Sashe 72
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..........“ALLAH sarki Dadah, kana cikin wannan halin amma babu wanda ya sani, sannan ka yarda ka cutu domin tausayinmu, tabbas namijin gaske shike zama mai tausayi gana ƙasa da shi sannan mai adalci ga abokin rayuwa”. Ta faɗa tana share hawayenta da kunna voice ɗin doctor. Amsar da Doctor ɗin ya bashi ya sake karya mata zuciya. Tausayin Dadah ya sake tasiri da faɗi a ruhinta.
“Gaskiya akwai haɗari a cikin hakan, dole sai ka fitar da fushinta a ranka, dan babu fushin ma haɗari ne babba inaga kana ciki... Amma ina ganin dabara ɗaya muke da ita anan. Second wife ɗinka komai a gareta yanzu a hankali yake farawa, ina ganin idan ka fara da ita cikin kulawa da natsuwa zai fi zama dai-dai to koba komai akwai tausayin kasancewar ta na farko. Amma fa dolene itama ka ɗauki komai a hankali. Kada ka gaggauta ko matsawa. Komai ya kasance a sannu-sannu, bayan zuwan farko ka ba jikinka lokaci ya gama farfaɗowa. Idan kana bukatar kusanci da ita ya zama cikin kulawa sosai, ba tare da wuce gona da iri ba. Zan haɗa maka wasu magunguna da zasu taimaka wajen daidaita yanayin jikinka da hanaka tsanantawa a lokacin da zaka kasance da ita. Amma har yanzu babban maganin shine haƙuri da kuma control. Bayan kasancewar farko ka sake bawa jikinka lokaci kafin wani kusanci na gaba kamar yanda na faɗa a baya. Amma sai ka yi haƙuri, dan zaka shiga matsi sosai a lokacin fiye da na shekarun da kayi a hakan sakamakon an ɗanɗanama jikin abinda ya jima yana buƙata. Idan ka iya hakan zai taimaketa ba zata jigata ba da zai kai ga cutuwa.”
“Shike nan Doctor. Zan yi ƙoƙari. Duk da nasan ba abune mai sauƙi a gareni, amma bazan so ta cutun nan ba ko kaɗan saboda........”
Bama takai ƙarshen bayanin Dadan ba ta fito kawai ta shiga kiran layin Ruƙayya, dan tana buƙatar shawara. Kuma bata san wa zata iya tunkara da wannan maganar ba sai Ruƙayyan kawai.
Cikin sa'a kuwa ta shiga. Sai da ta kusa tsinkewa aka ɗaga. Nimrah ta sauke ajiyar zuciya, sai dai jin muryar Ruky a sanyaye kamar wadda taci kuka ya saka gabanta faɗuwa..
“Ruky!”.
Ruƙayya da muryar Nimrah ta daketa a bazata ta ce, “Ninah kece? ALLAH na zata Dadah ne”.
“Ya ara mun ne. Baki da lafiya ne?”.
Cikin tura baki Ruky ta ce, “Mi kika ji?”.
Muryarki kamar wadda tai kuka. Ruky ta harari hanyar bayi da Ammar ke ciki. Sannan ƙasa-ƙasa ta ce, “Ba Uncle bane....”
Sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda fitowar sa.
Nimrah ta ce, “Dukan ki yayi”.
Ciki-ciki ta ce, “A'a.” sai kuma ta kawar da zancen ta hanyar cigaba da faɗin, “Kema kamar kinyi kuka?”.
Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke itama. “Ba kuka nayi ba nima.”
Badan Ruky ta yarda ba ta ce, “Shi ne kika tafi ko sallama”.
“Kiyi haƙiri ba laifina bane. Har sonai nazo na dubaki da akace baki da lafiya. Nima fa ban san da tafiyar ba......” ta bata labarin yanda komai ya kasance. A karo na farko Ruky ta sanya ƴar dariya.
