Sashe 46
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*
Received at 15:49
reacted with ❤
KIƊA A RUWA 3
61
.........Tsaff Mimi ta shirya akwatin bada wani kaya masu yawa ba. Ta zuba uban turarrruka tamkar su kaɗai ake buƙata. Dan haɗaɗɗun ƙamshin da Maman Abdull ta shirya ma amaren babu wanda bata zuba ba. Sai kayan kwalliya. Tana rufe akwatin ta juyo ta kalla Nimrah dake share hawaye. Yi tai kamar bataga kuka take ba. Ta ce, “Tashi muje bayi”.
Mamaki ya kama Nimrah. Sai dai bazata iya tambayar Mom ɗin ba. Musamman da zuciyarta ke a kusa yanzu. Idan ma tace zatai magana zata iya sakin kuka ne. Mimi da kanta ta haɗa ruwan wanka na musamman da yaji turarrrukan Maman Abdull dama wasu kalolin, ta ajiye mata shower gel na musamman sannan ta fito tana faɗin. “Ninah kiyi wanka mai ƙyau dan ALLAH. Ko kuma na dawo da kaina ma na miki shi. Kuma kiyi sauri kinji ko”.
Nimrah ta bita da kallo, dan harta fice ta rufe mata ƙofar. Yanda akace tayi tayi, bata jima ba kuma ta fito. Mom ɗin kuma da kanta ta shiga taimaka mata wajen shiri, bayan ta bata haɗaɗɗun turarruka ta shafe lungu da saƙo na jikinta. Ta bata farin dogon wandon jeans da ƴar riga body hug mai ƙyau itama an rubuta (I'm beautiful) a gabanta. Nimrah bata wani damu ba tunda suna saka kayan a gida, sai dai idan da baƙi ne Mammah ke hana su. Ko da daddare sannan Uncle's ɗinsu na gidan.
Kayan sun mata ƙyau sosai, dan sabbi ne bata taɓa saka su ba a cikin kayan lefe suke. Ga suranta yay masifar fita tamkar babyn roba. Dan duk ustazancin ustazu ALLAH sai yaji wani abu ya ganta a haka sai dai in ba irin macen da yake buƙata bace. Ita kanta Nimrah tasan tayi ƙyau sosai. Dan Mimi na gyara mata gashinta a gaban mirror ta kasa ɗauke idonta daga kallon kanta da kanta. A hakan ma wasu sabbin ƙamshin ta sake jiƙeta da shi, ta kuma saka turare a gawayin data kunna ta mata wani turaren a haka sannan ta bata after dress mai kauri ta sake sakawa. Hakanne ya ɓoye ainahin shigarta dake ciki gaba ɗaya. Ta bata hula ta saka sannan tai rolling mayafin rigar.
“Yes. Babyna ta fito a amaryanta”.
Mimin ta faɗa tana ja mata hanci. Kunya ta kama Nimrah. Tasa hannu ta rufe fuska da faɗin, “Kai Mom wai amarya”
“Eh mana ki jimin ja'ira amarya ce mana. Kinga zauna na ja miki kunne”.
A bakin gado suka zauna. Mimi ta ce, “Nimrah ki nutsu. Inda zaki ba wajen wasa bane. Sannan ina tuna miki duk huɗubar da mukai miki karki rage komai. Idan ma da naki dabarun ki ƙara. Kuma ki tabbatar kin kirani a waya...”
“Mom ina zanje wai?”.
“Zaki gani ai tambayau. Kar kiyi wasa da ƙamshi, shagwaɓar nan a ƙarata. Ke ki koma jaririya ma kinji na gaya miki. Sauran bayani sai kin kirani. A can ƙasan kayanki akwai saƙo dana saka, idan kin kira zan miki bayani”.
Kafin Nimrah tace wani abu kira ya shigo wayar Mimi. Ganin Yaya Imran yasa ta miƙewa da faɗin, “Kinga ta shi muje”.
