Sashe 108
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..........Nimrah ta gaishe da Daddy Imran bayan ya gaisa da su Mammah shima. Dai-dai nan aka buɗe gate ɗin gidan. T-Dalha ya fito cikin hanzari yana faɗin, “Ya salam Sir miyasa zaku tsaya nan. Ina bayi ne yanzu na fito nake ganinku ta cctv. Bari a buɗe gate ɗin ku shiga ai zai fi”.
Cak numfashin Nimrah ya tsaya da jin wannan murya. Yayinda Daddy Imran ke ce masa indai basu takura kowa ba nan ɗin ma yayi abar motocin. Badan T-Dalha yaso ba ya bari. Sai kuma ya ƙaraso wajen su Mammah yana musu barka da zuwa. Idanunsa suka sauka akan Nimrah da ke jin kamar zuciyarta zata zubo ƙasa.
Eh shekaru sunja, daga na ƙuruciya zuwa girma a gare ta da shi kansa wanda take gani a gabansa. Rayuwa ta sauya daga ƙauye zuwa birni. Jin daɗi da wayewar kai sun zama ado. Amma hakan bazaisa ta taɓa manta wannan fuskar da bata canja daga yanda ta santa ba face girma da jin daɗi da wayewa da suka sake ƙawatata.
“K...k..k... Kawu Tanimu!”.
Kalmomin suka fita a bakinta tamkar mai in ina. Shima dai kallonta yake. Haka ma Mammah da Gwaggo Khadijah da basu san komai ba. Dadah kam da sai yanzu yake fitowa a motar da Daddy Imran kallon juna sukayi, kafin su maida idanun nasu kan Nimrah da T-Dalha...
Kafin wani yay magana a cikinsu Nimrah ta ƙaraso gaban Kawu Tanimu da sassarfa. Jikinta kam rawa ma yake kaf-kaf. Ga hawaye na rige-rigen sauka. Kamar zararriya ta juyo ta kalli su Mammah dake kallonta da mamaki.
“Mammah mafarki nake ko? Irin wanda na saba yi. Dan ALLAH karku tashe ni, ku bari nayi magana da shi. Shi ɗin Babana ne. Na tabbatar zai gaya min duk abinda nake son sani....” sai kuma ta sake juyawa inda Kawu Tanimuda hawaye suka cikama ido yake. Wlhy baiyi zaton zata gane shi ba. Yama zata ta manta da shi fa, ashe yana ranta, har mafarkinsa take yi.. Tuni ya manta da ma kasancewar Dadah a wajen, hakama inda suke. Jikinsa na ƴar rawa shima ya kamo hannunta cikin nashi.
“Ba mafarki kike yi ba Zakanyata. Kawu Tanimun ki ne a zahiri ba wani daban ba. Ashe tsahon shekaru bazai sa ki manta dani ba Nimrah. Hakama ƙuruciya....” sai ga hawaye shaaa na gudu a fuskarsa.
Maimakon amsa jikinsa kawai Nimrah ta shige ta wani ƙanƙamesa itama tana fashewa da kuka mai ban tausayi.
Dadah ya kawar da kai. Murmurshi Daddy Imran dake lure da shi yayi. Mammah kam da mamaki ya cika ita da Gwaggo Khadijah. Cikin sauri take faɗin, “Ikon ALLAH. Bawan ALLAH da gaske kai jinin Nimrah ta ne?. Imrana ina kuka sanshi?”.
“Mammah labarine mai tsaho. In sha ALLAHU yanzu duk zaku ji komai. Sai yay ɗan gyaran murya yana kallon T-Dalha da har yanzu Nimrah ke jikinsa tana rusar kuka, shima hawaye share-share a fuska, kamar ba jarumin ɗan sandan farin kayan nan ba.
“Inaga mu shiga daga ciki zaifi. Duk da babu mutane anguwar wani zai iya gittawa”.
Furucin Daddy Imran ne ya maido T-Dalha a hayyacinsa. Da ƙyar ya iya ciro Nimrah a jikinsa. Su Mammah dai sun gama fahimtar ko waye wannan mutumi yana da alaƙa mai ƙarfi da ƴarsu..
