← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 113

Sashe 91

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Koda Nimrah ta dawo sashenta saboda korosu da Gwaggo Khadijah tayi bayan wucewar su Aunty Mommy wanka ta fara yi. Tasan har yanzu Dadah baya gida, dan in ya dawo bazai taɓa wutowa bai shiga gun su Mammah ba. Wanka tayi ta gyara jikinta. Duk da Magriba tayi tsaff ta shirya kanta cikin skirt da riga na lass. Dama indai kwalliya ce da iyayi a bar musu kayansu ita da Ruƙayya. Uban turaren data zuba a jikinta ga kabbasa har ji take yana hawa mata kai. Sashen nata ma ta sake saka turare kai kace yau ɗin itace da Dadahn. Wannan duk yana a cikin sabon karatun su Lailah. Sun tabbatar mata ba sai ranar girkinta zatace zatai abinda ya dace ga miji ba. Ita mace mai abokiyar zama tanayi abinda zai saka oga jin ƙaguwa dawowa wajenta a duk randa yake ba nata ba. Da wannan tunanin ta kammala saka kamshi ta koma bedroom tai sallar isha'i da aka kira, bayan ta idar karo na farko ta shiga kitchen ɗinta da nufin dafa wani abu, sai da ta gama ƙare masa kallo har store duk da ɗazu ko ina sun shiga da su Small Mom. Madara ta ɗakko da kayan tea ta kawo kitchen, komai ta zuba shi inda ya dace sannan ta ɗibo madara da yawa ta saka mata ruwa. Bata damu da yanda tai kauri ba dan yawunta har tsinkewa yake ta ɗakko biscuit ta fito. A kayan abinci da su Ja'afar suka kawo sashen nata daga ita har Ruky harda kayan kwalam aka haɗa musu saboda sanin halinsu....

    .....★ A dai-dai wannan lokacin motar Daddy Imran daya maido Dadah gida ke tsayawa ƙofar sashen. Daga gidan Uncle Nasiru suke, bayan sun bar gidan Baffa can suka je. Sai da sukai sallar magriba da isha'i suka baro. Dadah dake kwance jikin sit idanunsa a lumshe ya buɗesu a hankali. Idanun sunyi ja kaɗan, sannan jijiyar kansa ya ɗan fito.
      Cikin kasa haƙuri Imran ya ce, “Zak.. kamar baka da lafiya fa?”.
Ƙaramin tsaki Dadah yayi, ya ɗan furzar da huci yana mirza goshinsa kaɗan. “Kaina ke ciwo. Kwana biyu kenan na rasa mi yasa. Da ance maka yamma tayi sai naji yanayina na sauyawa kamar zanyi zazzaɓi, sai dai ƙarshe ciwon kai yake komawa”.
        “Kaje asibiti?”.
    “No. Ba wani serious bane bafa”.
“Babu ciwon daba serious ba. Musamman ma kai da har yanzu kake kan shan magani. Bari kawai mu juya asibiti”.
        “Bari dai mu gani kwana biyu in bai daina ba. Ya kamata kaje gida kaima ka huta.”
      “Shike nan, amma dan ALLAH kasha magani idan ka shiga. Maganar haɗuwa da Janar ma anjima kawai ka barta, zan masa bayani. Su Faro ma yau suke shirin kama Ojo”.
          “Good. Bazai yiwu ba Imran, dole mu gansa muma yau. Kasan bamu da wani isashen lokaci kasancewar mun rikita duniyar mutanen nan, yanzu kowane irin lissafi yazo musu yi zasuyi. Babban fatanmu dai Faro su kama Ojo ɗin”.
       “Haka ne, amma ai lafiya tafi komai.”
      “Karka damu zan iya. Dan ina son shiga UNIT ZERO ma da gobe in sha ALLAHU. Ya kamata nayi magana ta farko da tsohon driver ɗin nan. Idan Madam ta barka ka fito mu haɗu”.
     “Oh idan ma ta barni ne ko?”.
Murmurshi Dadah yayi batare da yace komai ba ya buɗe motar ya fice. “Ka isa gida cikin amincin UBANGIJI”. Ya faɗa yana rufe masa motar kawai. Murmurshi Imran yayi shima ya tada motar ya fice.
      Sai da Dadah ya fara shiga sashen Mammah. Bai jima ba ya fito dan ya samu tana waya da Ummu matar Uncle Nasiru. Yasan kuma wayarsu bamai ƙarewa bace cikin sauƙi. Gara yaje idan yayi wanka ya dawo, dan shima baya son katse su ma...

