← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 113

Sashe 48

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........Zuwa magriba gaba ɗaya baƙin dake ɗan ɗeba mata kewa suka wuce. Dama dauriya kawai take dan wani zazzaɓi take ji tun safe. Da farko Faro na gidan, sai da akai azhar ya fita. Shi ne bai dawo ba har yanzu. Cikin dauriya da jarumtar dole ta shiga gyara gidan, duk da ba wani an ɓata bane da yawa. Ɗan wanke-wanken da aka tara ma su Sumayya da suka kawo abincin rana sunyi shi. Gidan ma sun gyara an sake ɓatawa ne. Kuma yanayinsa bai mata yanda take so ba.
         Sai da ta tabbatar ko ina ya ɗauki irin ƙamshin da take buƙata sannan ta shiga wanka. Ta gyara jikinta sosai da ƙara shiga ruwan zafi sannan tai alwala ta fito. Tana shiri tana tunanin su Aunty Ummi da suka ce mata zasu zo amma shiru kake ji. Koda yake dama sun raba cewar yau ko gobe. Tai ƙaramin tsaki dan wani irin kewa ke damunta na ƴan uwan nata. Musamman ma Ruƙayya da Nimrah da Mu'azz. Gashi ta kira wayar Rukyn da Nimrah amma duk basu je ba da safe. Da rana kuma baƙi sun ɗauki hankalinta sosai. Garama Mu'azz da la'asar ya kirata yace sai weekend zasu zo da su Imam yau sun shiga makaranta ne.
         Ajiye tunanin tai gefe ta gabatar da sallar magriba da aka kira. Sai da ta idar ne ta hau kiran layin Ruƙayya. Akashe kamar ɗazun dai. Mamaki ya kamata ta koma kan Nimrah. Ita kuma taƙi shiga alamar matsalar network. Ta sauke wayar tana yamutse fuska aka taɓa ƙofa. Ɗagowa tai ta kalla wajen, dai-dai shigowar Faro da sallama a bakinsa. Amsawa tai tana duƙar da kanta dan idanunsa a kanta suke ƙyam.
        “Sannu da zuwa Yaya”.
     “Yauwa Ma'am”.
  Ya faɗa yana kaiwa zaune. Cikin wasa ta ɗan ɓata fuska da faɗin, “Kai Yaya Ma'am kuma?”.
        “Eh mana, nima bakin ƙi daina kirana da Yaya ba. Nima daga yanzu Ma'am zan dinga kiranki”.
     “Hu'um ashe zan kai ƙara ma Dadah”.
     Yalwatacciyar dariya ya saki, tare da baro inda yake zaune ya dawo kusa da ita ya zauna. Kamota yay zai saka a jikinsa yaji zafi. Tuni ya haɗiye abinda yay niyyar faɗa ya ce, “Ya Salam Biebalo jikinki zafi fa! Miya faru?”.
          “Ba komai”.
      “Ina fa ba komai”.
   Ya faɗa yana cire hijjab ɗin jikin nata gaba ɗaya. Tattaɓata ya shiga yi tako ina. Ita harma yaso bata dariya. Zatai magana ya dakatar da ita da faɗin, “Maza tashi asibiti zamuje”.
      “Ni dai Yaya a'a zan sha pracitemol kawai it's okay”.
   “No! Ban yarda ba. Oya tashi muje”.
  Ba yanda ta iya haka ya ɗagata tsaye. Ya ɗauki hijjab ɗinta ya mayar mata jikinta. Hannunta ya kama suka fice. Yana nufar inda motarsa take yake ma maigadi nunin ya buɗe gate. Da sauri kuwa ya miƙe, shi kuma ya buɗe ma Biebah motar ya taimaka mata ta shiga sannan ya zagaya side ɗin driver yay ma motar key suka fice, maigadin su na musu fatan dawowa lafiya, a ransa kuwa yana gulma wai amaren yanzu dai sai a hankali. Kwana ɗaya basa jin komai sai kaga sun fara fita....

        😂To kai ina ruwan ka? Gulma wuya.

