Sashe 59
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
.........Bayan idar da salla yayi addu'a mai zurfi data zama sirri a gareshi. Koda ya miƙe kai tsaye bayin ya koma. Ruwa ya haɗa a cikin bathtub dai-dai yanda yake buƙata. Daga haka ya sake fitowa zuwa gaban gadon da tarihinsa mai girma ne. Zaune ya kai yana yaye bargon daya rufeta da shi, kafin ya zuba ruwan dake a hannunsa kaɗan cikin tafin hannu ya kai fuskarta ya shafa.
Shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Abinka da tsohon soja daya saba ganin wannan kicimillin. Babu alamar ya tsorata balle tunanin ko dai ƴar shila ta shilla ne. Sake ɗibar ruwan yayi ya shafa mata sannan ya kamo hannunta cikin nashi ya fara murzawa. Tamkar wani abun tsafi ko almara kawai ta kawo wani nannauyan numfashi tare da zaburowar data saka shi tarota babu shiri. Maimakon komawa shi sai ya sakata a cikin jikinshi yana sauke nannauyar ajiyar zuciyar da tafi tata haɗari da barazana.
“I'm sorry”.
Kalma mai jimla biyu rak daya ambata akan lip yana sake matseta a cikin jikinsa ta fita a hankali. Sabon azaba da bigiren firgicin data suma akai ya sata fasa masa ƙara. Dole ya lumshe idanunsa dan ya shirya karɓar komai ɗin daga gareta da gaske kamar yanda ya ambata...
A tausashe ya sake ambaton, “Relax..”
Ina a wannan gaɓar fa relax bata aiki a cikin kunen manyan mata balle zame musu kalmar lallashi. Dan jin muryar mazajen fama ma kamar sake rikitar da ita yayi. Ba arziƙi jikin Nimrah mai son soyayya da son a nuna mata SOYAYYA ya fara rawa tana ƙoƙarin barin jikin Dadah. Hummm hajjaju Nimrah kenan. Waya gaya miki a banza ake shanye daɗaɗan kalaman rijalu ɗin ne a farkon yaƙin. Ai sai da kowa yaci ƙwal ubansa sai irin su BALLAGAZATU masu rabama BUNSIRAYEN titine kawai suke cin bulus mai komawa dana sani. Sune duk jawabin da zamu jero a labaran novels basa ganewa balle muhimmancin wannan dare da soyayya take ɗibar MATAN KWARAI a gajimare ta kaisu ta baro. Sai daga baya kiji ana wayyo-wayyo ka matsa bana son ganinka kafin wayyo-wayyo ta sakamakon shagali ta fara itama wato CIKI...
Dadah dai bashi da wani zaɓi a wannan gaɓar, face ajiye batun son ganin nutsuwar Little Shadow ɗinsa dan ba nutsuwar zatai ba kamar yanda yake buƙata. Fahimtar hakan da gaskatawa ya sashi ɓame bakinsa ya miƙe cak da ita zuwa bayi. Bata fasa kukan ba kuwa, dan yanda take ji da karfi ne da ita babu abinda zai hana ta nuna ta manta Dadah ne fa ta gallara masa cizo mai zafin gaske kamar yanda ya manta itace Nimrah ce ya bata gwale-gwale. Amma ina, manyan mata anyi laushi ɗan gaske. Dan koda ya sakata a cikin bathtub ma dake shaƙe da ruwan ɗumi banda ƙara da ƙanƙamesa babu abinda ta iya yi. Sai ko wasu nauyayan ajiyar zuciya masu kamar zasu maidata a suma da suka shiga biyo baya. Sai ruwan hawayen dake maye gurbin busassun na jiya da ɗauraye majinar datai ma fuskarta ado...
A hankali ya shiga shafa kanta cike da lallashi da tausayawa. Sai kuma ya sumbaci kan nata fin sau uku. Cikin ajiye batun miskilanci ya shiga jero kalamin lallashi masu kama da ban haƙuri cikin hikimar manya ma'abota kamewa da iko...
“Nimrah, duk abinda na koya a rayuwa… shine in kiyaye ki. Ki sani, ke ce nutsuwata, kuma ke ce tashin hankalina. Amma kiyi haƙuri komai zai daidaita JARMUTA MA'ABICIYAR KAMEWA DA TARBIYYA.”
Kalamai dai kam sun shiga, amma da alama basu da tasiri kamar na daren jiya a farkon wasa da shauƙinsu ya kwashi uwar daba taci mai garin ƙauyensu na bankwaura a hannun BARADA. Dan basu saka ta daina kukan da take rairawa ba. Haka dai Dadah ya cigaba da canja ruwa har karo uku bayan sun shiga jikinta sosai har sun huce. Koda yake shima har da shi, dan sai da kusan nashi rabin jikin ya jiƙe wajen gasa ƴar shila mai bakin akku da a yau ya rufe ruff ya koma na damo...
“Zaki iya wankan tsarki?”.
Kanta a ƙasa ta jinjina. A ransa ya ce (Ashe akwai ranar da bakin nan zai mutu. Eh lallai ta tabbata nayi aika-aika). Ita da da bata san mi yake ayyanawa ba duk da matsananciyar kunyar kasancewar a tare da ita haka tayi abinda ya dace. Yako ɗakko bathrobe ya naɗota a ciki kamar yanda dai akema MATAN NOVEL a daren farko. Itama ɗin dai matar novel ce, kunga bai kamata ace ta banbanta da ƴan uwanta wajen nuna gata a wannan safiya ba kamar saura da suka gabata.
