← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 113

Sashe 82

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........A bakin ruwan ya samu Faro dake jiransa. Sai dai sam baiga isowarsa ba saboda ya juya baya a jikin motar daya iso da ita yana waya da Biebah. Dadah dake taku a nutsensa ya ƙaraso wajen. Hannu yakai ya zare wayar daga kunnen Faro. Ai ko yay wata kalar juyowa yana kai masa bindiga gafen ciki cike da salon jami'in daya samu cikakken horo.
Ganin Dadah ne ya saka Faro runtse idanunsa da dafe kai ya juya da sauri yana ɗauke bindigar. Dadah daya tsaresa da idanu ya kawar. Screen ɗin wayar ya kalla. Dai-dai Biebah na faman faɗin, “Hello Love! Love baka jina wai?”.
Hankali kwance Dadah ya kai wayar kan kunensa. Hannunsa ɗaya a aljihu yay gyaran murya.
“Nayi seezing wayar”.
Biebah da muryar Dada ta dake ta ta waro idanu tare da dafe bakinta. Cikin rawar murya ta ce, “Na shiga uku Dadah”.
Wani sanyi ya ratsa zuciyar Dadah, tare da ƙaunar ƴar ƙanwar tashi.
Biebah ta shiga gaishe shi muryarta na ɗan rawa.
“Ykk?”.
“Ina lafiya Dadah. Sai dai ina kewar ku”.
“Ƙarya ko?”.
“ALLAH Dadah”.
Ta faɗa cikin shagwaɓa.
Ƙaramin murmurshi yayi, batare da ya sake cewa komai ba ya miƙama Faro wayar yana hararar sa. Amshe abarsa yay yana gimtse dariya. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Biebalo next kada yayanki ya mun yankan rago”.
Dariya ta ƙyalƙyale da shi. Shima ya yanke wayar yana murmurshi. A haka ya buɗe mazaunin driver ya shiga. Dan Dadah har ya shige gefen mai zaman banza. Sai da ya tada motar har suka fara barin wajen sannan Faro ya juyo ya ɗan kallesa. Kan Dadah a duƙe yake yana danna waya. Dan haka Sai ya sake maida kansa ga titi.
“Yanzu asibitin zamu je?”.
Wayar Dadah ya ajiye yana ɗan furzar da iska. Sai da yay crossing ƙafafunsa sannan ya bashi amsa da.
“Ba Imran na tare da shi ba?”.
“Eh suna tare”.
“Kira su kawai mu haɗu acan”.
“Okay”.
Faro ya faɗa yana ɗaukar waya. Cikin ɗan raba hankalinsa tsakanin wayar da titi yay kiran Imran. Bugu ɗaya ya daga. Yasa wayar a hans free.
Daga can Imran yace, “Yaya kun taho ne?”.
“Eh gamu nan a hanya. Kuna asibitin ne?”.
“No mun fito. Yanzu haka gamu a hanyar gidan.”
“Oh har yazo kenan?”.
“Tun ɗazu ma. Kawai mu haɗe daku a can”.
“Okay”.
Wayar ya yanke.
Shiru ya ɗan ratsa motar, sai kuma zuwa can Dadah ya katse shirun.
“Ya jikin yaran nan guda biyu?”.
“Humm ka bari kawai sai a hankali wlhy. Brain ɗin yaran baida ƙarfi. Shiyyasa hodar iblis ɗin tai musu illa da yawa.”
Dadah ya ɗan taune lips. Cike da takaici.
“Ina zaton akwai abinda suke haɗa musu a ciki. Ya kamata ayi gwaje-gwaje a kanta”.
“Nima nayi wannan tunanin. Dan har nake ma Imran bayani. Dama dawowarka muke jira”.
“No wannan ba abinda za'a jirani bane. Kawai a aiwatar”.
“Shike nan, in sha ALLAHU muna komawa”....

%==%==%==%

Nimrah data gama ƴan koke-kokenta falo ta koma. Ta hau kujera ta zauna tare da ɗaukar mayafi ta rufe ƙafafunta dan akwai sanyi. Ga skirt ɗin jikinta ƙarami. Koma ace kayan duka. Damma Dadah ya saka mata Safa a ƙafa da kansa bayan sun idar da sallar magriba. Television ta kunna, ta saka ƙarar can ƙasa. Sai kuma ta ɗauka bowl dake cike da grapes ta sa a cinyarta. Sai da takai ɗaya baki sannan ta ɗauki wayarsa ta fara ƙoƙarin kiran Mammah.
Yau dai cikin sa'a ta shiga. Wani farin ciki ya tsarga mata. A take murmurshi ya ƙawata fuskarta. Damuwar da Dadah ya barta a ciki ta gudu. Cikin ƙaguwar a ɗaga mata tace, “Mammah ɗaga Mammah”.
“Ai na ɗaga Autar Mammah”.
Mammah ta faɗa daga can tana dariya. Itama Nimrah dariyar ta ƙyalƙyale da shi da faɗin, “Mammah na i miss you irin mai cika duniya ɗin nan”.
Anan ma Mammah sai da ta dara. Ta ce, “Auta ƴar Mammahn ta. Ina fatan kina lafiya?”.
Da sauri Nimrah ta fara gaishe ta. Mammah ta amsa da kulawa tana tambayarta yaya take?.
“Mammah ina lafiya. Sai kewar ku. Ina jin kamar nayi tsuntsuwa na zo na ganku. Mammah ina su Yaya Mu'azz?”.
Kafin Mammah ta amsa karaɗin su Ruky ya cika falon ita da Mu'azz. Suna kitchen ne dama wai suna wainar fulawa. Dan yanzu anan su bayan la'asar ne. Su kuma Dubai na jiran isha'i ma dan bakwai ta gota sosai.
“Kin gansu nan ma sun ishe mu da rigimarsu tunda ke ALLAH ya hutar dake ta kwana biyu”.
Cikin dariya Nimrah tace, “Mammah Yaya Mu'azz ɗin ne sai a hankali. Rinton sa yayi yawa ne”.
Mammah bata kai ga bata amsa ba Mu'azz ya iso wajen yana kawo ƙarar Ruky data zabtare waina wai ita da Ninah. Dan yanzu tsabar fitina idan za'a raba abu sai tace sai an raba da Ninah, kuma itace mai cin gadonta. Mu'azz na jin an ambaci Nimrah ya saki batun faɗa yana matsowa kusa da Mammah da kwalama Ruky kira tazo. Ai dole Mammah ta miƙa musu wayar ganin suna shirin hayeta. Su Kulu na kwasar dariya da Gwaggo Khadijah data fito.....