“Lallai Dadah ya iya wayo ALLAH. Har naji kin bani tausayi fa.”
“Muguwa kawai.”
Nimrah ta faɗa a hankali
Ruky ta ƙyalƙyale da dariya har Ammar na juyowa ya kalleta. Sai dai baice komai ba ya cigaba da shirinsa. Sai kuma ga kiran Bilal ya shigo masa waya shima. Dole ya fita a ɗakin saboda jiransa da yake yi zasu je gidan Daddy Imran godiya da gidan Baffah irin ta surukai...
Ruky na ganin ya fita ta miƙe taje ta sakama ƙofar key.
“Humm Uncle fa na nan ne”.
“Da gaske?”.
“ALLAH kuwa. Amma ya fita yanzu. Ninah wlhy ina cikin Boni Uncle zai kashe ni. ALLAH da nasan haka auren yake kuka zan taima su Mammah kar a kawoni nan. Gashi ya hanani ko zuwa sashen Mammah, sau ɗaya muka je da shi”.
“Humm Ruky kema kenan da kike cikin gidan. Ni nace mi an kawoni nan babu mai ceto. Daren shekaran jiya na zata mutuwa zanyi. Ni bama wannan ba, ina cikin ruɗani Ruky magana nake son muyi.”
Jiki a sayaye Ruky ta ce, “Miya faru?”.
Shiru na sakkanni ya biyo baya daga ɓangaren Nimrah, sai faman jujjuya yanda a karo na farko zata fitar da abinda ke danƙare a zuciyarta take..
“Ni–nah…?” Ruky ta kirata a hankali.
Nimrah ta ja numfashi mai nauyi kafin ta ce, “Ruky.. kina ganin mutum zai iya zama mai hali mara ƙyau, amma kuma a wani ɓangare yana tsoron cutar da wani?”.
Ruky ta ɗan yi shiru tana juya tambayar..
“Ban gane ba, mizai hana ki bani a buɗe” ta faɗa a hankali.
Nimrah ta lumshe idanu na ɗan lokaci, kamar mai tattara ƙarfin magana. Kafin ta ce, “Misali.. idan mutum yana da ikon yin abu, ko ya taɓa aikata maka wani mummunan laifi da shi yake tunanin baka sani ba. Sai kuma ka sameshi yana riƙe kansa saboda kada ya cutar da kai a wani ɓangare na rayuwa”. Muryarta ta ɗan dusashe a ƙarshe.
Ruky ta zauna sosai a gefen gado, zuciyarta na bugawa da sauri.
“Ninah mi yake faruwa ne a nan?.” ta tambaya da kulawa.
Nimrah ta yi saurin girgiza kai kamar tana a gaban Ruky.
“Ba abinda ya faru...” ta faɗa da sauri. Sai kuma ta rage murya, “Ni dai… ina jin kamar ina buƙatar sanin Dadah fiye da haka.”
Ruky ta haɗiye yawu. Sukai shiru na wasu sakanni. Kowa da abinda yake tunani a bangarensa.
Ruƙayya ta katse shirun nasu murya na rawa. “Kina nufin Dadah ne ya aikata miki wani abu na laifi ko wani?”.
Nimrah ta yi shiru. Numfashinta na fita a hankali kamar wanda ke jin nauyi a ƙirji. Cikin basar da tambayar Ruky ta ce,
“Ruky…” ta kira a hankali, “idan aka ce miki mutum ya canza saboda wani abu da ya faru da shi zaki yarda?”.
Ruky ta ɗan kalli ƙofa, zuciyarta na mata wani irin bugawa, cikin in ina ta ce, “Idan akwai hujja Nimrah zan yarda. Kinga ko hujja sai da bincike ake iya tabbatar da ita”.
“Haka ne. To idan kuma akwai abinda kika gani da idonki ya saɓa da abinda aka faɗa miki na hujjar da kika bincika fa?”.
