Sashe 17
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Duk yanda su Hanoon suke taka tsantsan da su Ruky yau da alama muguntar tasu zata motsa. Dan tunda Afeef ya sakko daga sama suke kallonsa suna ƙus-ƙus. Tun bai kulasu ba har yay tsaki ya tashi ya bar falon.
“Zakaci ubanka. Shegen ƙafa kamar na ƴan tsaki.”
Ruky ta faɗa tana raka shi da harara. Tsakin Nimrah taja itama da faɗin, “Ai garama ƴan tsaki kamar dai wani tsuntsu da ake kira zalɓe. Ya kamata yau yaji a jikinsa.”
Ruƙayya tace, “Ni kaina ina son ya fara ji a jikin san. Kina da wani plan ne?”.
“Akwai kuwa. Zo ki ji.......”
Ta gwargawaɗama Ruky komai a kunne. Dariya suka sanya. Tare da tafawa. A lokacin Biebah ke fitowa a kitchen. Sai suka gimtse. Dan basa son ta gane komai balle ta hana su. Bako ta gane ɗin ba. Sai ma aiki data sakasu na gyara mata ɗakin baƙi dan yau Faro zai zo. Shima take yima abu a kitchen. Yanda suka tashi ba musu yin aikin nan ya bama Biebah mamaki. Amma sai batace komai ba ta juya ta koma.
Sun fito sai karaf a kunensu Hanoon na cema Afeef, “Bro bakayi wankan bane?”.
Ƙaramin tsaki yaja yana bata amsa da, “Banyi ba, wannan Mumun yaron ashe ya birke makunar water higher kafin ya fita. Shine na ɗan kunna ruwan yayi zafi a ɗakin su Dayyan na ɗibo acan Dad ya kirani na kawo miki waya”.
Kallon juna Ruky da Nimrah sukai. A take kansu ya kawo haske. Komawa sukai da baya. Wuff suka shige ɗaki Nimrah na faɗin, “Ga dama ta samu ma ai basai anje da nisa ba”.
“Kamar ya?”.
Cewar Ruky yana waro idanu. Nimrah bata bata amsa ba. Sai ɗan goran dake ɓoye ta ɗakko tare da leda. “Da wanne za'a fara?”.
“Kai jama'a. Hot pepper kin fini bala'i fa. Yanzu dan ALLAH wa kika saka ya samo miki abin nan?”.
“Hahhh kina wasa dani. Kulu na saka shekaran jiya da zata gida. Wannan kalkashine kwanansa biyu kenan a jiƙe. Wannan karara ne”.
“Miye karara?”.
“Banza kefa haihuwar birni ce baki san komai ba. Wani abu ne mai shegen ƙaiƙayi. Idan aka sakama mutum sai ya koma kamar ya haukace”.
Dariya Ruky ta sanya babu alamar tausayi. Ta ce, “Yayi yanzu ya za'ayi?”.
“Muje ki gani”.
Da sanɗa suka fito a ɗakinsu suka haura sama. Sun san Mammah barci take yanzu. Dan in tai sallar Azhar takan ɗan kwanta. Small Mom da su Kulu hankalinsu nakan aiki a kitchen. Uncles duk sun fice. Mu'azz ma na school. Dayyan kuwa basu san ina yake ba. Ɗakin Mu'azz da Afeef yake zaune suka nufa. Ɗakin kaca-kaca. Shiyyasa kullum Mu'azz cikin ƙorafi yake yanzu. Sai da suka rufe kofar sannan suka shiga Bathroom. Shi da ɗan sauƙi a gyare yake, sun san kuma Mu'azz ya gyara kafin ya fita.
Sun san shower gel ɗin da Mu'azz ke amfani da shi. Dan haka suka ɗauki ɗayan da suka tabbatar na Afeef ne. Tsabar mugunta yana da yawa fa a ciki amma suka tatse rabi a wata robar sabulu da babu komai ciki suka haɗa da kaf kayan wankan bayin suka ɓoye sannan suka zuba karara a sauran suka ajiye. Sosansa ma suka ɗauka suka barbaɗa.
