← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 113

Sashe 13

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

          WASHE GARI Litinin tushen aiki. Ƙarfe shida da rabi na safiya Bilal da Ammar masu fita aiki nata saurin zaman shan shayi da Mammah kan tsaresu shansa dole kafin su fita sautin takun da suke jiyowa daga stairscase ya saka su juyawa suna kallon wajen. Ba su kaɗai ba harda Mammah da su Kulu dake tsaftace falon. Isowar sirrintaccen ƙamshin turarensa ya tabbatar musu da mai gayya da aiki ne. Kafin ya bayyana a cikin idanunsu. Babu wanda bai ambaci Masha ALLAH ba a zuciya.
Received at 4:41 PM
reacted with ❤Saboda yanda Dadan ya fito a jarumin jarumansa. Baya buƙatar kurantawa ko wasawa, ko maƙiyinsa ya gansa dole yaji eh lallai wankan ya wanku. Sosai Suit ɗin sun zauna masa a jiki tamkar kayan gadonsa.
        “Anya yau ba Dadanmu za'a kalla matsayin shugaban ƙasa a fadar shugaban ƙasar ba”. Bilal ya faɗa da iya gaskiyarsa. Amshe masa Ammar yay da shima. “Yaya kamar ka shiga zuciyata ka karanto abinda ke cikinta.”
     Dada daya ƙaraso kamar yasan gulmarsa suke ya zuba musu harara. Zamansu suka gyara kuwa kowa na haɗiye sauran gulmar a zuciyarsa. Mammah tai murmurshi, cikin kafesa da ido ta ce, “Kun haƙura dai kenan?”.
         “To Mammah ya zamuyi kema kina bayan Janar”.
    Nan ma murmurshin ta ƙara yi, dan jiya da dare ya shiga mata hira yake mata ƙorafin wannan aiki. Shine tai zama na musamman ta masa nasiha yanda ya kamata. Bai dai ce komai ba a jiyan, amma tasan dama bazai bijirema lallashinta ba. Ya sake gaisheta, suma su Bilal suka gaishe shi duk da sunyi a ɗazun da suka dawo salla. Mammah tasan bazai ci abinci ba a yanzu. Dan haka ta saka Kulu kawo masa zallar ruwan zafin da babu komai a cikinsa. Shi kuwa yasha, yana cikin sha ɗin ne Mu'azz ya fito dan shima zai wuce makaranta. Sai ga Biebah dake son shiga kitchen.
     Duk gaishe sa sukayi. Ya amsa musu da kulawa. Dai-dai ya miƙe Bilal ke tambayar su Nimrah. Mu'azz ya ce, “Tab Uncle kaima kasan suna can suna barci. Tunda suka daina zuwa makaranta ai suka samu wannan lasisin. Yanzu haka sai su kai sha ɗaya a gado”.
       “Mu'azz kaji tsoron ALLAH banda sharri. Suna kai dai tara amma ba sha ɗaya ba ”.
      Biebah ta faɗa tana hararar sa. Mu'azz ya tura baki da faɗin, “To Small Mom miye marabar 9 da 11 ɗin?”.
        “Awa biyu”.
    Ta sake bashi amsa tana hararar tasa dai. Shi dai Dada baima nuna yana jinsu ba. Hasalima sallama yayma Mammah dake jera masa addu'oi sannan ya fice. Su Ammar na take masa baya..........✍️
Received at 4:41 PM.........Sun fito compound da Sanda ya gama sharewa tsaf, dan yana tsaka da banruwan fulawa ne ma ya hangosu ya ɓuya. Sai maigadi ne ya zo da sauri yana gaishe da Dada. Sannan suka gaisa dasu Ammar.
         “Alhaji dama tun ɗazu baƙi suke jiranka.”
    Da mamaki Dada daya ɗan zuba masa ido ya furta, “Baƙi?”.
     “Eh wlhy suna wajen gate. Sai dai daga gani jami'an tsaro ne. Amma fa da wasu zuƙa-zuƙan motoci suke baƙaƙe wulik kamar na shigar shugaban ƙasa”.
      Dada baiyi magana ba, sai ma juyawa yay ya kalla Bilal. Bilal ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya miƙama Ammar briefcase ɗinsa ya nufi gate, sai kuma akai sa'a ma jami'an dake a gidan tun dawowarsa sai ga shugabansu ya shigo. Tare suka dawo inda Dadan yake da Bilal, yay gaisuwa. Kai kawai Dada ya jinjina masa.
     Cikin ƙara gyara nutsuwarsa ya cigaba da faɗin, “Sir! Masu rakkiyarka ne daga fadar shubagaban ƙasa. Idan ka amince zan shigo da shugaban su”.
     Kallon juna Bilal da Ammar sukayi suka kashe ido da jinjina. Sai kuma suka gimtse murmushin fuskokinsu dan dai-dai nan Dada ya jinjinama jami'in kai. Da alama yau babu ƴan maganar a kusa. Da sauri kuwa Jam'in ya juya, dan ya gane yaren Boss ɗin. Babu jimawa suka dawo da wani mutumin dake sanye cikin baƙaƙen suit shima. Bazai wuce sa'an su Ja'afar ba. Sai da suka iso wajen yay gaisuwa irin ta girmamawa sannan yay bayanin dake tafe da shi.
         “Ranka ya daɗe, bisa umarnin Shugaban Ƙasa, mun zo ɗaukar nauyin tsaronka da rakkiyarka zuwa Office.”
        Birkitattun idanunsa ya zubama jami'in, aiko bawan ALLAH babu shiri yay ƙasa da kansa. Zuciyarsa kuwa sai bugawa take da sauri-sauri. A ransa ya furta, (Tab wlhy bazan iya ba. Dama haka mutumin nan yake da cika waje. Ina wannan filin ba nawa bane dan zan iya tona kaina). A zahiri kuwa ya kasa ɗago kai ya kalla Dada a karo na biyu, shima kuma baiyi magana ba ya nufi gate abinsa. Da sauri su Ammar suka bisa kuwa, dole suma suka take musu baya.
         Tabbas maigadi baiyi ƙarya ba. Zuƙa-zuƙan motoci ne da ko wanda bai san mota ba yasan an saye su da kuɗaɗe masu nauyin gaske. Ga wasu baradan jaruman tsaye masu jiran kota kwana. Suna fitowa duk suka sake nutsuwa, sai kuma sukai caaa suna miƙa gaisuwa. Hannu kawai ya ɗaga musu..
         Wanda ya masa bayani a cikin gidan nan ne dai ya buɗe masa motar tsakkiya da saurinsa. Dada yay ɗan jimm yana karanta addu'ar hawa abin hawa kamar yanda ya saba koda tashi ce sannan ya shiga ya zauna. Jami'in ya maida ya rufe. Sannan ya zagaya gaba ya zauna ta gefen mai zaman banza, cikin waɗancan kuma wani ya buɗe mazaunin driver ya shiga. Matsowa su Bilal sukai suka masa bye, ya jinjina musu kai yana lumshe idanunsa.
       Suma sauran jami'an duk sun shiga sauran motoci biyun. Daga haka suka harba kan titi. Kasa haƙuri su Ammar sukai sai da suka koma cikin gidan kaima su Mammah rahoto. Dan Ammar ma harda video ya ɗauka dama. Kuma ya ƙudiri aniyar ɗorashi a media dan zukatan maƙiya su buga.....

