Sashe 80
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
.........Ruƙayya na cikin damuwa sosai tun wayar da sukai da Nimrah. Taso sanarma Ammar, amma sai saƙon Nimrah ya katse hanzarin ta. Dan ta turo mata cewar dan ALLAH sirri ne karta gayama kowa. Hakan yasata dole haɗiyewa. Sai dai damuwa ta kasa barinta. Gashi tana jin nauyin kiran layin kada Dadah ya ɗaga. Ta roƙi Ammar ya kira mata Dadah su gaisa da Nimrah yaƙi.
Acewarsa yana jin kunyar Dadah, dan tunda har bai kira su ba tunda yay wannan tafiyar ya tabbatar akwai dalili. Dole ta haƙura, amma damuwar ta kasa barinta. Tun tana ƙoƙarin dannewa har Ammar ya ganota. Tambayar duniya tace masa ba komai. Shi kuma bai kawo wani matsala bane sai yake tunanin kewar Nimrah ɗin ce ke damunta. Dan haka ya ta bata damar dinga zuwa sashen Mammah dan shima sun koma aiki shi da Bilal a yau.
Hakan ya mata daɗi, dan koba komai ta rage nauyin zuciyarta. Sannan zata huta da fitinar Uncle ɗin kwana biyun nan. Cike da zumuɗi yana fita itama tai gyara ta shirya sai sashen Mammah. Acan ta samu su Ammy. Babu jimawa sai ga Asma'u ma. Nan fa hira ta ɓarke, ɗaya biyu zakiji sunan Biebah da Nimrah ciki, alamar suna kewar su, abinka da dama jini ɗaya. ALLAH kuma ya haɗa a gida ɗaya. Idan ka gansu da Mammah abin sha'awa. Dan tamkar ƴaƴan data haifa ne ba surukai ba. Bare ma Ruƙayya da dama rainonta ce.
A tare sukai girkin rana. Bayan sun kammala kowacce ta koma sashenta yin salla. Dan suna son zuwa gidan Biebah. Da farko banda su Asma'u. Sai da Ruky ta dage da shagwaɓa harda kuka sannan Mammah tace su gayawa mazajen su. Sun san bazasu yarda ba, dan fitar su tayi wuri yanzu. Sati ɗaya kenan fa kacal. Dan haka Ruky ta sake lallaɓa Gwaggo Khadijah ta shiga maganar. Daga ƙarshe ma ita ta kira Bilal da Ammar da kanta. Ba zasu iya jayayya da Gwaggon tasu ba, dan haka babu wanda ya musa sukace to. Da wannan farin cikin sukai girkin.
Kowacce tsaff ta dawo cikin kwalliya. Har Gwaggo Khadijah ma na tsokanar su. A tare sukai dariya. Mammah na tayasu da murmurshi. Sai da sukaci abincin da suka girka sannan sukai ma su Mammah sallama suka wuce. Asma'u da Ruƙayya ɗauke da su Naseer.
Lailah taja motar, Ruƙayya a gefenta. Asma'u da Shariffa a baya. Da sauri Malam Alamu ya miƙe ya wangale musu gate. Sanda da Malam Buba dake zaune suka ɗaga musu hannu. Haka kawai wani abu yaso ɗan haskowa a zuciyar Ruƙayya game da malam Buba. Sai kuma dai bata bari abin yayi tasiri ba ta watsar saboda farin cikin ganin Small Mom dake ɗawainiya da ita yanzu. Sai da suka tsaya wani babban mall sukai shopping sannan suka ɗauki hanyar gidan Biebah, duk da ba wani nisa bane sosai amma dai akwai ƴar tafiya.
Lokacin da suke isowa gate ɗin ji Ruƙayya take kamar ta fita ta shiga da ƙafa. Tadai daure har aka buɗe musu suka shige.....
(@@@@).(@@@@)
Tun bayan wucewar Daddy Imran ya koma ɗakin. Kamar yanda yay hasashe ruwan ya ƙare. Cire mata yayi, ganin tana zufa alamar zazzaɓin ya sauka ya janye mata bargon shima. Barci take sosai. Kuma da alama yana mata daɗi. Suma windows ɗin buɗe mata su yayi. Iska mai daɗi ta tekun ta fara rige-rigen shigowa ɗakin.
Falo ya dawo ya zauna. Dan yana son yay kiran Nabeeha sannan ya taɓa aiki. Kiran Nabeehan ya fara yi, wadda suka ɗan jima suna hira. Dan yau da arziƙi nasihar Jiddah ta jiya bata gama sakinta ba. Ta daure sosai ko sau ɗaya bata kawo masa batun Nimrah ba. Hakan sai yay masa daɗi, a ransa yana addu'ar ALLAH ya sa ta ɗore. Magiya ta shiga masa akan yaushe zai dawo. Dan ita dai haƙurinta ya fara zuwa ƙarshe a kewarsa.
Kasancewar zuwa yanzu abubuwa data haddasa masa na ɓacin rai sun fara ɗan sassautawa saboda ƙudirtar yafe mata da yayi sai ya hau lallashinta. Tare da tabbatar mata nan da sati ɗaya in sha ALLAHU yana a gabanta. Sosai taji daɗin albishir ɗin nasa. Duk da satin gudan ji take ya mata nisa da yawa. Amma dai zata jure.
Bayan sunyi sallama tai shiru cike da nazari. Maganganun Jiddah na dawo mata. Tabbas ta yarda in har zata rage wasu abubuwan zata cigaba da samun Haysam. Ita matsalar gaskiya tayi masifar tsanar yarinyar nan ne. Da ace Haysam zai yarda ya canja mata gida ace bata ganinta, bata kuma ganin waɗan nan ƴan uwan nasa daba sonta suke zata rage jin hakan. Amma zama dasu shine babbar matsalar. Dan magana ta ALLAH bata ƙaunar mutanen nan sam..
