← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 113

Sashe 71

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Koda ta yi wanka har ta ɗauka bathrobe zata saka ta fasa. Towel ta ɗauka irin ƙaramin nan na goge jiki sai dai yafi mitsitsi girma ta saka. Koda ta kalla kanta sai da taji kamar bazata iya fita a hakan ba, dan gaba ɗaya cinyoyinta a buɗe suke. Inda zatai tafiya cikin sauri ma za'a iya ganin jikinta.
        Tana fitowa suka haɗa ido da Dadah dake tsaye yana waya. Nata ta kawar cikin dakiyar dole. Ta cigaba da tafiyarta zuwa gaban mirror domin shiryawa. Shiru Dadah yama kasa bama Daddy Imran amsar zancen da yake masa. Sai da Daddy Imran ya ce, “Zak.. kana jina kuwa.”
    Dadah yaja ɓoyayyar ajiyar zuciya. Sai kuma ya kauda kansa daga kallon Nimrah ɗin gaba ɗaya. Yana kammala wayar kamar dama abinda take jira kenan ta ƙaraso inda yake. Tamkar wata ƴar shekara goma cikin shagwaɓa ta ce, “Dadah yunwa nake ji”.
        Dadah dake kallon sai yaji ma ya kasa magana. Sosai ƴar rigar data saka da wando bomshort sukai mata ƙyau da sake maidata yarinya ƙarama. A hankali ya ciro hannunsa a aljihu ya miƙa mata alamar tazo. Babu musu ta matsa, maimakon kama hannun sai kawai ta shige jikinsa. Ta zagaye shi da hannayenta duk biyu tana kwantar da kanta a ƙirjinsa. Ɗakin yay shiru tamkar anma duk abinda ke motsi tsawa. 
       Sunfi mintina uku a haka, kafin Dadah ya ɗago fuskarta suna kallon juna. Cikin motsa lips kaɗan ya furta, “Bayan abincin fa?”.
        “Sai ka kaini yawo”.
    “Ai bakin ki ne yawon”.
Murmurshi irin na jin kunya tayi, sai kuma ta maida kanta ta kwantar a jikinsa. Kanta ya shafa shima da faɗin, “Zan kai ki yawo amma ba yanzu ba.”
       “Dadah nidai yanzu”.
    “No. Yanzu ana jirana”.
“Wayyo Dadah, nifa ranar daka tafi ka barni tsoro na dinga ji”.
       “Karki damu yau bazan daɗe ba. Awa biyu ne kawai.”
    “To Dadah ka bani aron wayarka”.
  “Shike nan naji”.
Da sauri ta ɗago cike da farin ciki ta ce, “Dadah da gaske?”.
      Maimakon amsata sai ya ja mata hanci tare da ɗage gira. Aiko ta daka tsalle ta ɗane shi cike da farin ciki.
          Idanunsa ya ɗan rumtse yana riƙeta, cikin jan numfashi da fesarwa ya furta, “Baƙya tausayina ko Kiddo. A koda yaushe kina son tada rikici”.
      Cike da wauta da rashin fahimtar ina kalamansa suka dosa tace, “Wai wannan rikicin minene shi? Sannan Idan banji tausayin Dadana ba nawa zanji”.
Cikin basar da tambayarta ya ce,
     “Uhmm banda wayo Kiddo”.
  “Hhhh Dadah ai kai kayi babba bazan maka wayo ba.”
      Yay ƙaramin murmushi.
   “Shike nan na barma anjima. Zan gani ko da gaske ana tausayin nawa”.
           Anan ma dariyar tayi, shima ya sauketa yana nufar bayi domin yin wanka...

       Sanda ya fito har ta gyara gadon tsaf. Tunda ta kallesa sau ɗaya ta kauda kanta dan shima da towel ya fito. Shima dai bai mata magana ba ya hau shiri, bayan ya kammala yay sallar walha daya saba. Koda ya idar gaban mirror ya koma yana ɗaukar agogonsa zai saka Nimrah ta iso wajen. Babu zato ta ɗora hannunta akan nashi dake ƙoƙarin ɗaura agogon.
        “Dadah kawo na tayaka”.
     Sakar mata yay babu musu. Koda ta gama ɗaura masa sai ta ɗauki turare ta fesa masa shima. Sannan ta juya ta ɗauka jacket ɗin suit ɗinsa dake sagale a kujerar mirror ɗin tana faɗin, “Dadah juya”.
       Ƙaramin murmushi yayi tare da juyawar batare da yayi magana ba. Tana gama saka masa ta dawo ta gabansa tana gyarawa. Dadah dai gaba ɗaya ta gama kashe masa jiki da mamakinta. Tie ɗinsa daya ɗan karkace ta kalla.
        “Dadah duƙo ka gani”.
     Dadah da bai san mi zatai ba ya duƙo babu musu, tana kai hannu saman tie ɗin ya ɗan sake matsowa har fuskarsu na zama gab da juna. A yanda ya kawo lips ɗinsa gab da nata ya sata ɗan ja baya tana murmurshi.
      “Zan fa gyara maka tie ne”.
   “Oh, na zata fa an kira ni nan ne”.
Ya faɗa yana sumbatar lips ɗin nata kaɗan, zai sake mayarwa ta ja baya da sakin ƴar dariya dan har ta gyara masa. Da dariyar a fuskarta tabar wajen. Ya bita da kallo zuciyarsa na masa sanyi daga fushin da suka nema sakashi ɗazun...

