← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 113

Sashe 49

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Sun iso asibitin cikin mintuna kaɗan saboda gudun da yayi. Bayan yayi parking da kansa ya fita ya buɗe mata. Ya miƙa mata hannu. Babu musu ta ɗora nata akai ya taimaka mata ta sauka. Tun suna hanya taji ya kira wani doctor RK. Dan haka suka shiga kai tsaye. Hakan ya tabbatar mata yasan asibitin sosai.
        A reception ya yanka kati, sai dai ita ya zaunar da ita a ɗaya daga kujerun wajen. Yana kammalawa yazo ya kama hannunta ɗaya a cikin receptionist ɗin tai musu rakkiya kamar yanda aka bata umarni. Dan bayan sun yanki katin ya sake kiran Doctor RK ɗin shine yace ya haɗashi da receptionist ɗaya.
       Har cikin office ɗin tai musu rakkiya bayan tayi knocking an basu izinin shiga. Har lokacin kuma hannun Biebah na riƙe a nashi.
    “Kaga manya, mazan fama”.
Dr RK ya faɗa da salon shaƙiyanci na abokai. Faro yay murmurshi yana kaiwa zaune bayan ya zaunar da Biebah. “Kai dai bazaka taɓa canjawa ba Doctor”.
         Dr RK yay dariya da faɗin, “Haba na canja mana.”
    “Kadai canja wataran. Ya kwana da yawa?”.
    “To Alhamdullah, ka ɓuya gaba ɗaya. Madam sannu da zuwa”.
       Gaishe shi Biebah tayi. Ya amsa tare da tambayarta yaya jiki. Kanta a ƙasa tace da sauƙi. A lokacin ne Faro ke bashi amsa. “Kai ne ka ɓuya Doctor. Tunda har invention na walima na tura maka kai da AA Darma amma banga idonku ba”.
      “Ya salam. I'm sorry ɗan uwan. Wlhy ban gani ba saboda bana ƙasar. Jiya jiyan nan na dawo. AA ma kuma baya nan. Kasan babu yanda za'ai ace mun gani muƙi zuwa”.
     “Nima nayi tunanin haka, duk da nasan kafi AA kirki”.
    Dariya RK yayi. “Ayi haƙuri to kammu a ƙasa. Kace mutumin ka shige daga ciki gwauranci ya ƙare?”. Dariya suka sanya a tare. Faro ya nuna Biebah da kanta ke ƙasa. “Ga Biebalo na nan kam Alhamdullah”.
       “To ALLAH ya sanya albarka ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba. Amarya sai munzo cin girkin amare. Amma sai AA ya dawo in sha ALLAHU zamu zo tare”.
      “ALLAH ya kawo ku lafiya”.
Biebah ta faɗa har yanzu dai kanta a ƙasa. Doctor RK ya ɗauka waya yana faɗin, “Bara na kira Doctor ɗin da zata dubata.”
