake laɓe ta bar jikin ƙofar da sauri ta koma inda suka barta.
Hajiya Hasiba na fita First Lady taja tsaki da hararar ƙofar. Wayarta ta ɗauka tai kira. Bugu ɗaya aka ɗaga daga can. Takai zaune a inda ta tashi tana jera gaisuwa cike da girmamawa da turanci. Shiru ya ɗan biyo baya alamar ana amsa mata daga can.
“Idan ba damuwa ina son ganinka da gaggawa ranka ya daɗe. Idan zai yiwu a daren yau dan oga baya nan”.
Banji amsar da aka bata ba daga can, tadai shiga amsawa da, “Okay shike nan sai an jima ɗin”. Daga haka ta yanke kiran tana ajiye wayar da sauke ajiyar zuciya......
Hummmmmm!!
>>>>><<<<<<
Yanayin yammacin yay matuƙar yima Nimrah daɗi fiye da waccan fitar tasu ta farko ma. Dan yau rana ta ɗan sauka a hankali, hasken yamma ya saka garin zama luff-luff da yanayin shimfiɗar manyan giza-gizai da kamar an tsara su a saman ruwan Arabian Gulf.. Ga wata iska mai sanyi na kaɗawa, tana ɗauke da ƙamshin teku da nutsuwa mai zurfi.
Tunda motar su ta tsaya a bakin marina inda manyan jiragen ruwa ke jere kamar masu jiran umarni Nimrah ta saki baki da hanci da idanu tana kallo. Kafin ma Dadah yace wani abu ta sauka a hankali, idanunta na yawo a wajen fiye da sanda tana cikin motar, wani irin yanayi ne ya lulluɓeta dan wannan ruwan yafi na waccan ranar yawa da ƙyawun kallo ma.
Dadah ya fito daga ɗaya gefen motar shima, cikin natsuwarsa idanunsa suka sauka a kanta na ɗan lokaci, ya lumshe su ya sake buɗewa. Hakan yayi dai-dai da isowarta gabansa. Jinta kawai yay a jikinsa cike da farin ciki tana faɗin, “Wayyo Dadah kana kasheni wlhy.”
Kaɗan ya murmusa da riƙe hannunta kawai cikin nashi. Dan a yanzu yafi buƙatar ƴar nesa-nesa. Nimrah data gama fahimtarsa bata damu ba, sai ma hannun nasa data rungume tana kwantar da kanta a jiki. A ranta faɗi take (Dadah bana san shiru-shirun nan, indai kana tare dani sai ka manta kanka a miskili mara yawan magana. Dan sai na maidaka Aku na).
Shi ko da bai san mi take tattaunawa da zuciyarta ba a hankali ya furta, “Mu je.”
“Yes SARKIN YAƘIN Nimrah”.
“Baƙya ji yarinyar nan. Yaushe na zama Sarkin yaƙinki kuma?”.
Siririyar dariya ta saki, tare da sake maƙalƙalesa, sai kuma ta furta “Yanzun nan mana”.
Murmurshin yanzun ma kawai ya saki batare da yace mata komai ba. A haka suka iso gaban ruwan, dai-dai kuma lokacin jirgin Al-Noor Majesty ya tsaya a gabansu. Fari ne tas, mai ɗaukar ido, fitilu na haskawa a jikinsa duk da rana bata gama faɗuwa ba. Ma’aikatan jirgin suka yi musu maraba cikin girmamawar dake nuna ansan da zuwan nasu. Dadah na birgeta, dan yana ƙoƙarin shirya mata komai kafin ya kaita waje. Dan haka hankalinta gaba ɗaya yana kan girman wurin. Ta ɗan sake matse hannunsa da har yanzu take maƙale da shi ba tare da ta sani ba.