^^^^^^^^^^^^^

       A ɓangaren Daddy Imran ma hakan ce ta faru. Yayi shirinsa tsaf cikin Suit masu duhu Ammie tai masa rakkiya compound da shirin shiga motarsa, Asma'u dake riƙe da briefcase ɗinsa na roƙonsa bin Ammie kasuwa dan za'ai sunan Aunty Lailah gobe, shi kuma yace a'a tanata shagwaɓa. Gefe Khalifa na mata dariya, Lolo kuwa na ɗakinsa yana shirin makaranta. Isowar mai wankinsu ya katse faɗan Khalifa da Asma'u. Ya gaishesu sannan yake sanar muku baƙin dake gate.
     Mamaki ya kama Daddy Imran sosai, amma sai yace maiwanki ya shigo da Ogansu yaji lafiya. Saɓanin na Dada shi nashi sojoji ne, duk da dai a wanda ke waje akwai wasu jami'an harda ɓoyayyu ma. Yanda akaima Dada bayani anan shima haka akai masa. Yasan hakan normal ne dama, amma yayi tunanin sai sun fara zuwa office a yau sannan za'a basu waɗan nan damammakin. Dole yay sallama da iyalinsa yana sake jaddadama Asma'u karta fita ko'ina. Daga haka aka buɗe masa mota suka wuce fadar shugaban ƙasa.
Chapter 13 · 0% Book details