»»««»»««»»««

A hanya su Dadah suka haɗe da su Imran dake cikin wata zuƙeƙiyar mota baƙa wulik. Dan duk da tasu Dadan ma nada shegen ƙau wadda su Daddy Imran ke ciki ta fita.
Leƙowa kawai Imran yayi ta window ya miƙoma Dadah tab. Daga haka kowa ya maida gilashinsa ya zuge suka tafi a jere. Gida ne kyakkyawan gaske, sannan katafare bana wasa ba, dan kai tsaye zamu kirashi da Mansion ne. Yanda suna isowa aka wangale musu gate zai baka tabbacin an san da zuwan su.
Akwai securitys a gidan sai dai ba masu yawa ba. Dan da'alama gida ne na sirri. Security ɗaya dake tsaye a ƙatuwar ƙofar shiga cikin gidan ya matso gaban motocin, dan basu tsaya a ko ina ba sai gaban ƙofar.
Ido suka haɗa da Dadah. Yay masa signal da nashi idon da ake gani kaɗai. Dan akwai facemask daya sanya. Dadah ya kawar da nashi idanun sannan ya fito dan security ɗin harya buɗe masa. Suma su Imran dun fitowar sukai. Sai dai yanzu ɗaya ya ƙaru a cikinsu. Su duka sun rufe fuskokinsu da mask suma. Dan shima Dadah ya saka, sanda yake fitowa kuma ya sake ɗora baƙin gilashi daya lulluɓe ainahin ƙwayoyin idanunsa. Dama ga kayan jikinsa komai baƙi, hatta hannayensa akwai safar hannu a jikinsu.
Zaratan mazajen huɗu suka rufa masa baya. Dan ɗayan da ya sake ƙaruwa a cikinsu yasa su zama huɗu bayan Imran, Faro, T-Dalha. Sai dai kasancewar fuskokinsu a rufe suke bazamuce waye shi ba. Suna isowa ƙofar ta rabe biyu a hankali. Wani azababben luxury parlor ya bayyana. Kai da gani kasan kuɗi sun jigata. A bakin ƙofar computer ce zatai searching nasu kafin su wuce, ai ko Dadah ya danna agogonsa a kaikaice. Na'urar ta gama zuƙe-zuƙenta ta sanar da babu komai a tare da shi tana danna green danja. Hakama su Imran ɗaya bayan ɗaya sai da ƙofar tai musu. Suma kuma babu wani damuwa suka wuce.
Wata kyakkyawar doguwar farar mace dake sanye cikin jar doguwar riga da akai ma wata shegiyar tsaga tun daga ƙasa har ƙarshen cinya ta taso tana wani kalar juya siririn jikinta mai kama dana tarwaɗa. Daga sama kuwa rabin ƙirjinta a bayyane yake. Cikin wani kallo dake bayyana ainahin fitinar dake ranta tabi Dadah da kallo. Shi kam bamace kallonta yake ba ko a'a. Dan idanunsa na cikin gilashi. Cikin yarfar da hannu da karya jiki tai musu baraba da zuwa da harshen turanci.
Dadah ya ɗaga mata yatsu biyu kawai. Sai ta saki wani mugun murmushi. Sannan tai wani juyi da jikinta ta fara tafiya. Babu wanda yay magana suka take mata baya. Ƙayataccen staircase ɗin dake tsakkiyar falon ta fara takawa, daga gani kasan akwai zinari a kwalliyar dake wajen. Ta tsaya a step ɗin farko tana juyowa. Cikin wani irin kaɗa yatsunta a jikin gilashin staircase ɗin da salo irin na iskanci ta ce “Shi kaɗai zai haura”. A take Imran ya zaburo zai yi magana amma sai Dadah ya ɗaga masa hannu. Wani alama yay musu da yatsunsa batare da yace komai ba yay mata nunin suje.
Tayi murmurshi mai haɗe da lumshe idanu. Sai kuma ta botsare ta fara wata banzar tafiya. Dadah ya kawar da kansa cike da takaici yana jan tsaki a zuciyarsa. Eh shi mai yawan buƙata ne. Amma a kan halattacen nama. Shifa ko mace zatai zir a gabansa in har ba halak ɗinsa ba koda yana cikin yanayi ne baya jin ta birge shi. Dan a rayuwarsa zina da shaye-shaye suna cikin abubuwan da yafi tsana a ruhinsa. Sai dai hakan baya hana shi yin addu'a ga masu yi da musu fatan dainawa idan suna da rabo. Tare da nema wa wanda basayi da shi kansa kariya wajen UBANGIJI na har abadan. Dan wasu mummunar ƙaddararsu ce ke musu jagora fara aikatawar. Shima mutum ne kuma kamar kowa bashi da tabbacin tsallakewa sai da yarda da kariyar ALLAH...........✍️
KIƊA A RUWA 3

98
Chapter 82 · 0% Book details