     %}}}}}}}}%{{{{{{{%

     3:pm iirgin ya sauka a hankali a cikin hasken dare na Dubai. Fitilu na walƙiya kamar taurari a ƙasa. Nimrah na kallon window, idanunta a buɗe sosai. Zuciyarta na bugawa da ayyana (Wannan ce Dubai…?)
       Numfashin Dadah ya sauka a hankali shima alamar yana ambaton ALLAH a zuciya. Suna haɗa ido da Nimrah tai saurin kauda nata. Shima komai baice mata ba ya kauda nashin. A kusan tare suka miƙe, tana riƙe da ƙaramar handbag ɗinta da waya ce kawai a ciki, zai ɗauki laptop bag ɗinsa shima tai saurin ɗauka. Tsayawa yayi yana kallonta. Yayinda a yanzun ma ita taƙi kallonsa. Baice komai ba ya fara tafiya tabi bayansa.
        A hankali Kofar jirgin ta buɗe. Iskar dare mai sanyi ta bugi fuskokin su. Guard ɗin da suke tare suna jera suka sake gyara tsaiwa cikin tsari da nutsuwa.
      Dadah na ajiye ƙafarsa a tare suka furta, “Good evening, sir.”
   Dadah ya jinjina musu kai tare da ɗaga hannunsa kawai. Cikin takunsa na ƙasaita yay ƙoƙarin wuce su. Nimrah dake biye a bayansa suka shiga gaisarwa. Itama kanta ta jinjina musu tana jin kamar ba ita ba. Wani daga cikin su ya matsa zai amshi bags ɗin hannun nata ta girgiza kai. A karo na farko ya furta, “No. Thank you”.
         Kansa ya jinjina cike da girmamawa. Wanda ya matsa kusa da Dadah kuma ya furta, “Welcome, sir. Your car is ready.” yay maganar yana nuna musu haɗaɗɗun jibga-jibgan motoci guda uku dake can gefen runway sai sheƙi suke da ɗaukar idanun mai kallo. Rolls-Royce Phantom nasu, sai black SUVs securitys ɗin su.
        Da sauri Driver dake cikin suit shima ya buɗe musu ƙofa da faɗin, “Welcome. Sir”.
      Dadah ya ɗan juya ga Nimrah. A kan laɓɓa ya furta “Shiga.”
   Ba tare da ta ce komai ba ta shiga. Har yanzu fuskarta na nuna dai fushi ake da Dadah. Shi kuma ya basar kamar bai lura ba. Amma a ransa dariya take bashi sosai. Motar ta fara tafiya cikin nutsuwa. Dubai na walƙiya a idanun Nimrah. Gine-gine masu tsayi. Haske mai burgewa daya sakata sake tsarkake sunan UBANGIJI mamallakin duniya da abinda ke cikinta. Gaba ɗaya ma sai taji ta manta da fushinta na ɗan lokaci. Bata ko cuci kanta ba idanunta na zagaya komai. Faɗi take a zuciya (Subhanallah… wannan duniya ce fa kenan, inaga aljanna. Ya rabbi ka bamu aljanna, ya rabbi ka cece mu kasa ko ganin wuta bazamuyi ba). Ta sauke wani nannauyan numfashi tana haɗe hannayenta waje guda.
        Duk abinda take Dadah na lure da ita. Sai dai bai ce komai ba, hasalima ya basar tare da kwanciya a kujera kai kace idanunsa a rufe suke. Sai dai ta ƙasan ido yake ƙare mata kallo tsaff.
      A nutse Motar ta tsaya a gaban Burj Al-Arab. Ginin ya wani kalar haskakawa tamkar wata ginanniyar masarauta. A hankali ƙofar ta buɗe. Staff uku sun jera alamar jiran isowarsu suke. Dan a tare suka furta,
        “Welcome, sir. Welcome Maa”
    Ko jinsu Nimrah data sauka ta tsaya cak bata yi. Dan Idanunta sai uban kai kawo suke kamar zasu faɗo saboda kallo. (Wannan hotel ne… ko aljanna? Kai jama'a Ruky na tayaki takaici wlhy).
