← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 113

Sashe 90

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Bayan su Dadah sun kammala cin abinci basu zauna ba, acewar su zasu je gaisuwar juma'a. Addu'a Mammah da Gwaggo Khadijah tai musu. Sun zo zasu wuce Nimrah dake yima su Naseer wasa suka haɗa ido da Dadah. Yatsunta babba da manuniya na duka hannun ta haɗe tai shape ɗin love tamkar tanama su Khadijah wasa. Suna sake haɗa ido ta ɗaga masa gira ɗaya alamar da shi take.
         Dadah da ke kallonta ƙasa-ƙasa amma sai ka rantse hankalinsa nakan Afrah dake masa shagwaɓar zata bisu ne. Ƙaramin ɓoyayyan murmushi yayi. Sannan ya ɗauki Afrah yana gaya mata abinda babu mai ji. Sai gani kawai sukai yarinyar na dariya. Koda ya ajiyeta kuma alamar ta haƙura sai ta sheƙa inda su Nimrah suke ta haye saman jikinta.....

        %%%%%

    “Yau lafiya naga kana haɗa kaya?”.
“Akwai matsala ne, zanyi tafiya taa kwana biyu.”
      Mamaki ya sake kama Malam Almu. Cikin kasa haƙuri ya ce, “Kwana biyu? Amma kasan akwai matsala yin hakan? Musamman tunda ba'a sanar da masu gidan ba.”
        Wata uwar Harara Sanda ya watsa ma Malam Alamun. Sai dai kafin yace wani abu Malam Buba ya shigo ɗakin, dole yay shiru. Shima Malam Almu sai ya wayance da ɗakko wani zancen dan kar malam Buba ya tsargu. Biye masa Sanda yayi, suka cigaba da tattaunawa akan abinda bashi suke magana ba da farko. Dan haka Malam Buba bai fahimci komai ba....

      Lokacin da su Dadah ke fitowa ma sai da sukai horn malam Almu ya fito ya buɗe gate. Daddy Imran na ficewa ya ɗan kalla Dadah dake gefensa yana danna waya. “Ina muka nufa?”.
       Dadah ya ajiye wayar yana furzar da iska. Shima Imran ɗin ya ɗan kalla, sai kuma ya kauda idanun nasa. “Mu fara gaida Baffah da Hajjo. Sai dai kira min Yusuf”.
        “Okay”.
   Imran ya faɗa yana ɗaukar wayarsa. Yusuf ya kira, bugu ɗaya ya ɗaga. Cike da girmamawa yay sallama tare da gaisuwa. Maimakon yaji Imran ya amsa sai yaji Dadah. Cikin ƴar rikicewa ya sake faɗin, “I'm sorry Boss. Barka da dawowa”.
       Dadah bai kula ba. Sai ma tambaya daya jeho masa.
    “Kana ina?”.
“A yanzu haka ina barrack Sir?”.
“Ina yaron nan da nake yawan ganinku tare?”.
       “Maina! Yana nan, yanzu haka tare muke kiran Oga ya shigo na tashi”.
     “Ka yarda da shi?”.
  “Wlhy ɗari bisa ɗari Sir. Dan ban taɓa kamashi da wani abu mara ƙyau ba. Sannan Soja ne mai ƙwazo da kishin ƙasa”.
       “Good. Ka sashi ya shirya akwai aikin da zai min za'a tura maka komai yanzu”.
     “An gama boss”.
  Dadah bai sake cewa komai ba ya ma yanke wayar. Imran da ke kallonsa ya ce, “Kamashi zaka sa ayi?”.
       “Dole muyi hakan da gaggawa, idan ba haka ba zai gudu”.
     “Zaki nawa maganin ƴan iska”.
Ƙaramar harara Dadah yay masa yana ɗauke kai. Shima sai ya tada motar yana dariya. Shima waya ya ɗauka kawai ya tura ma Yusuf saƙo....