Kallonta yayi idanun ƙasa-ƙasa, sai dai bai ce mata komai ba. Sai ma tafiya daya fara yi dasu dan itama dai ƙarfin nata na'a jikinsa ne. Suna shiga cikin jirgin, komai na ciki ya cika da ƙamshi da tsarin daya sake rikita lissafin Nimrah. Komai an tsara shi ne tamkar ɗakin dake a gine, koma tace wani ɗan ƙaramin flat. Ga haske mai sanyi da ke ba zuciya nutsuwa. A gefe sanyin ruwa dana yammaci tamkar ba'a cikin duniya ba.
Nimrah bata ƙarasa narkewa ba sai da Dadah ya buɗe wata ƙofar gilashi suka fito ta waje gaban jirgin, yanda suke ganin ruwa muraran da babu iyaka ya sata sauke ajiyar zuciya. Zuwa yanzun kuma jirgin nasu ya fara tafiya a hankali.
“Ya rabbi”.
Nimrah ta faɗa tana yima kanta fifita da hannu biyu. Cike da zumuɗi ta ce, “Dadah dan ALLAH anan ɗin zamu kwana kuma?”.
“Ko baƙya so?”.
“Hu'um ina so mana. Dadah kawo wayarka kaga”.
“Mi zakiyi da shi?”.
Kanta ta ɗan karkata kamar yarinya ta ce, “Please Baby na”.
Idanunsa ya kawar daga kallonta, baice komai ba ya ciro wayar a aljihu ya miƙa mata.
“Thank you”.
Ta faɗa tana matsawa kusa da shi kaɗan, kawai sai gani yay ta fara musu hoto. Abinda yakan jima baiyi ba a rayuwarsa. Kai shi a wayar nan tashi ma zai iya cewa babu hoton kowa sai nata na lokacin biki da har yanzu bai san waye ya turo ba. Dan bashi da tabbacin itace da kanta.
Fitinar Nimrah ta saka dole ya tsaya akai hotunan nan kala da iri. Kafin ta koma gefe ta cigaba da yi ita kaɗai. A ransa mamaki yake yanda ko tsoron ruwan ma bata ji. Dan har ya koma ciki ita bata da alamar hutawa..
Duhun magriba ya fara, Jirgin Al Noor Majesty yana yawo a hankali a saman ruwan Arabian Gulf… hasken gari daga nesa yana walƙiya kamar taurari a ƙasa. Dadah daya sake fitowa ya tisa ƙeyar Nimrah suka koma ciki domin gabatar da sallar magriba.
Bedroom ɗin ya matuƙar ƙayatar da Nimrah shima. Komai dake cikinsa fari ne tas. Yanda ya ajiye musu abin salla har biyu ya sake bata mamaki. Amma dai batai magana ba. Ya ƙara bata wani mamakin da hijjab. Anan kam sai da tace, “Wai Dadah kodai jirgin nan naka ne?”.
Hancinta yaja kaɗan da faɗin, “Maganatu mi zanyi da wani jirgi ni. Oya muyi salla”.
Hijjab ɗin ta saka. Ya jasu jam'i kamar yanda ya saba. Koda suka idar Alkur'ani taga ya fiddo a laptop bag ɗinsa alamar zaiyi karatu. Sai kawai itama ta matsa jikinsa.
“Dadah nima zanyi karatu”.
Zamansa kawai ya gyara ya rungumota a jikinsa duk da hakan na cutar da shi. Sai dai baya son ta fahimta. Abinda kuma bai sani ba ta riga ta san wannan sirrin da yake ɓoye mata. Basu tashi ba sai da yaga lokacin isha'i yayi, itama sun gabatar. Nimrah tai addu'a sosai da roƙon ALLAH ya ƙarfafata ta iya dauriyar taimakawa Dadah. UBANGIJI ya sauƙaƙa mata koma miye da yake tausaya mata har ya yarda shi ya azabtar da kansa a kai...........✍️
To hajjaju Nimrah bari muga yaya wasan zai kaya keda SARKIN YAƘIN naki.🤣😂😂?.
90