Idan Nimrah tace ba'a sakata a ruɗani ba tayi ƙarya. Koda suka fito babu kowa a babban falon sashen sai Nana mai aiki. Ta gaishe su tana binsu da kallo ganin akwati. A ranta gulma take. Ai ko da sauri ta nufi ɗakinta dan kiran First Lady. Su ko dama basu damu da ita ba tuni sun fice. Baƙuwar motar dake fake a ƙofar sashen wani mutum ke tsaye cikin suit baƙaƙe. Yana ganinsu ya zaburo, cikin girmamawa yake gaishe su da faɗin shine aka turo. Akwatin Nimrah ya amsa a hannun Mimi, ya saka a booth sannan ya buɗe baya. Aunty Mimi tace, “Shiga. Ki tabbatar fa kin kira ni”.
“Mom....”
Nimrah ta faɗa kamar zatai kuka. Harararta Mimi tayi da mata alamar karma tace komai. Daga haka tama mutumin umarnin suje kawai. Shi ko ya rufe mota da sauri ya koma mazauninsa na driver ya tayar. Maigadi ya wangale gate suka fice ransa fal gulma. Ƙagara yay Sanda ya fito a bayi ya gumtsa masa labari...
Komai ya ƙara cinkushe ma Nimrah. Tsoro na musamman na shigarta da mamakin ina za'a kaita. Ko fa sallama batayi da Mammah ba balle Ruky da yau gaba ɗaya aka hana musu ganin juna. Cikin kasa haƙuri ta share hawayenta ta maida hankalinta ga drivern. Tambayarsa tai ina zasu je?. Cikin girmamawa yace shima bai sani ba umarni kawai yake bi. Zuciyarta ta fara rawa yanzu kam.
Received at 15:49Kadafa abinda ya faru kwanaki ne zai ƙara faruwa da ita batare da Mom ta fahimta ba. Ai a take zufa ta fara taruwar mata a goshi. Addu'a ta fara cikin zuciyarta.
Abinka da lafiyayyen titi da mota cikin ƴan mintuna suka iso.
“Filin jirgin sama”.
Nimrah ta furta a hankali, kamar tana tambayar kanta zuciyar na bugawa da ƙarfi. Idanunta suka buɗe sosai tana kallon wajen, hasken fitilu, zirga-zirgar mutane, da tsaro mai tsauri da ya nuna mata cewa wannan ba tafiya ta yau da kullum ba ce da suka saba da su Mammah zuwa umrah. Motar ta tsaya a gefen wani ɓangare na musamman da zai tabbatar maka VIP section ne. Ga uban securitys tako ina. Driver ɗin ya sauka da sauri ya buɗe mata ƙofa. Cike da girmamawa ya ce, “Please, ma’am.”
Rasama abin faɗa tayi. Ta sauka a hankali, ƙafafuwanta kamar ba nata ba. Ta kalla wani a cikin security guard ɗin dai daya iso da sauri ya fita da akwatin ta shima. Wani mutum cikin suit ya karɓa daga hannunsa shima yana rissinar da kai irin na girmamawa ya ce, “Welcome ma'am”.
Kanta kawai ta iya jinjina masa ita kam. Dan an gama kasheta da ganin yanda komai ya ke faruwa cikin tsari, ga yanda manya-manyan garata ke bata girmamawa kamar basa ganin yanda take ƴar mitsila a gabansu…
Tafiya suka fara yi a nutse kamar an shirya komai tun tuni. Zuciyarta ta ƙara bugawa, cikin kasa haƙuri ta ce, “Excuse me. Ina zaku kai ni ne wai?”.
Cikin girmamawa mai riƙe da akwatin nata ya furta, “I'm sorry, ma'am”. Daga haka yay shiru. Amma babu wanda ya bata amsar da take buƙatar ji. Sai dai ya cigaba da faɗin, “Follow me, ma’am.”