       Kamar ko yaushe babban falon a gyare, sannan Rayhana mayyayatu na zaune, sai Amimah tsaye da waya a hannu tana miƙa mata. Da alama Amima zuwa falon tayi kawo wayar. Kusan tare sukai masa sannu da zuwa. Sai dai Rayhana an wani kashe murya.
     Amsa musu yayi yana wucewarsa kai tsaye sashen Nimrah. Ba Rayhana ba hatta Amimah sai da ɓata fuska. Dan ita fa kishin take taya Nabeeha da gaske. Aiko tana ganin Dadahn ya shige fuuu ta tafi sashen su kaima Nabeeha rahoto...

    ....Buɗe ƙofar da ƙamshin turarensa ya saka Nimrah da idonta ke kan television tana kallo da shan biscuit ɗinta da take sakawa cikin madara ta juyi da sauri. Ido suka haɗa da Dadah dake maida ƙofar ya rufe. Kyakkyawan murmushi ta sakar masa, tare da ajiye kofin ta taso inda yake. Harta iso idanunsa a kanta. Kanta tsaye jikinsa ta shige. Cikin ƙanƙamesa ta ce, “I miss you Mijin Naja'atu Nimrah”.
      Murmurshin da bai shirya ba ya saki. Ya sauke nashi hannun ɗaya a bayanta yana ɗan bubbugawa na lallashi. Kafin cikin ƙaramin sauti ya furta, “Kin tabbatar?”.
     Kai ta jinjina masa batare data ɗago ba.
        “Uhmm to mi Mijin Naja'atu Nimrah zai samu?”.
      Bai ma gama rufe baki ba ta ɗago tare da yin ɗiɗɗishe ta sumbaci gefen wuyansa. Lipstick ɗin data ƙawata bakinta da shi ya manne batare da Dadah ya sani ba. Sai kuma da sauri ta sake mayar da kanta ta ɓoye a jikinsa tare da sake rungume shi tana murmurshi.
       Saitin kunnen ya duƙo ya raɗa mata. “Mijin Naja'atu Nimrah na godiya, sai dai wannan ya yi masa kaɗan”. Yay maganar da ɗago fuskarta ya nuna mata lips ɗinsa. Murmurshi tayi, sannan ta matsar da fuskartata gab da tashi har kowa na jin saukar numfashin ɗan uwansa. Yanda ta matso da lips ɗin ta gab da nashi yasa shi lumshe ido yana jiran saukar nata. Ganin ya sakankance kawai ta kwace jikinta ta bar wajen tana masa dariyar ƙeta.
         Lips ɗin ya cije a hankali yana buɗe idanunsa ya bita da kallo. Sai kuma ya miƙe cike da basarwa ya koma kan ƙafafunsa ya tsaya da ƙyau. A lokacin Nimrah ke dawowa da ruwa mara sanyi da glass cup data ɗoro akan ƙaramin tray mai ƙyau. Har yanzu fuskarta da murmushi ta ce, “Dadah ga ruwa.”
       “Sha abinki na ƙoshi”.
    Ya faɗa kamar irin yayi fushin nan. Nimrah data yarda fushin yayi ta ajiye tray ɗin tana dawowa inda yake. Hannunsa ta kama cike da shagwaɓa tana diddira ƙafa ta ce, “Yi haƙuri na tuba. Naji zan maka idan kasha”.
      “Ni zakima wayo?”.
   “ALLAH Dadah da gaske.”
Idan ya biye mata yasan zata iya tada rikici. Dan hakan ya fara takawa kawai zuwa kujerar data ajiye ruwan. Zaune ya kai, ita kuma ta zuba a kofin ta miƙa masa.
       “Thanks”.
    Ya faɗa yana kai kofin bakinsa. Ita kuma ta ɗan zubama kansa idanunta. A bazata yaji saukar yatsarta a saman kansa.
          “Dadah kanka na maka ciwo ko?”.
    (Yarinyar nan wayonta yayi yawa) Ya faɗa a zuciyarsa yana kallonta. Kafin ma yace wani abu ta miƙe tana sake faɗin, “Dan ALLAH Dadah jirani ina zuwa”. Ta shige bedroom. Babu jimawa sai gata ta fito da ɗan ƙaramin towel a hannu. Ta bayansa taje yanzu ta tsaya. Kan nasa ta kama ta kwanto jikin kujerar sosai, hakan ya sashi ɗaga idanun sa ya kalleta. Dai-dai tana sauke towel ɗin hannunta dake a jiƙe saman goshinsa. Sanyin ya ratsa shi. Har sai da yaja ɓoyayyar ajiyar zuciya. A zahiri kuma ya yamutsa fuska kaɗan.
        “Sorry Baby na kada kayi kuka”.
    Ta faɗa cikin kunensa da raɗa. Tana gama faɗa kuma ta saka tafin hannunta ta rufe masa idanu tana ƴar dariya. Sai kuma a bazata yaji saukar ƙananun lips ɗinta kan nashi. Kaɗan tayi ta janye tana zamewa bayan kujerar.
     Rasama abin yi Dadah yay. Dan gaba ɗaya ta gama tsinka masa jini. Dole ya miƙe a hankali yana cire towel ɗin data saka masa ya juya shi, yana dafe da shi a goshin nasa ya zagayo inda take a bayan kujerar. Kanta tai saurin cusawa a tsakanin ƙafafu.
       “Dadah kada kayi magana dan ALLAH sai da safe”.
     Ya tabbatar yarinyar nan sai ta saka shi sakin layuka a bainar nasi watarana. Baiyi maganar ba kamar yanda ta roƙa, ya cire towel ɗin kawai ya kama hannunta ɗaya ya sanya mata a ciki. Sai kuma ya kamo ɗaya ya sumbaci tsakiyarsa kawai ya juya ya fice a binsa yana murmurshi..........✍️
107