         |•|•|•|•|•|•|•|

    Cikin sanɗa Rayhana da tun ɗazun take auna yanda zata shiga sashen Dadah ta samu nasarar shiga yanzu. Ba ƙaramin ƙyau da tsari falon yay mata ba kuwa. Amma yanzu bata ƙyawun falo take ba. Ta samu damar aiwatar da abinda ya kawota ne barinta. Cikin waige-waigen rashin gaskiya duk da ta sakama ƙofar falon key ta ƙarasa inda bedroom ɗin ƙarshe yake. Sai dai koda ta murɗa handle ɗin sai taji ƙofar a rufe. Da sauri ta bar wajen ta dawo na farkon. Tana taɓa nan ta buɗe. Wani irin sauke numfashi tai da tura ƙofar.
     Har yanzu Nabeeha na kwance kuwa tana shaƙar barci. Ta ɗan bi bedroom ɗin da kallo. Ƙmnshin turaren mai shi daya zama iskar shaƙa a ɗakin na ratsata. Komai tsaff  kamar ba'ai amfani da shi ba. Gudun kar Nabeeha ta farka dan tasan bata da nauyin barci sosai ta duƙe, da tafiyar sanɗa sannan a duƙe ta ƙaraso gaban gadon. Barci sosai kuwa Nabeeha dake mamuƙe da filo keyi. Sai taji kamar ta cakama banza wuƙa, dan ta gama fahimtar abinda take zargi ne ya faru. Hawaye suka cika mata ido. Tadai daure bata bari sun zubo ba. Ƙaramin fright dake bedroom ɗin ta buɗe, ta ajiye goron ruwan data naƙalo guda biyu bayan ta kwashe na ciki da suka rage guda huɗu, cikin sake ballama Nabeehan harara ta rarrafa ta fice da su....

        Fitowarta a sashen gaba ɗaya tayi dai-dai da shigowar Nimrah da Ruky, sai Small Mom da Asma'u dake bayansu. Small Mom ce tazo taga ɗakunan su. Shine suka fara zuwa nan kafin su je nasu Ruky dan su Aunty Ummi sunce su haɗe a sashen su Shariffa zasuyi magana da su. Basa kuma son su Mammah su fahimta shiyyasa akai abin cike da tsari. Ita Ruky hankalinta nakan charting da Ammar, lallaɓata yake wai tazo zai bata saƙo a sashen su. Ita kuma tace taƙi wayon. Shine ya sake turo mata “Please Baby”.
       Tana bashi amsa ne suka shigo babban falon sashen su Nimrah dake kallonta baki sake. Zatai magana idonta ya sauka akan Rayhana dake sakkowa daga sashen Dadahn. Sai dai tana ganinsu ta wayance ta hau danna waya kamar a tsaye take wajen kawai.
     Nimrah sarkin tsarguwa. Tuni ta sakama Rayhana alamar tambaya. Sai dai batace komai ba suka wuce. Rayhana kuma tabar wajen tana saka waya a kunne cike da bariki tana magana cikin ɗaga murya ita a dole kar su Nimrah su zarge ta...