Uhmm su Dadah an zama masu hidima ga Nimrah. Dan tsaff ya goge mata jiki da gashin kanta sannan ya saka mata jallabiyarsa datai mata uban yawa ta koma kamar wata fatalwar dare a ciki. Hijjab ɗinta ya saka mata shima daga haka ya sake ɗaukarta ya kai saman abin salla ya tsayar. Cikin salon manya dake sake nuna naku ba irin nasu bane ya kamo fuskarta cikin tafin hannunsa duk biyu ya bata tagwayen sumba a goshi kafin ya furta, “Yi salla”. Daga haka ya matsa ya bata freedom na wucin gadi.
Hawaye suka silalo mata. Tadai daure ta kabbara salla dan bayan fa shagalin jin daɗin duniya akwai muhimmin abu shine neman aljanna. Ba kuma a saminta a gantali sai da sauke haƙƙin ibada. Abin tausayi da ƙyar dai Nimrah ta idar da salla. Sai dai fa wajen zaman tahiya hawayenta sun ninka na sanda take tsaye. Sannan sai mutsu-mutsu take alamar SOJA yayi aikin nasu irin na masu ɗammara wato aika-aikar daya ambata.
Tana yin sallama ta zame ƙasa ta kwanta tana neman agajin UBANGIJI daga wannan yanayi. A dai-dai wannan lokacin Dadah daya gama kwashe abin shimfiɗar gadon daya sake tabbatar masa da gaske fa ƴar shilar nan ɗanya sharafar ya mallaka. Dan kuwa bayan shedar da shi kaɗai ya shaida ya sake ganin sheda ta biyu da ba lallai a gani daga kowace mace ba. Dan kowacce da irin tata halittar da kuma yanayin shekarun da aka lulluɓeta aka miƙama rijalu. To ita dai hajjaju Nimrah an dace. Dan kuwa takai dole sai shimfiɗa taga ruwa musamman daya kasance farin abu baya zama tare da ja idan ba wanda akai adonsa ba tun daga inji..
Duk da ya ga ta idar kafin yaje gareta sai da ya sake canja sabuwar shinfiɗa daga wadda ya saka aka kawo ta hanyar kiran waya. Wannan kuwa da dama can ya kasance sabo ne fil yaci alwashin adana shi har zuwa ƙasar haihuwarsa bayan ya wanke da kansa dan babu shegen da ya isa sake hawanshi sakamakon ya zama na musamman. Amma sai ya gana da masu hotel ɗin dan samun dai-dai to tunda ba kayan gado bane...
Durƙusawarsa a gabata da durƙuso mai kayatarwa irin na maza tare da saukar tattausan hannunsa a saman fuskarta ya saka idanunta dake zubar da hawaye har yanzu buɗewa a hankali. Na shi na shiga cikin natan da gudun tsiya ta maida su ta rumtse gam. Ita a dole saita tabbatar masa da bata son ganinsa. Banga laifinta ba, dan duk macen da batai haka ba a irin wannan safiyar walle an barta a tasha. Murɗa irin wannan kambun da sarauta na mace itace tarihi baya manta ta koda ga tauriƙiƙin rijalu ne irin su Dadah...
“Good morning Little One…”
Ya faɗa da wani soft voice.
Sosai ta tura baki gaba kumatun na kumbura. Murmurshi ya suɓuce masa. “Ayi haƙuri manyan mata. In dai nine …you’re safe a tare da ni. Kin manta?”.
“Hummm!”.
Nimrah ta faɗa tana jan hijjab ya rufe mata fuska. Dadah ya sake murmurshin da har haƙoransa sai da suka bayyana. Cikin muryarsa data shige ga kuma ciwon kai ya furta, “Hummm na nufin bata shiga ba kenan ko. Da gaske nake you’re safe with me Little Tiger. Kuma zan tabbatar miki da hakan”.
Daga haka ya miƙe, tare da ɗaukarta camak. Yanda ya zubama fuskarta ido yasa ta sinneta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan murmusa tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda. Sai kuma ya fara takawa a hankali tamkar baya so har zuwa gaban gadon daya sha sabuwar shimfiɗa. Kwantar da ita yayi, tare da zama a gefenta ya zare hijjab ɗin jikinta. Rigar ya tattaro itama da nufin cirewa tai saurin riƙe hannunsa jikinta na rawa da tsuma...
“Relax.. tayi nauyi da yawa”.
“Uhm-uhmm”.
Ta faɗa tana sakin masa sabon kuka. Hannunsa ya maida kan goshinsa yana ɗan cije lips. Kansa ciwo yake masa kamar zai dare biyu, sam baya son yawan magana shima a wannan lokacin. Amma ya lura darun Nimrah mai lasisi ne. Sai da yaja sakanni kafin ya janye hannun ya zuba mata idanunsa kawai.........✍️
Kuna da bashin sauran 1 page a wajena, zuwa anjima idan uzirin daya riƙe ni jiya ya barni, dan wlhy a cikinsa na ƙara tashi, kun ganni kwana nai akan waya babu ko barcin minti ɗaya saboda farin cikinku😭. Har zuwa Monday kuma ba lallai na samu yanda nake so ba. Ku dai yi addu'a kawai, in ba haka ba kuda gani na sai Talata kuma🥺🥲🚶.
75