........Yana shigowa sashensa da fuskar Nabeeha da ke zaune tana lissafin mintuna ta cika fam ya fara cin karo. Shi abin ma sai yaso bashi dariya. Bai dai yi ba, sai ma a ransa ayyanawa yake (Dole maza masu mata da yawa su samu hawan jin.....)
    Tunanin nasa ya yanke, sakamakon isowar Nabeeha inda yake. Da farko kamar zata rungumesa sai kuma ta tsaya cak. Yanda ta buɗe hanci tana shinshinarsa kamar wata mage dake son gano inda kifi yake yasa shi fahimtar ta. Sai dai kafin ma yay magana idonta ya ciko da ƙwalla. “Amma kana ganin hakan adalci ne? Ni ce da kai kaje kana kasancewa da wata?”.
          Shi dai kallonta kawai yake, sai kuma ya kawar da kansa yana kallon agogon hannunsa. Kafin ya sake maido idanun nasa kanta. Sai kuma ya ɗan duƙo kansa saitin kunnenta. “Ita wadda ta kawo miki gulmar bata haɗa miki da lokacin shigowata bane?”.
     Cike da takaici ta ce, “Koma dai miye ai sai ka dinga jin tsoron ALLAH. Kun je kunyi sati biyu bance komai ba. Kun dawo ɗin ma nawa lokacin da ita zaka raba”.
     Fuuu tai shirin barin wajen. Hannunta ya riƙo ya maido ta gabansa. Batare da yayi magana ba kawai ya rungumeta. Zazzamewa ta shiga yi da sake faɗin, “Ni sake ni. Kaje ka gama rungume wata banza zaka zo ka samin wannan ƙazamin turaren nata a jiki.”
        Sakin nata kuwa yayi, bai kuma sake cewa komai ba ya raɓata zai wuce. Karaf kuwa sai idonta akan wuyansa dake zane da shatin lips ɗin janbakin Nimrah. Saukar hannunta kawai yaji akan wuyan nashi, ta shafo jambakin tana nuna masa. Da rawar murya ta ce, “Oh har saƙo ta baka kazo min da shi?”.
        Dadah ya kai hannunsa saman goshi ya murza da ƙarfi. Shi bai san tsakanin Nimrah da Nabeeha ɗin ma wake son maida shi mahaukaci ba kam. Rashin abin faɗa ya sashi zagayeta kawai ya cigaba da tafiyar sa.....
Chapter 91 · 0% Book details