     Bai fita ba sai da sukai breakfast tare. Ya kuma cika alƙawari ya bar mata wayarsa. Ai kamar ALLAH-ALLAH take ya fita dama. Mammah ta fara kira. Sai dai yaƙi shiga. Ta ce, “Bari na bari anjima.” tai maganar tana maida akalar kiran kan Ruky. Video call taso suyi, dan haka ta shiga WhatsApp. Cikin rashin sa'a hannunta ya danna saƙon farko. Voice note ɗin dake ƙarshe yay playing. Ƙoƙarin kashewa tai sai kuma jin abinda ake faɗa ta ɗan dakata.
       Haka kawai ta samu kanta da yin scrolling charts ɗin zuwa sama, dan ta fahimci likitansa ne. A fili ta furta, “Badai Dadah yana da wani rashin lafiya bane bai son a sani?”. Jitai jikinta na neman ma fara rawa. Ta dai daure ta fara bin chart ɗin, dan gaba ɗaya voice note ne daga doctor, Dadah kuma na bada amsa da rubutu.
     Tun a voice note ɗin farko ta fahimci an taɓa poisoning ɗin Dadah, dan bayanin doctor ɗin ya buɗe mata komai. Mamaki ya kamata, sai taji ƙaimin bin chart ɗin daki-daki fiye da farko. Tun a kusan na tsakiya ta fara hawaye, dan ta fahimci har yanzu Dadah na'a kan magani ne, zai kuma ɗauki kusan shekara ne ma yana shansa.
      Hannunta na rawa ta sake kunna wani voice note ɗin. Tai shiru tana sauraren bayanin doctor ɗin da ke faɗin, “Mr Haysam na duba results ɗinka sosai. Gaskiya akwai cigaba, amma jikin ka bai gama dawowa daidai ba tukuna. Abinda ya faru da kai a baya ya bar tasiri a cikin tsarin jikin ka, musamman wajen daidaituwar hormones da nerves.”
      Nimrah ta haɗiye yawu a hankali.
Ta ci gaba da sauraro. “Abinda nake so ka fahimta shi ne, a wannan lokacin, duk wani abu da zai saka jikin ka cikin tsananin motsi ko matsin lamba zai iya janyo maka matsala. Ba wai nan take ba, amma a hankali zai iya jefa ka cikin wani yanayi da zai wahalar da kai. Hakan na nufin dole ka jinkirta a kasancewarka da mace daga nan har zuwa wasu watanni da zamuga yiwuwar hakan”.
      Amsar Dadah ta saka hawayenta silalowa.
        “Doctor akwai damuwa yin hakan gaskiya, amma me kake ganin zan yi? Saboda ina jin abubuwa suna wuce min hankali wani lokacin. Ina ƙoƙarin danne kaina amma bana jin zan iya ɗaukar hakan na dogon lokaci, shekara takwas ba kwana takwas bace ba. A sanda bana ganin su jikina bai cika tsanantawa ba. Amma wata ɗayan nan da dawowata gida kusa da su abubuwa na neman kwacewa”.
        Nimrah ta kalla date ɗin da aka tura saƙon, tabbas bai wuce wata da dawowar Dadan ba. Numfashinta ya ɗan tsaya. Cikin furzo shi ta sake kunna wani voice note ɗin daya kasance bayanin doctor ne.
     “Na fahimce ka Mr Haysam. Wannan ba sabon abu bane a irin yanayin da kake ciki. Amma dole ne ka yi taka-tsantsan. Idan ka bari kanka ya wuce gona da iri akwai yiwuwar ka rasa control ɗinka gaba ɗaya. Kuma hakan zai iya jawo maka matsalar da zata iya jinkirta warakar ka anan ma, ko ma ta dawo da wasu daga cikin ciwon da muka riga muka shawo kansu. Sannan ita kanta matarka zata iya jigata a hannunka fiye da kima…”
      Hawayen Nimrah suka fara taruwa. Ta sake matsawa kan saƙon Dadah dake a rubuce saɓanin na doctor dake duk voice note.
     “Okay then, I’ll do my best.”
“Hakan shine dai-dai Mr Haysam”.
    Amsar doctor ta biyo baya. Daga nan sakwannin da suka biyo baya duk akan yanda yake jin cigaban jikinsa ne, da karin shawarwarin doctor. Sai a sati ɗaya daya wuce Dadah ya kara ɗakko ma Doctor waccan maganar tasu dai, acewarsa ya kai wata matsaya komai fa zai iya faruwa. Amsar da Doctor ya bashi itace ta zuwa asibiti yayi wasu gwaje-gwaje ya tura masa.
     Bayan kwana biyu taga Dadah ya tura masa result. Koda ta buɗe hoton bata fahimci komai a cikinsa ba. Sai ta haƙura ta buɗe voice note ɗin doctor ɗin. Doctor ya nuna farin cikinsa da ganin yanda result yay ƙyau, sannan ya bama Dadahn damar iya kasancewa da iyalinsa a yanzu. Amma har yanzu akwai sharaɗin controling kai, in ba haka ba zai iya cutar da matarsa, saboda yanayin treating ɗin daya samu a watannin nan jikinsa ya ƙara samun tunzuruwar ƙarfi fiye da shekarun baya ma.
      Abinda Dadan yace ya ɗauki hankalinta sosai.
     “Da matsala kenan kuwa Doctor. Akwai fushin laifin da first wife ɗina ta mun har yanzu bai barni ba. Na tabbatar a irin wannan yanayin za'a iya samun matsala tsakanina da ita har a samu fiye da abinda ba'a so in har naje mata. My second wife is still very young, kuma bata fahimci abubuwa da yawa ba. Bana son na saka mata tsoro ko na cutar da ita saboda halin da nake ciki.”
        Murmurshi mai haɗe da kuka ya suɓuce mata........✍️

87
Chapter 71 · 0% Book details