Received at 6:24 AMReactions: Tsakanin Nimrah da Ruky kar ta san kar ne. Tun ba'ayi nisa ba Ruky ta gane ƙarya Nimrah take. Da ƙyar ta iya gimtse dariya ta lallaɓa ta ɗauki wayar Biebah ta kunna recording ɗin video. Abu ya kai yanzu Afeef susa harda cokali. Da wuƙa ma ya rarumo aka ƙwace. Ya koma bango, ganin bazai masa ba ya koma ya ɗakko cokula. Riga dai tuni ya saluɓe ya watsar. Hijjabin Mammah kam sai da aka tsawatar masa. Amma ya gwada son cirewa yafi sau babu adadi.
Ita Hanoon da farko iya wuyanta ne da hannaye. Sai da ya kacame ta gudu ɗaki wai zatai wanka. Aiko tana zuboma kanta ruwan nan tun a bayin ta ƙara haukacewa. Da ƙyar ta iya ɗauro towel. Ganin haka Mammah ta hana Nimrah zuwa yin wanka, sai kaya da tace Biebah ta kaita ta cire. Caraf Ruky tace bari ta kaita. Suna shiga ɗaki Nimrah ta fashe da dariya.........✍️
Received at 6:24 AMKIƊA A RUWA 3
36
.........“Muguwa, wlhy dama na zargi ƙarya kike. Kai Trouble Queen kin iya munahinci”.
“Bazaki gane ba Trouble Buddy, dole fa sai da haka. Idan ba hakaba kin san halin Mammah tsaff zata ramfomu. I sauri bani kaya na canja mu koma kada a cigaba babu mu kallo ya wuce”.
Kwantar da hankalinki ai ina mana video. Tafawa sukai Nimrah na rungume Ruky. “Sai dake abokiyar ɓuruntu. Dole mai bakin uwa yasha bulalarmu”.
Haka suka cigaba da shaƙiyancin su kafin a canja riga a fito. Sai dai yanzu Nimrah ta rage nata soshe-soshen wai taji dama-dama data cire rigar. A wannan halin su Ja'afar suka iso gidan. Sai kuma ga doctor da suka kira shima ya iso. Nan fa doctor ya fara duba Afeef da yafi jin jiki. Abinka da fata fara jikinsa yay burɗin-burɗin kuma jazur kamar borin jini. A haka ma na Hanoon yafi nunawa saboda bayan farin ta tana ƙarawa da mai ita. Shi dai doctor bai gane komai ba sai hasashen Allergy ne kawai. Maybe ruwan da sukai wanka da shi ne. Nan fa kowa yace badai ruwa ba. Sai dai ko wani abu suka ci.
Koda ya tambaye su shi Afeef Banda kukan a taimakeshi babu abinda yake yi. Itama Hanoon ta kasa bada amsa. Sai da aka zo kan Nimrah ne tace ita bataci komai ba. Kuma batai wanka ba. Sai ta sake rikita tunanin doctor. Gashi ita bai maga komai a jikinta ba. Ƙarshe sai ya ɓige da wai jininta ne mai ƙarfi shiyyasa nata bai ƙarfi kamar nasu ba. Zai mata allura kamar su ta wayance ita dai a bata magani kawai tunda bai kai nasu ba. Nata ƙaiƙayin ma ya fara sauka. Maganin kuwa ya bata, akace a kaisu ɗaki su kwanta dan zasu iya yin barci. Nimrah bata sha magani ba. Cike da dabara ta juyema Ruky data kawo mata ruwa shi a hannu. Dan haka koda suka je ɗaki ƙofa ma suka rufo suka hau rawa....
ALLAH ya shirya🥱. Yau dai Afeef ya gane ALLAH ɗaya ne shi da Hanoon😂🏃🏼♀️.
\••••\••••\••••\••••\