← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 113

Sashe 95

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   ...★ Anan kam kusan tare members na ƙungiyar duhu suka sauke ajiyar zuciya. Domin kuwa wannan kira nasu ne bana Dagger ba.
     A daren jiya duk wani mai alaƙa da ƙungiyar ya dawo gida. Cike da matsanancin ruɗanin abinda ya faru da Oga Jush. Tun a jiyan suke meeting. Sai faman ƙullawa da kwancewa suke tare da hasashe-hasashe. Daga ƙarshe dai suka yanke komawa yin amfani da Nimrah kamar yanda Oga Jush ya tsara kafin mutuwarsa. Shine suka saka Dagger ya kirata tunda dama shine ya fara aikin.
       “Woow aiki mai ƙyau Dagger”.
   Viper ya faɗa cikin katse shiru da tunin da ɗakin meeting ɗin ya ɗauka. Murmurshi Dagger ɗin yayi, zuciyarsa na ayyana masa (Kaina nake ma wannan aikin ba ku ba. Tunda Oga Jush ya tafi gara na ɗauke Nimrah ta mu kama gabanmu muma) a zahiri kuwa godiya yay ma Viper dama sauran shugabanin dake nuna yabawa.
        Mr Specter ya miƙe, cikin gyaran murya ya fara magana da isar daya saba.. “Yanzu dai mun samu bakin zare na farko da zamu tabbatar da zarginmu da ya karkata akan Zak-Shadow sakamakon binciken da muka yi a kansa. Inda muka samu tabbacin tafiyar da yayi kwanaki ƙasar Dubai yaje. Wannan yasa bazamu taɓa cire zarginmu a kansa ba game da kisan shugaba. Duk da a yau sabon bayani ya sake fitowa game da budurwarsa. Ba zamu ƙi amsarsa zancen su ba. Tunda iya tunaninmu mun rasa makamar riƙewa dangane da abinda ya faru da shi. A labarin sirri dana samu daga majiya mai ƙarfi  game da rasa Oga daren jiya shine budurwarsa ce ta kashe sa. Dan bincike ya nuna sunyi faɗa a watannin baya da shi, inda har ta nema suyi aure shi kuma yaƙi, ita kuma tace dolene fa wannan aure nasu ayi, idan ba haka ba zata bashi mamaki. Dan zata kai shi kotu tare da bayyana ma duniya ɗan da suka haifa tare tun shekarun baya da shi kansa bai san da shi ba na nan. Da farko ya ɗauki maganarta ƙarya da wawanci, sukai faɗa sosai suka rabu. Sai dai ya kasa samun nutsuwa ya shiga binciken ta batare data sani ba tsahon watanni. Kwatsam a watan daya gabata ya gano maganarta gaskiya ce. Ta haifi yaro tun a farko fara mu'amular su, amma ta kai yaron gidan marayu ta ɓoye. Yabi wasu hanyoyi domin ɗauke yaron dan yana masifar tsananin kama da shi amma ya samu duk ta toshe, daga ƙarshe ma data gane yana bibiyarta sai ta ɗauke yaron ta sake ɓoye shi. Wannan shine dalilin da yasa muka kasa gane kanshi kwanaki da yin sakaci da komai na ƙungiya, shine kuma dalilin koma mata ya bata haƙuri ya kuma ce ya amince, sannan ya buƙaci ta bashi yaron ko ganinsa yayi. Ta amince zata bashi, sai dai da sharaɗin dukkan dukiyarsa zai maida da sunan ɗan nasu ko ya yarda dai ayi aure. Anan ne ya gane manufarta a kansa, wato ta ajiye yaron matsayin makami dan ta mallaki abinda ya tara shiyyasa take son suyi aure. A zahiri baiƙi ba, ya amince mata, sai dai ya shirya mata shima da shiri na musamman, dan haka ya yaudareta suje Dubai su huta daga nan suyi baiko sai ya shigo ya gana da mu ya kuma ƙaddamar da sabon tsare-tsare na ƙungiya. sai ya sake komawa wajenta suje suga yaro ya kuma mallaka komai gareshi na dukiya. Ita kuma suyi aure. Batai ko musu ba duk ta amince, sai dai itama da nata shirin take. Shirin nata ne kuma ta aiwatar, duk da masu fashin baƙi sun shiga rikicin tunani akan miyasa zatai haka batare da samun damar mallakar dukiyar ba? Wasu kuma na kallon lamarin da Oga Jush ɗin ne ya fara kai mata hari kota gano manufarsa shiyyasa... To gaskiya dai ta gagara bayyana. A yanzu haka jami'an ƙasar su dana ƙasar Dubai abinda suka duƙufa nema kenan wannan gaskiyar da dalilin kisan da sukaima junan. Dan an gano bullet ɗin da aka harbi budurwar har sau biyu na Oga Jush ne. Shine yake amfani da shi a bindigar daya saka aka ƙera masa ta musamman daga zinari. An kuma samu bindigar a ɗakin itama.. kunga kenan basu kaɗai ba harmu muna buƙatar sanin wannan gaskiyar, sannan zarginmu nada ƙarfi akan Zak-Shadow”.
        “Tabbas haka ne. Dan ko zamu yarda da wancan labarin dole mu fara tabbatar da babu hannun matsiyatan can guda uku. Janar, Zak-Shadow, Imran. Dan ni kaina bawai wancan labarin bai kama hankalina bane. Zuciyata ta kasa gamsuwa ne. Musamman idan mukai dubi da tafiyar Zak-Shadow ɗin ta sirri a kwanakin nan. Mutumin nan makiri ne, zai iyama haɗa hannu da yarinyar ai...”
       “Wlhy komai zai iya faruwa indai matsiyacin yaron can ne. Dan haka dole ne barci ya ƙare mana daga yanzu. Dan in har da hannunsa to mu tabbatar ya mana duka ne a ƙashin baya. Idan mukai sakaci zamu koma rayuwa ne a wheelchair kamar masu ciwon laka....”
      “Tabbas indai da hannunsa wannan shine target ɗin sa a kammu. Amma idan yasan wata ai bai san wata ba. Idan ya dake mu a baya ta hanyar kashe Oga Jush, mu kuma zamu dake sa a zuciya ta hanyar yin amfani da matan aurensa guda biyu. Dan a yanzu haka wasan mu ya fara, yana can a buge kuma zai iya ɗaukar sati guda a haka, zamuyi amfani da wannan damar domin kafa sabon tsarin ƙungiya, bazamu bari yaci nasarar shirinsa ba. Rikita mu, sace mana gwiwa, da hargitsa mu. Zamu haɗa zaman makokin Oga Jush da samar da sabon shugaba a tare, hakan ne zai bamu damar shimfiɗa sabbin ayyukanmu kafin ya dawo hayyacinsa. Zamu fara da zaɓen candidate guda biyu a yau ɗin nan, amma sai zuwa dare muje mu fara nazari..”
     Kowa ya gamsu da tsarin. Dan haka aka buga table. Sannan akai shiru na mintuna biyar. Ma'anar shirun shine zaman makoki....