Ƙaramin tsaki taja da miƙewa. Tana son fita ne ta ɗan sha iska, dan haka ta nufi bayi dan yin wanka..
......★★★......
Anan kam Nimrah ce ta farka. Sosai taji jikinta ya mata daɗin. Duk ciwon nan da yake da nauyin da yay mata sun saki. Sannan can ɗin ma ta rage jin zafin. Bata damu da rashin ganin Dadah a ɗakin ba. Sai ma daɗi da taji. Ta lallaɓa ta gyara gadon saboda jikinta da take jin babu ƙarfi.
Madaidaicin bayin ta shiga tayi wanka tare da ƙara shiga ruwan zafi. Sai da taji ta ƙara samun nutsuwa sannan ta fito. Mai ta fara shafawa, sannan ta mulke jikinta da turarrukanta masu ƙamshi na musamman. Inda taga yana ɗakko kaya ta duba. Sai ta samu harda kayan mata. Sai dai duk ƙananu ne sosai dan babu wani na arziƙi a ciki sai rigar da tazo da ita a jikinta jiya. Tana jin matuƙar kunyar sakawa. Amma babu yanda zatayi tunda ba wasu ne da ita ba. Sannan yunwa take ji, burinta kawai ta fita ta samu abinci taci.
Wani ɗan mini skirt ta sanya da ƙaramar top mai guntun hannu. Kayan sun mata ɗas a jiki. Ta gyara gashinta sama-sama tana ɓata fuska dan bata ƙaunar abinda zai taɓa mata kai. Koda ta ɗaure sai ta sake ɗaukar turarensa ta ƙara. Sannan ta saka bedroom slippers ta fito a ɗarare.
Dadah na zaune a falon kansa duƙe ya duƙufa aiki ƙamshinta ya fara masa sallama. A hankali ya ɗago kansa ya zubama ƙofar. Dai-dai tana kawar da kai daga kallonsa.
“Kin tashi?”.
Ya faɗa a cikin maƙoshi idanunsa na yawo a kanta. Kanta ta jinjina masa batare data sake yarda ta kallesa ba. Shima nashi idanun ya kawar. Aikinsa ya cigaba da yi sannan yace, “Ƙaraso mana”.
Kamar wadda aka makema ƙafafu da ƙyar ta dinga ɗaga su tana nufar inda yake. Sai da taje gab ta risina tana gaishe shi. Maimakon amsawa sai ya kamota ya zaunar kusa da shi. Hannunsa ya saka a wuyanta, sai kuma ya maida goshinta.
“Zazzaɓi ya tafi?”.
Kai ta jinjina masa.
“City ɗin fa?”.
Cikin rashin fahimta ta ɗago idannunta da har yanzu basu gama bajewa daga kukan data sha ba ta kallesa. Sai dai da sauri ta kawar ganin nasa dake narke a kanta. Ya gane bata fahimta ba, dan haka shima sai ya basar.
“Mi kike son ci?”.
“Abu mai yaji. Baki na babu daɗi”.
Ta faɗa a hankali idonta na tara ƙwalla.
“To shagwaɓatu basai kin yi kuka ba ai. Zaki ci gasashen kifi?”.
“Uhmm”.
Bai sake cewa komai ba ya ɗauka waya yay kira. Babu jimawa kuwa sai ga wata baturiyar mata ta shigo ɗauke da kyakkyawan basket. Sai yanzu Nimrah ta fahimci basu kaɗai bane a cikin jirgin kenan. Dan dama tun jiya tana ta son tambayarsa wanda ya haɗa musu dinner. Bayan matar ta gaishe su ta shirya abincin a table ɗin dake gabansu ta fice abinta. Sai lokacin Dadah ya ajiye system ɗinsa.
Da kansa ya ɗauki lemon tsamin dake gefen plate ɗin kifin ya matsa a kansa. Sannan ya ɗauka spoon ya ɗebo yana juyowa gareta
“Open”.
Ya faɗa a hankali.
Itama a hankali ta motsa lips ɗin nata ta buɗe ya saka mata kifin a baki. Sai ta shiga taunawa sannu-sannu kamar bata so. Shi ko ya zubama lips ɗin nata idanunsa da take jin kaifinsu sosai.
“Dadah yaushe zamu tafi gida? ALLAH ina jin kewar Mammah”.
“Zamu koma, amma sai kin amsar musu tsaraba”.
“A wajen wa?”.
Kansa ya nuna mata.
Tai ɗanyi tsai tana kallonsa. Sai kuma ta kawar da idanun. Kai tsaye tace, “Ba sai muje ka saya ba”.
“Ita wannan tsarabar babu kuɗin dake sayenta ai”.
Yanzun kam mamakinta a bayyane yake. Ta ce, “Saboda mi?”.
Shiru kamar bazai amsa ba. Sai zuwa can ya ɗan ja mata hanci.
“Saboda wanda ke bayarwa yafi ƙarfin a biya shi”.
Baki ta tura da faɗin, “ALLAH Dadah wani lokacin sai kaita rikitani. Idan kai magana ba komai nake ganewa ba”.
Murmushi yayi, bai sake cewa komai ba ya cigaba da bata kifin. Sai da tace ta ƙoshi sannan ya barta. A marairaice ta ce, “Kaifa?”.
“Kallon Little Tiger ta ƙosar da ni tuni”.
Murmurshi tayi da saka hannu ta rufe fuskarta tana faɗin,
“Ni dai ba ruwana ALLAH”.
Dadah yay murmushi kawai yana sake ɗaukar laptop ɗin sa batare da yace komai ba..........✍️
96