Tambayar ta tsaya kai tsaye a zuciyar Ruky. Ta kasa bada amsa na ɗan lokaci. Sai zuwa can ta ce, “To a nan dole ne na fara tambayar kaina gaskiya Ninah? Sannan dolene na ɗauki abinda na gani a zahiri ba wanda aka faɗa min ba. Idan har a lokacin ina jin rashin gamsuwa ko rarrabuwar tunani, sai nabi komai da misalin zahiri sannan na rage tsanantawa. Na kuma saki jiki da wanda nake zargin koda bai cancanta ba domin kawai na samu tabbaci na ƙarshe”.
Nimrah ta runtse idanu. Hawayen da suka ciko mata na son zubo mata. Amma ta haɗiyesu da ƙyar.
“Duk abinda kika faɗa shine gaskiya Ruƙayya, nima kuma shine matsayata. Sai dai wlhy wannan gaskiyar kuma tana tsorata ni da rikita min tunani…” ta faɗa muryarta na rawar kuka.
Ruky ta miƙe tsaye gaba ɗaya.
“Ninah… kina bani tsoro fa? Minene wannan abin dake baki tsoron?”
Nimrah ta kasa amsawa, shiru na wasu sakanni kafin ta ce da murya mai rauni, “Ruky Dadah ba kamar yadda suka ce da ni bane, idan har zan auna da gaskiyar da naketa gani a yau ɗina…”
Kalmar ta fita a hankali… amma nauyinta ya sauka a zuciyar Ruky sosai da ƙarfi.
“Me kike nufi?” ta tambaya da sauri.
“Bazan iya faɗa miki yanzu ba saboda wasu dalilai…” ta faɗa da murya mai rawa.
Ruky ta dafe kanta jikinta na ƙoƙarin fara rawa.
“Ninah!”
ta kira da ƙarfi kaɗan, “kina nufin kina cikin wani hali ne da ban sani ba?”.
Nimrah ta girgiza kai a hankali tamkar tana a gaban Ruky.
“A’a, ba haka bane. Kawai dai akwai abubuwa da ban taɓa tunanin su ba ne, sai kuma gasu a yanzu ina gani. Ruky ko kin san an taɓa poisoning Dadah? Kuma har yanzu yana akan magani ne....”
Numfashin Ruky ya tsaya cak. Kafin jikinta ya ɗan fara rawa kar-kar. Cikin rawar harshe ta ce, “Poisoning? Dadan namu?”.
“Tabbas Ruƙayya. Amma yana ɓoyewa babu wanda ya sani. Idan ma akwai na tabbata sai Daddy ne kawai ya sani.” tai ɗan yi murmushi, irin murmushin da ke cike da rikicewa da jin ciwo. Sai kuma ta cigaba da faɗin, “Ban sani ba ko kwanaki ukun da nai da shi ne anan ke neman canja min tunani, wani lokacin ina jin tsoro wani lokacin kuma…” Ta yi shiru.
“Wani lokacin kuma mi?” Ruky ta tari numfashinta cikin ƙaguwa da zubar hawaye. Sai Nimrah ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi itama tana share hawayenta
“…ina jin tausayinsa. Tausayinsa nake ji mai tsananin musamman a wannan gaɓar da naji abubuwa a kansa. Yana da damuwa, amma saboda karya cutar da mu yake kauda kai. Al'amarin akwai wahala, amma ina jin kwarin gwiwar na sallama masa koda zan cutu ɗin, tunda ban taɓa jin ance ga mace ta mutu saboda kasancewarta da namiji ba...”
Kalaman ƙarshe suka fita da rauni matuƙa. Ruky ta rasa me zata ce, sai sautin kukanta da ke fita a hankali har Nimrah na iya jiyowa.
Itama sai kawai ta yanke kiran saboda wani kuka mai ƙarfin gaske da ya taho mata, ta tabbatar kuma idan Ruƙayya ta jishi zai ƙara tayar mata da hankali ne.........✍️
88