        Wata staff mace ta matsa kusa da ita, cikin katse mata tunani ta sake furta. “Welcome, ma’am.” tana yi mata murmushi. Kai ta jinjina mata kawai da takaicin katse mata jin daɗin kallon ta. Dai-dai nan ya iso inda taken, batare da yayi magana ba ya kama hannunta. Dole ta fara takawa suka nufi ciki. Komai zinariya ne a wajen nan, ƙamshi mai laushi, haske mai sanyaya zuciya. Da sauri nan ma wani manager ya zo da kansa.
     Bayan gaisuwa da girmamawa ya cigaba da faɗin, “Your suite is ready, sir.” daga haka yay gaba suka bi bayansa zuwa lift. Suna shiga Dadah ya saki hannun Nimrah ya tsaya daga bayanta hannayensa a aljihu. Tafiyar sakanni suka iso. Lift ta buɗe. Anan ma abin kallo kaca-kaca har Nimrah tama rasa wanne zatayi.
        Manager ya tsaya a daidai ƙofar suite dazai kasance nasu. Ya danna wani abu ta buɗe a hankali. Daga haka yay musu sallama ya juya. Dadah ya fara shiga. Nimrah data biyo baya ta tsaya cak numfashinta yana ɗaukewa. A kan lips ta furta “Ya subahanallah”. Babban ɗaki ne sosai. Ga wani sirrintaccen haske mai ƙawata ruhi da kwaranye baƙin ciki. Wani gado kamar na sarauta a gefe yaji shimfiɗu na alfarma. Window mai kallon Dubai gaba ɗaya. Tuni ta manta da wani batun fushi. Ta ɗan taka gaban ƙaton glass ɗin bango guda a hankali. (Oh ni Ninrah. Ni ce a nan yau…?)  Kasa haƙuri tai ta juyo inda Dadah yake. Idanunta suka sauka a kansa. Shi kam har yanzu yana tsaye a ƙofar kawai yana kallonta. Ta wani waro masa idanunta da watsa hannaye ta ce,
         “Woow Dadah. Wlhy Dubai ta haɗu”.
      Murmushi ya ɗan yi kawai da kauda idanunsa a kanta cike da wani salon basarwa irin na manya. Bata damu ba dan tasan murmushinsa shine amsar ta. Gaban gadon ta matsa shima ta tattaɓa. Sai kuma ta wani juya ya faɗa a kansa. Ai ko gaba ɗayanta ta wani nutse a ciki. Tako ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Wayyo duniya ina sonki zan barki. Ya ALLAH kasa mu ƴan aljanna ne”.
           Dadah dake jinta ya girgiza kai kawai yana ƙarasa takowa da cire agogonsa. Ta gabanta ya gitta zuwa bed side drawer ɗin ya ajiye agogon. Baiyi magana ba ya nufi hanyar ƙofar da yake ƙyautata zaton bayi ne. Hajjaju Nimrah bata ma san abinda yake ba. Sai faman juye-juye take a gado ranta fes. Sai ko barci ɓarawo ya samu nasarar kwasheta dan dama wanda tai a jirgi bawai ya mata daɗi bane. Yanzu ko ga gado ta samu.
      Sosai mamaki ya kama Dadah daya fito ganin wai har tayi barci. Kai ƙuruciya daban ce. Matsawa yay kawai gaban gadon ya gyara mata kwanciya tare da jan lallausan blanket ɗin gadon ya rufeta. Gaban gadon ya bari zuwa inda laptop bag ɗinsa yake. Ya buɗeta ya ciro wani ɗan abu kamar irin wayar jami'an tsaron nan. Sai dai da alama ba wayar bace wani abu ne daban. Dan kunna shi yay ya ajiye a saman table ɗin dake rukunin kujerun dake gefe. Sannan ya ɗauka laptop. Sai da ya tabbatar da abinda yake neman babu wato camera a ɗakin sannan ya kashe komai ya ajiye..........✍️64
Chapter 48 · 0% Book details