Sun shiga gidan, sai dai Dadah ne ƙarshe. Dole Daddy Imran ya dawo baya suka jera. Cikin magana ƙasa-ƙasa ya ce, “Babanta ne fa, kada kayi kishi dan ALLAH”.
Shiru Dadah yayi kamar baiji ba. Shima Daddy Imran sai yay murmurshi kawai. Dan shi kaɗai yasan abinda ya hango a idanun mutumin nasa a lokacin da Nimrah ta rungume Kawun nata.....
(0)+(0)+(0)+(0)+(0)
First Lady da Hajja Mangu sun iso asibiti duba Hajiya Hasiba. A lokacin Jiddah ta dawo su kuma su Ismat na shirin komawa gida dan su yi wanka. Dan sun gaji da kiran Number ɗin Nabeeha da bata sake ɗagawa ba.
Har lokacin barci take. Dan haka suka gaisa kawai da su Jiddah. Tsabar bariki sai take tambayar wai miya faru?. Rayhana ta bata labari dalla-dalla. Cike da barikanci ta nuna tashin hankali ta. Har tana jaddada dole ne yanzu taje ta sanarma IG ko su waye wannan sai an nemo su. Da wannan yaudarar suka baro asibitin da wuri. Su ko su Jiddah duk sun yarda har ransu da gaske take. Dan hatta Rayhana abinda First Lady taso ta sani kawai ta sanar mata. Dan ko cikakkiyar manufarta akan Nabeeha bawai ta bayyana mata bane. Ta dai nuna mata kawai tana son Nabeeha tabar gidan ne...
Yanda First Lady ke kwasar dariya kamar wata shashasha yasa Hajja Mangu zuba mata idanu kawai. Dan ta ƙara sarewa da muguntar matar nan wlhy. Ta jima bataga mace mara imani da tausayi ba irinta. Dan sanda mijinta ke mulki idan buɗe ɓarnar da tayi za'ai ALLAH ƙuda bazai bi ba sam saboda munin abubuwan. Amma da yake ƙasarmu ƙasar daɗi ce gata nan tana rayuwa babu abinda aka rasa sai mulkin kawai. Kuɗi ne an ɗiba an ɗiba har ba'a san miza'ai da su ba. Shiyyasa yanzu haka ɗan nasu tilo namiji da su Nimrah suka bubbuge an maidashi ma ƙasar waje acan ya ƙarasa Secondary ɗin tasa zai fara jami'a. Matan kuwa guda biyu duk suna ƙetare da mazajen su. Ita kanta tasan wannan masifar bin matan data sakama ranta ne yasa bata son barin ƙasar, sai dai ta fita ta ɗan huta ta dawo...
Bayan sun iso gida ne take tambayarta wai miye shirinta haka akan Hasiba ɗin?. Shine tace mata ta jira ai zata gani. Daga haka Hajja Mangu bata sake tambaya ba....
<<<<<<★>>>>>>
Kamar yanda gidan yake ɗan cas-cas madaidaici haka falon nasu ma ya ƙayatu cikin tsari dai-dai misali da girma. Har yanzu hannun Nimrah na maƙale dana Kawu Tanimu. Dadah dai ya dake ya fiske da ƙara kamewa. Sai da suka zauna kuma fitowar matarsa Maijiddah ta kawo ruɗani musamman ga Mammah da Nimrah da Gwaggo Khadijah.
“Kulu!”.
Cewar Mammah data kasa riƙewa. Kan Maijiddah a ƙasa cikin girmamawa ta ce, “Na'am Mammah sannunku da zuwa”.
Nimrah ko ta kalli Kawu Tanimu ta kalli Kulu. Haka ma Daddy Imran ya tsare Kawu Tanimu da idanu. Kawu Tanimu yay murmurshi da faɗin, “Ayi mana afuwa Sir! Zan ƙarasa warware muku komai in sha ALLAHU.”
“Humm” kawai Daddy Imran ya iya faɗa. Dadah kam ma shi idanunsa nakan wani ƙaton hoto dake facing inda yake. Bana kowa bane kuma face hoton Nimrah, bayan shi akwai wasu kala-kala a falon. Ita kanta da su Daddy Imran a yanzu hotunan suke bi da kallo. Kaf ɗin su kuma bata san sanda akayi su ba. Dan wasu ma da Uniform ne. Harda wasu biyu tare da Ruky. Yanda take bin hotunan da kallo haka su Mammah ke bi. A haka Kawu Tanimu da Kulu suka shigo da kayan sanyi suka ajiye musu.