     Babu jimawa kuwa wata babbar mace ta shigo. Cikin girmama juna suka gaisa da Dr RK. Ya nuna mata Biebah da faɗin ta dubata. Gefe suka koma. Bayan Dr Fatima ta fahimci matsalar Biebah ɗin ta rubuta mata magunguna, sai allura guda ɗaya da zatai mata yanzun nan. Biebah ba ƙaunar allura take ba sam. Dan haka dole Faro ya taso ya riƙeta cike da lallashi akai mata. Daga haka wata Nurse da RK ya kira ta shigo da ledar magunguna.
     Biebah nata ɓata fuska suka fito. Har gaban mota RK yay musu rakkiya. Sunyi sallama Faro na masa godiya sosai. Shi kuma yace ba komai ai ana tare. Itama Biebah tai masa godiya suka wuce. Koda suka iso gida bai barta ta taka ba. Yana gama taimaka mata ta fito a motar ya ɗauketa cak.
          Dariya ta fara da roƙon ya sauketa zata iya. Ya ce, “Ina Biebalo wannan aikina ne”. Haka ya kaita har cikin bedroom ya dire a gado. Ya kuma cire mata hijjab ɗin yana faɗin, “So sorry Zuciyar Haydar, na jawo miki ciwo ko”.
      Fuskarta ta ɓoye a jikinsa. Ya rungumeta kuwa tsam yana sumbatar wuyanta. Jikin nata ta ƙanƙame gabanta na faɗuwa. Zatai magana ya haɗe bakinsu waje guda. Bai barta ba sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so sannan ya saki lips ɗin yana rungumeta sosai.
     “Wannan na lallashi ne Baby”.
Ya faɗa a cikin kunnenta yana sake ƙanƙameta. Ita dai fatanta a rabu lafiya iya hakan. Dan haka cikin dauriya ta furta, “Yaya bamuyi sallar isha'i ba fa”.
          Idanunsa a lumshe yana shafa bayanta ya amsa da, “Yanzu zamuyi in sha ALLAHU Baby. Amma a tausaya min da kirana Yayan nan dan yanzu na tashi a wannan layin tunda na....”
     Ya ƙarasa faɗa a cikin kunnenta. Matsananciyar kunya ce ta gama dabaibaye ta. Ta ƙara cusa fuskarta a jikinsa da faɗin, “Kai Yaya ni dai ba ruwana”.
          “Har ɗan tsaki-tsakin ki akwai kuwa Biebalo na. I love you ALLAH yay miki albarka. Kin sani farin ciki sosai yau har kowa ya fahimci fuskanta ta kasa daina murmushi. Tabbas ke duniya ta ce. Bake ba hatta su Haysam yau na sanya musu albarka mara adadi. Dan sun rainar min farin cikina, matata cikin tarbiyya. ALLAH ya ƙarama Mammah lafiya da nisan kwana mai amfani da albarka. Ya bani ikon faranta miki da riƙe amanar Haysam har ƙarshen numfashi na”.
        “Amin Yayana, tare da su Hajiya. Itama ALLAH ya ƙara mata lafiya da tsohon rai. Tare damu baki ɗaya.”
      “Amin zuciyar Haydar. Kinga tashi muyi salla kici abinci kisha maganin ko”.
    Babu musu ta miƙe kamar yanda ya buƙata......

          ∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

   A hankali ta shiga buɗe idanunta. Sai kuma tai miƙa da ambaton addu'ar tashi a barci. A yanzu kam ɗakin akwai ƙarancin haske. Sai dai kana iya ganin komai. Dan haka kai tsaye ta gane a inda take.  Ta lumshe idanu da sake buɗewa lokaci guda tana tashi a zaune. Tabi gadon da take kwance da kallo, alamu sun tabbatar da kuma ita kaɗai ta kwana akai. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Cikin rashin damuwa da hakan ta yaye blanket ɗin da take ciki. Sai dai can ƙasan ranta tana mamakin ina Dadah.
       (Maybe ɗakinsa daban shima) Zuciyarta ta ayyana. Cikin gamsuwa da hakan ta sakko a gadon gaba ɗaya hankalinta a kwance. Karo na farko ta kai dubanta ga agogo. “What 6:34 fa?. Na shiga tara banyi sallar asuba ba”. Ta faɗa a fili tana sauka a gadon gaba ɗaya cikin rawar jiki. Da sauri-sauri ta sauke zip ɗin after dress ɗin jikinta. Wando da rigar ciki suka bayyana. Imani da ita kaɗaice a ɗakin yasa bata damu ba, hankali kwance ta nufi ƙofar da take hasashen bayi ce. Babu kuma wani tunani a ranta ta murɗa ta shige. Ya rabbi ƙaton bayi ne da yaji kayan amfani na alfarma. Sai dai bata da lokacin tsayawa kalla dan hankalinta na'a kan salla ne.
         Gaban mirror ta ƙarasa, harga ALLAH bata kawoma ranta akwai wani a ciki ba sam. Dan haka hankali kwance takai idanunta kan mirror ɗin da nufin kallon kanta. Hakan kuma yayi dai-dai da fitowar Dadah da yaji motsi daga wajen wanka. A matuƙar bazata ya bayyana ma Nimrah, kamar yanda shima ganin nata ya zame masa bazatar. A gigice ta jiyo har tana neman bugewa. Dole Dadah yasa hannu ya tarota. Saukar hannun nasa a dai-dai ƙugunta kuwa yay masifa-masifar sake gigitata. Ta runtse idanunta da suka sauka akan lafiyayyen jikinsa dake buɗe, dan daga shi sai guntun towel yake ɗaure daga ƙugu zuwa cinya.
         Duk da yaji wani iri shima amma ya basar. Wani kallo ya bita da shi daga sama har ƙasa, ya haɗiye yawun dake neman katse jijiyoyin maƙoshinsa, illahirin gashin jikinsa na miƙewa. Tun a jirgi yaga alamar ƙafar wando a jikinta amma bai kawoma ransa wannan shigar bace cikin after dress ɗin jikinta. Ba ƙaramin ɗaga masa hankali da tada sabuwar tarzoma surar jikin nata tayi ba. Cikin lumshe idanunsa da suka kaɗe a ƙanƙanin lokaci ya matsar da fuskarsa gab da tata, a hankali ya fara hura mata idanu da iskar bakinsa.
       Nimrah ta zabura sosai tana buɗe idanun. Suna shiga cikin nasa daya tsareta da su taji wata sabuwar kiɗima. Ga shi sai a lokacin ta fahimci hannunta fa ajiye yake a saman ƙirjinsa. Cikin sauri ta janye kamar wadda ta taɓa wuta tana ƙoƙarin fita a inda ya matseta jikin mirror ɗin. Ɗayan hannunsa yasa ya tarota tacan. Kanta ta shiga girgiza masa idanunta dake mar-marr na cika da hawaye. Batama san cikin suɓutar baki ta furta,
         “Na shiga uku Dadah ka rufa min asiri. Wlhy ban san kana ciki ba”.
    Sai hawaye sharr suka fara gudu.
Cikin wata kalar tattausar murya da bata taɓa ji daga garesa ba ya furta, “Shagwaɓaɓɓiyar Dadanta, waye yace kinyi laifi?”.
         “Ya rabbi! Dadah are you okay?”.
   Cikin sake lalacewar murya dakai fuskarsa kan wuyanta idanunsa a lumshe yana shinshinarta ya bata amsa da, “I'm not. I'm not okay Little Shadddd..”
      Tsirrr fitsari ya zubo ma Nimrah. Ta fashe da kuka tana son ture fuskar tashi, dan yanda yake shinshinar mata wuya gaba ɗaya ji take kamar wasu abubuwa na mata yawo a fata dama kwakwalwar ta.
      “Shike nan aljanu sun shiga Dadah Mammah. Na shiga ukuna Dadah kaiwa addinin ALLAH ka daina zan suma wlhy”.
           Karo na farko yay wani mugun murmushi, sai kuma ya kama kunnenta ya ciza kaɗan har sai da ta ƙanƙamesa babu shiri, tausasan laɓɓansa ya ƙarasa matsarwa kan kunnen sosai ya sumbata tsakkiya. Ai yanzu kam fitsarin ta saki da ƙyau tana buga salati kawai ta daka tsalle ta ɗare jikinsa gaba ɗaya. Ƙafafunta ta zagaye a bayansa tare da hannuwanta. Cikin magagin ruɗani ta furta, “ALLAHU Akbar, shike nan Mammah na kawo kaina. Dadah aljanu ni kuma mutuwa.”
        Dariya ta suɓuce ma Dadah, sai dai a maimakon ƙyalƙyalawa murmushi ne mai bayyana haƙora da da'ace Hajja Nimrah a nutse take babu abinda zai hana ta ajiye murmurshin nan cikin tarihi........✍️

       Wayyo ALLAH na🤣, wato aljanu sun shigi Dadah, ita kuma mutuwa zatayi. Ashe Ruky jaruma ce. Dangin Nimraty sai a nemo gumbar sadaka to, tun yanzu ana zancen mutuwa inaga an.....😂😂🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️.
65
Chapter 49 · 0% Book details