← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 113

Sashe 75

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..........“Dadah barci”.
     Nimrah ta faɗa a galabaice tana miƙa masa kofin lemon dake hannunta. Wani mitsitsin murmushi ya suɓuce masa. Hannu yasa ya amshi kofin, tare da riƙota ta kwanto jikinsa. Komai bai ce ba, sai ma cigaba da shan nashi shayin da yay. Bayan kamar mintina biyar ya tabbatar da barcin nata yayi nisa sannan ya ɗauki wayarsa dake gefensa.
     Number Imran yay kira. Bugu biyu aka ɗaga. Yay ƙaramar gyaran murya yana amsa sallamar Imran ɗin, tare da faɗin, “Zaku iya ƙarasowa yanzu”.
      Daga haka ya katse wayar yana miƙewa ɗauke da Nimrah. Bedroom ya kaita ya kwantar a gadon dake gyare da shinfiɗu na alfarma. Ya ɗan ja jikinsa baya da nufin janyewa daga rankwafen da yake kanta ta riƙe hannunsa. Kanta dake saman filo ta mirgino ta kwantar da shi kan hannun tana sake ƙanƙamesa da ƙyau.
           Murmushi yayi da kai ɗayan hannunsa ya shafa kanta. “Sarkin rikici” ya faɗa akan lips tare da sumbatar ɗayan gefen na fuskar tata. Tamkar wadda taji abinda yay ɗin ta wani sauke ajiyar zuciya cikin barci.
     Da ƙyar ya samu ya zame hannunsa data dabaibaye. Yaja blanket ya lulluɓa mata tare da rage hasken ɗakin gaba ɗaya. Fitiwarsa tayi dai-dai da isowar wani jirgi mai kama da nasu. A jikin nasun ya tsaya tafiyarsu ta daidaita. Cikin abinda baifi mintuna uku ba zaratan mazajen guda uku suka bayyana cikin mabanbanta shigar sutura. Imran, Faro, T-Dalha. 
        A yanda Dada yay tamkar baiji shigowar su ba sai T-Dalha yasha jinin jikinsa. Ya ɗan dakata daga bayansu zuciyarsa na kai kawo. Yasan dama za'a rina. Zak-Shadow bazai taɓa wasa a bincikar waye shi ba zuwa yau. Ba komai shima ya shirya bayyana a gare su ɗin dama ai....
      Faro ya katse masa tunani ta hanyar nuna masa su ƙarasa. Koda suka ƙaraso Dada bai nuna yasan sun iso ɗin ba sai da yaja wasu sakanni. Su Imran kam da suka san halin kayansu babu wanda yanayin Dadan ya dama. Sai ma Imran ɗinne ya kai zaune a kujerar kusa da shi ƙasa-ƙasa ya furta, “Ango kasha ƙamshi”.
        Ƙasa-ƙasa ya harare shi. Shi ko yay guntun murmushi dan yasan iyakar amsar da zai samu kenan. Karo na farko ya ɗago da ƙyau ya kallesu. A yanda ya ɗago ɗin kuma tare da zubama T. Dalha idanunsa ya sa T. Dalha ɗin kasa jurewa ya risinar da nashi yana sakin murmurshi. Sai kuma ya furta, “Ai min afuwa ranka ya daɗe”.
     Dada ya kauda kansa batare da yace komai ba. Hannu ya fara miƙama Imran sukai musabaha, kafin ya maida ga Faro shina sukayi, sai kuma ya miƙama T-Dalha da baiyi zato ba. Ba'a fagen aikin kawai ba, hatta a shekaru Zak-Shadow ya girme sa. Dan haka ya kasa bashi hannun, cike da girmamawa kawai ya ce, “Good Evening Sir”.
        Dadah bai amsa ba, sannan bai ajiye hannun nasa ba, sannan bai daina kallonsa da kaifafan idanunsa ba. Sai ma a karo na farko da bakinsa ya furta, “Ai min afuwa, idan gaishe da suruki ta hanyar musabaha a al'adarku kuskure ne”.