Nimrah ta haɗiye wani abu a maƙoshinta. A ranta tana faɗin (Na shiga uku ni Naja'atu. Wai mike faruwa ne?) bata da mai bata amsa, dan haka ta bi bayansa kamar yanda ya buƙata. Suna shiga cikin VIP lounge ɗin ta tsaya cak....
Tsaye yake a can gefe cikin suit masu ƙyau da suka zauna a ginannen jikinsa, ba wanda ya fita da su ɗazun da safe a gida bane, duk da ita bama taga shigar tasa ta safiya ba. Kyakkyawan sajen nan nashi dake da adon furfura tsilli-tsilli ya kwanta luff-luff da sake ƙawata kamilallar fuskarsa ma'abociyar kamewa da rashin fara'a. Hannayensa duk biyu a aljihunsa. Tunda suka shigo idanunsa a kanta..
Numfashinta ne taji ya tsaya cak a maƙoshi. Tsigar jikinta ta tashi. A zuciyarta ta ayyana (Kyawu, nutsuwa, da iya tsara ado duk Dadah ya haɗa). Ganin ya nufota cikin takunsa na ƙasaita da nutsuwa ta ɗan sauke ajiyar zuciya.
A gabanta ya tsaya cak, tsaiwa irin ta jaruman soja da suka jiƙu da nagartar girma. Shanyayyun idanunsa suna kanta da wani salon kallo mai zurfi da sanyi. Sai dai akwai wani abu mai nauyi a ɓoye dake fitowa daga cikinsu suna shiga cikin nata. Kasa jurewa tai ta rissinar da natan dake cikowa da hawaye ƙasa....
“Get in.”
Ya furta a hankali yana kamo hannunta cikin nashi daya fitar a aljihu.
Jitai gaba ɗaya ma zuciyarta ta karye. Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafafunta da sukai mata nauyi. Sai kuma cikin rawar murya da ƙunƙuni ta samu kanta da furta, “Dadah Why…?”. A hankali muryarta na rawa.
In dai ji ne Dadah ALLAH ya bashi baiwarsa. Dan haka ya tsaya cak tare da juyowa yana kallonta, duk da bai san ma'anar tambayar tata ba. Kamar yanda itama ta fita ne kawai daga bakin nata batare da sanin akan mi ba ko dalili ba. Dadah Ya ɗan karkatar da kansa kaɗan ya ƙara shanye girman idanunsa a kanta. A hankali shima ya motsa tausasan lips ɗinsa cikin ƙanƙanuwar murya irin ta mai raɗa ya furta, ““Because I need you with me.”
Nimrah ta yi sauri ta kallesa, idanunta suna cike da mamaki da ɗan tsoro. Ya ɗan ɗage mata gira kaɗan, numfashinsa ya yi ɗan zurfi. Sai kawai ta tura masa baki, idanunsa ya kauda cike da basarwa, murmushi mitsitsin murmushi na bayyana a fuskar sa.
Sosai murmushin nasa ya sake keta zuciyar Nimrah. Yanayin wajen yay kamar yana juya mata kowane motsi da kowane numfashin su. Sai take jin kamar duniya ta tsaya cak a tsakanin su biyu kawai. A wannan lokaci, dukkan ƙarfin gangar jikinta da ƙarfin zuciyarta ya gama ɗaukewa.
ReceivedDadah ya ɗan matsa hannunta dake cikin nashi.
Da sauri ta kallesa, ya ɗan ɗage mata gira kaɗan. Sai kawai ta tura masa baki. Idanunsa ya kauda cike da basarwa yana ɗan cizar lips.......✍️
Yanzu tsakani da ALLAH ina Dadah zai kai ƴar cikular yarinyar mutane da daren nan🥺, wannan ai cin amanar ƙawata Nabeeha ne ƙuru-ƙuru a bainar nasi😏 a dinga mana adalci dai mai girma cheff of staff 🏃🏼♀️🏃🏼♀️.
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa) (1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*
Received at 15:49Reactions: ❤
62