        <%><%><%><%>

     Duk da a hargitse ta fito, koda tazo ƙofar shiga sashen sai ta nutsu ta saita kanta sannan ya shiga. Da Daddy Imran ya fara cin karo a falon. Wanda tunda ya mata kallo ɗaya shima sai ya kauda kansa. Inda yake ta ƙarasa, cike da girmamawa ta durƙusa tare da faɗin,
        “Dadday ina kwana”.
   “Lafiya lau Nimrah, kin tashi lafiya”.
Maimakon amsa saita ɓata fuska zatai masa shagwaɓa. Murmushi yayi kawai, cikin katseta ya ce, “Dadan ku ne baida lafiya. Yana bedroom an saka masa drip. Shiga ki zauna da shi zanje wani waje yanzu na dawo na samu kiran gaggawa”.
     Sosai ta nuna tashin hankalinta. Dan da ƙyar ma ta saurare shi yay mata bayanin idan ruwan ya ƙare zata iya cirewa?. Tace eh zata iya. Yace to taje, amma karta fita ko ina ga abinci nan ya kira za'a kawo daga sashen Mammah. Kai ta jinjina masa cike da girmamawa tana miƙewa..........✍️
110

.........Koda ta shige shi ficewa yay dan Dabo ne ke kiransa akan wani babban al'amari daya taso. An kama wata mota da bomb a kusa da fadar shugaban ƙasa. Bama Dabo ɗin kaɗai ba har Janar tun ɗazu yake neman layinsa matsayinsa na NSA amma bai samu ba. Shima Dabo dan wannan layin na sirrin su ne daya shafi UNIT ZERO shiyyasa ya samesa.
       Sosai Nimrah ke kallon Dadah kamar zatai kuka. A ranta kam tana mamakin miya same shi haka bayan jiya lafiya lau suka rabu har lokacin barci, zancen Dagger ya shiga dawo mata (Kije ga mijinki dan yau kaɗan ya rage kishiyar ki ta halaka shi da ƙwaya....). Mi hakan ke nufi? Mi zai sa Nabeeha ɗin ta aikata haka to?. Kai ina bata yarda ba. To amma mizai sa taƙi yardar? Bata da mai bata amsa dan haka ta share hawayen dake neman zubo matan tana kaiwa zaune. Samun kanta tai da riƙo hannunsa na haggu dake a saman cikinsa, dan ana damar ne aka saka masa drip ɗin. Cikin nata ta rumtse, duk da yafi natan girma. Ga wani irin taushi kai bakace hannun namiji bane, namijin ma tsohon soja kamar Dadansu.
      Karo na farko a rayuwarta data zuba masa idanunta. Kallo sosai take masa irin na ƙurulla fiye da ko yaushe. Badan kar ace tayi ƙarya ba data rantse Dadah yafi kowa ƙyau a gidan. Musamman a yanzu daya ajiye gashin saje a fuska. Gashin kuma ya gauraya da tsilli-tsillin farin gashi da yay matuƙar ƙara masa kamala da cikar haiba masu irin shekarunsa da nutsuwa ta gama ratsawa da kwarjini na musamman. Tabbas kalmar Dattijo kalma ce mai daraja da malam bahaushe kan faɗa ga mutanen da shekaru suka fara matsawa a sahun ƙuruciya. Bata taɓa ƙara jin girma da darajar wannan kalmarba irin yanzu data gama sanin ai nahin HAYSAM ABDUL-RASHEED SHEHU. Domin kuwa duk namiji daya fara shiga shekarun dattijan taka da suka fara ne daga 45 zakaga al'amuransa sun dai-daita nutsuwarsa da kamewa sun yalwata. Sai dai in har asharari ne a shekarun samartakar sa..
Dadan su kuma kamili ne mai addini kowa ya sani....
        Motsin da yay da hannunsa ya saka tunaninta yankewa. Tai saurin ƙoƙarin sake matsawa tana kallonsa. Sai kuma akai sa'a ma bai ko buɗe idanunsa ba ya cigaba da barcin. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, sannan ta zuba tagumi tunaninta ya koma kan wayarta da Dagger....

          [=][=][=][=][=]
Chapter 95 · 0% Book details