     Ba T-Dalha ba hatta Imran da Faro sai da abin ya basu dariya. T-Dalha ya shiga girgiza kansa da faɗin, “Sam ba haka bane ranka ya daɗe, ai anan ba surukuta bace maƙasudi, muna a fage ne na Boss da yaron sa”.
        “Tabbas ina girmama aiki, amma mafi girma a cikin alaƙa shine na girmama zuri'ar da suka bani tsatso daga cikin tsatson su”.
        “Haka ne ranka ya daɗe”.
T-Dalha ya faɗa murmurshi mai faɗi na mamaye fuskarsa. Hannunsa ya saka cikin na Dadah, sukai musabaha cike da girmama juna. Imran da Faro hakan ya musu daɗi matuƙa. Dan hatta fuskokinsu sun kasa ɓoyewa. Dadah ya ɗan gyara zama bayan ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya, sam babu wasa a tare da shi, dan aikin dake a ƙarƙashin UNIT ZERO shi oga ne a gare su, duk da yasan badan kasancewar T-Dalha a wajen ba shaƙiyancin da Faro da Imran zasu masa bashi da iyaka, koda yake yaga yau Faro ɗin ma kamar yana jin kunyarsa ne shima.
       “Barkan ku da zuwa Dubai”.
   A tare suka amsa masa. Yay shiru na wasu mintinan sannan ya kalla T-Dalha tare da jeho masa tambaya.
      “Ka ɓoye mana kanka saboda baka yarda damu bane? Ko kana bibiyarta saboda kana tare da su?”.
         T-Dalha da tambayar tazo masa a bazata yay saurin girgiza kansa da faɗin, “Har abada Sir! Har abada ni Tanimu Dalhatu Muhammadu bazan kasance a bayan azzalumai ba.”
       Dada ya lumshe idanun a hankali. Sai kuma ya sake buɗewa a kansa. Wata tambayar ya sake jeho masa mai kamanceceniya data farko.
          “Tun yaushe kake bibiyarta?”.
      Kawu Tanimu yay ƙaramar dariyar data saka su Imran murmusawa suma. Yatsa ya kai ya ɗauke hawayen da suka ciko masa ido. Har lokacin fuskarsa da murmurshi. “Tun a ranar farko da Yaya Hassatu ta baka ita. Komai daya faru ina a wajen. Dan in baka manta ba a daren ranar kuka sallameni ni da sauran ƴan uwana bayan kun mana tambayoyi. Koda muka zo gida mun samu Yaya Hassatu bata gidan, ƴan uwanta sun zo sun ɗauketa bisa umarnin mahaifinta. Ni kuma sai nayi tunanin binta, na fito kenan kawai mutanen nan suka kawo wannan harin daya zama sanadin rashin da har yanzu har ma abada bazamu maida madadinsa ba....”
       Yay shiru ya kasa ƙarasawa. Sai dai idanunsa sun sake kaɗewa jazur. Sai da yaja numfashi ya fesar sannan ya cigaba da faɗin. “Sir labarin mai tsaho ne sosai. Amma komai ba zan ɓoye maka ba. Ka tambayeni duk abinda kake son ji zan baka amsa. A taƙaice dai ina tare da Zakanyata tun daga kuruciyarta har zuwa girma. Ko case ɗin yaron tsohon shugaban ƙasa a hannuna yake”.
       “What! Haba koda nace. Wlhy nayi mamakin lalata case ɗin nan cikin sauƙi”.
    Imran ne yay maganar dan ya kasa shanyewa. T-Dalha yay murmushi, tare da faɗin, “Sir! Aimin afuwa”.
       Imran dake murmushi shima ya ce, “Ba laifi kayi ba. Sai dai miyasa ka zaɓi yin hakan?”.