Suna sake haɗa ido da Nimrah ya sakar mata murmushi. Hawayen da suka cika mata ido ne suka zubo itama tai masa murmushin. A zuciyarta faɗi take (Ashe har yanzu Kawunta ta sonta...)
Kayan sanyin da aka dire musu ruwa da lemuka na tatattun ƴaƴan itatuwa da Kulu ta haɗa saboda sanin Dadah baya shan na gwangwani ne. Kawu Tanimu da kansa ya zuba ma Daddy Imran da Dadah. Koda ya zuzzuba a kofuna sai ya ajiye a table ɗin gabansu sannan ya zauna yana sake musu sannu da zuwa. Su Mammah kuma Kulu ke zuba musu. Tana kammalawa taja hannun Nimrah dan ta tayata kwaso abinci.
Kawu Tanimu zai fara musu gaisuwar oganni da yaro Daddy Imran ya hararesa da faɗin, “Yau matsayin surukai muke anan ai ba Ogannin aiki ba. Shiyyasa ma muka ce ka bari mu fara zuwa mu kawo maka girmanka kafin kai kaje gare mu.”
Murmurshi Mammah da Gwaggo Khadijah sukayi. Shima Kawu Tanimu sai yay murmurshin da faɗin,
“Haka ne Sir, ina godiya sosai. ALLAH ya saka muku da alkairinsa. Yay musu sakamako da makulayen gidaje a aljannarsa. Tabbas Nimrah ta samu dukkan gata a wajen ku da ba lallai ace ko mu da muka haifeta mun bata ba. Yanda kuka riƙe wannan amana UBANGIJI ya riƙe muku amanonin naku zuriar kuma. Wlhy bamma san da wane baki zanyi godiya ba ko nuna farin cikina Mammah sannunku sannunku....”
Gwaggo Khadijah ta ce, “Karka damu wannan yima kaine. Muma a yanzu Nimrah ta zama tamu. Muna mata kallon jininmu ne. Idan ma bamu haɗa da ita ba, in sha ALLAHU zata haifa mana”.
“Wannan haka yake”.
T-Dalha ya faɗa yana murmushi kansa a ƙasa. Sai kuma ya ɗan saci kallon Dadah da har yanzu baice komai ba... Daddy Imran ya katse shi da faɗin, “Amma fa ka sake sakamu a ruɗani. Dama kana da alaƙa da Kulu?”.
Murmurshi Kawu Tanimu yayi tare da shafa kai. “Ayi haƙuri Sir! Wancan karon ba komai na gama buɗe muku ba ai saboda rashin lokaci. Amma yanzu komai da kuke son ji zan sanar muku. Kusha ruwa dan ALLAH, ga abinci za'a shirya muku.”
Yay maganar yana miƙewa.........✍️
123
.......Inda su Nimrah suka shige shima ya shiga. Ƙasa-ƙasa Dadah ya bishi da kallo. Sai kuma ya basar. Daddy Imran dake lure da shi yay murmurshi. Cikin ƴar raɗa yanda su Mammah ba zasu ji ba dan suna ɗan nesa da su ya ce,
“Duk surukutar ce wai?”.
“Humm”.
Kawai Dadah yace. Daddy Imran yay ƙaramar dariya da faɗin, “Zak.. nawa. Badai kishi kake ba har yanzu dan Daughter ta rungume shi. Babanta ne fa. Badan tana da nutsuwa ba ai abinda zaka gani sai yafi haka. C-mon My Lion”.
“Ikon ALLAH wai ka koma sharri ne?”.
Dadah ya faɗa a karo na farko yana zuba masa harara a karkace. Murmurshi Daddy Imran ya sake yi. “Ba wani sharri. Nasan waye Zaki na ai. Sai dai na bama wasu labari. Dan ALLAH ka sassauta fuskar shakkar ka yake ji sosai ALLAH, kana ganin duk ya kasa nutsuwa da sakewa da ita”.
Rasa ma abin cewa Dadah yayi ga Imran. Sai kawai ya ƙyaleshi...