        Har suka gama abinda suke a sashen suka sake fitowa abin nan na Rayhana bai bar zuciyar Nimrah ba. Daga nan sashen Asma'u suka shiga. Nan ma ko'ina sai da suka shiga kowa na santi kamar sashen Nimrah. Sun iso sashen Ruky suka samu Ammar ya ɗakko abu zai fito. Ruky yay ma ƙaramar harara a kaikaice. Ta masa gwalo itama tana murmurshi. Sai yay mata alamar zasu haɗe ya fice.
       Nimrah dake lure da su tai murmurshi. Sai da suka shiga ne take ma Ruky raɗa. Itama cikin raɗa Rukyn ta ce, “Ninah a rage sakama masoya ido.”
      Baki Nimrah ta riƙe. Tare da faɗin, “ALLAH ya shirya min ke Trouble Buddy”.
       Ruky ta sake sakin dariya. Asma'u da Biebah dai basu bi takan su ba. Dan sun san munafuncin kafi Autocin Mammah mai lasis ne. Sashen Rukyn ma ko'ina sai da suka shiga. Nan ma komai ya musu ƙyau. Koda suka fito sai suka nufi sashen Lailah inda su Aunty Mommy ke jiransu.
       Kayan da aka baje a tsakiyar falon suke kallo. Ruky da Nimrah suka kalla juna. Dan sarai sun gane irin kayan da akaita danna musu ne lokacin biki. Sai da suka zauna Mimi ta ce, “Ku bani hankalin ku nan musamman ku iyayen rawar kan nan guda biyu. Mu da ku yanzu mun zama ƙawaye. Duk wadda aka ba abu tai wasa zata sha mamaki na. Dan wlhy ɗura zan koma yi muku. Kayan nan kaf dake nan babu wani abu na cutarwa. Daga su Dabino, cukwiy, madara ne da abinda nan gaba duk zaku gane. Ninah! Ninah! Ninah sau nawa na kira ki”.
        “Uku Mom”.
    “Kece mai Head girl a cikin ku, wlhy ki nutsu ki karɓo mana kambun SARAUNIYA. Wanan bakin na Dadah so muke muji ya buɗe duk motsinsa murmurshi ya dinga fita”.
       Kasa daurewa Aunty Mommy tayi ta sanya dariya da faɗin, “Baki da kunya Mimi. So kike Dadanmu ya susu ce.”
     “A wlhy Aunty a ɗaki ya susu ce mata. Mu mun yarda idan ya fito yayta haɗe fuskar”.
   Yanzu kam babu wanda bai dara ba. Ta koma kan su Biebah. “Kuma kar kuji nace dan tana da Head girl ku zama lusarai. Duk wadda ta bari saboda sakacinta akai mata Head girl ɗin sai naci ƙaniyar ku. In ma zata zo tazo da wani dalili bana sakacin kula da miji ba. Ba kuma waɗan nan ne kawai kular ba. Tsafta, ƙamshi, ku nutsu kusan mi mazan ku ke so miye basa so. Mutum yasan abinda zai fito bakinsa a gaban miji. Ibada, ibada ina sake maimaitawa. Dan duk yanda kake tunanin namiji na sonka dole ka sake dagewa da gayama UBANGIJI ya ƙara saka masa soyayyar ka. Sai haƙuri. Ba komai ake ma shiru ba, sannan ba komai akema faɗa ba. Kowacce ta iya maganin matsalar ta a ɗakinta. Sai in abun yafi ƙarfinta ne dan kar naji kar na gani yawon kai ƙara”..
       Bayan Mimi ta gama nata suma sauran ɗaya bayan ɗaya sukai nasu. Harda koya musu kalolin abubuwa da suka kusan saka Nimrah da Ruky narkewa. Asma'u da Biebah da yake sun girme su ƴar sinne kai kawai ake. Su ko sukai fuska kamar basu fahimce su ba sai da suka feɗe musu biri har wutsiya...........✍️

      (Wai head girl, ALLAH ya shirya matar Uncle L dai jama'a ita ta bamu sunan ga🤣🤣).
106

..........“Halan bakaji inda nace ka kaini bane zaka yo nan dani?”.
     Zaka rantse mai taxi baiji abinda Sanda ya faɗa ba. Ran Sanda ya fara ɓaci, cikin fusata ya fara masifa, yayi da turanci yayi da hausa. Amma mai taxi yayi kunnen uwar shegu da shi yana ta garzaza gudu. Sanda ya fahimci dole ne yay wani abu a wannan gaɓar. Dan wannan mai taxi ɗin ɗayan biyu ne. Kodai ƴan one chance, ko liƙi ne ya buɗe abokan hamayya masu neman sa'a suka harbo shi. Ina hakan bazai faru ba, dolene ya ƙarasa abinda ya fara...
        Da wannan tunanin ya mamayi drivern ya kai masa mahangurɓa a wuya. Sai dai ina shima ƙwararre ne, dan cike da salon ganewa ya duƙe kan steering. Yana kuma ɗagowa ya wanke fuskar Sanda da spry. Luuu Sanda yay baya ya zube a kujera.
      Dariya Driver ya ƙyalƙyale da ita harda duka steering. Daga haka ya ƙarama motar wuta zuwa inda ya nufa...

•=•===•===•=•
Chapter 90 · 0% Book details