           T-Dalha yay ɗan shiru kamar mai nazartar amsa. Sai kuma ya nisa kaɗan tare da ɗauke guntun hawayen da suka sake cika masa ido. “Saboda na bama garina kariya Sir. Dan a yanzu haka kaf zuri'ata babu wanda yasan ina raye.”
      “Kayi ƙoƙari, kenan tun sanda muka maka kamun farko kai jam'i ne?”.
         “Bana ce ba, dan bani da wata shaida a rubuce ga kudin ƙasa da za'a iya kirana da jam'i a wancan lokacin. Sai dai na kasance babban ɗan leƙen asiri ga BABA”.
      “BABA!!”.
   Faro da Imran suka faɗa a tare, yayinda Dadah ya ɗan dakata da ga danna waya da yake shima ya ɗago idanunsa ya zuba masa.
         “WAYE BABA?”.
    A yanzu ma suka haɗa baki wajen tambaya. Shiru Baba Tanimu ya kasa magana. Har Dadah sai da ya ƙosa bama su Imran ba. Kafin yaja numfashi mai nauyi tare da fesarwa sannan ya miƙe. Kalma ta farko daya furta shine, “Ku gafarceni Sir's. Duk yanda zan bayyana muku waye Baba idan ba'a gabansa kuke ba ba lallai ku fahimta ba. Baba wani mutum ne ɓoyayye, sai dai ba yana ɓoyewa ne dan rashin gaskiya ko ta'addanci ba. Jarumi ne na gaske duk da a yanzu girma ya cimma sa. Yana hidima wa ƙasa batare da ƙasar ta sani ba, hasalima duk wanda ya sanshi yana ɗauka ya daɗe da rasuwa ne hatta a kundin tarihin aikinsa. Baba ya raini irin da yawa, da yawan da ni kaina bazance muku ga adadi ba. Baba nada manyan sirrikan shugabannin ƙasamu dama ƴan siyasa harda jam'in gwamnati. Sir's idan nace zan cigaba da baku bayani akan Baba zamu kwana anan ne batare dana ambaci koda kwatar abinda ya shafesa ba. Amma ga saƙo yace na bama Boss, sannan yace yana gaisheka, amincin ALLAH ya tabbata a gareka tare da aminanka guda biyu da zuri'arka baki ɗaya”.
     Yay maganar ƙarshe yana juyawa ga Dadah. Sai kuma ya ajiye wani mitsitsin box tamkar na ƴan kunne ko zobe a gabansa.
       Wajen ya ɗauki shiru, Dadah ya zubama box ɗin ido batare da ya ɗauka ba. Hakama Faro da Imran Box ɗin suke kallo tamkar wani bomb mai ƙoƙarin tashi a gabansu..
     “Taya ka san shi?”.
    Furucin Dadah ya yanke shirun daya ratsa.
    Kawu Tanimu ya bashi amsa cike da girmamawa.
         “Na san shi ne ta tun ina da ƙarancin shekaru a dalilin mahaifinmu. Dan mukan je kai masa abinci a wasu lokutan tare. Lokacin yana rayuwa ne a gefen garinmu. A hirarsa da Babanmu na fara jin kishi ƙasata da son cigaban yankina da mahaifata. Daga baya aka kaini makarantar allo, sai da na shekara bakwai acan sannan na zo gida, sakamakon rasuwar mahaifinmu. Tun daga nan ban koma makarantar allo ba, na kuma manta da Baba sai dai gininsa ya faɗaɗa a ruhina, amma banda karatun boko balle nasan ta ina zan kama. Yayana yamun aure bayan shekara biyu, dan a garinmu hatta mu maza ana mana aure da ƙarancin shekaru da basu wuce ashirin ba. Duk wani matashi kan fita neman kuɗi bayan an masa aure, sai lokacin noma muzo gida.........✍️
91
Chapter 75 · 0% Book details