Sashe 69
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..........First Lady ta saki wani murmushin ƙasaita da sauke nannauyan numfashi da ya saka Hajja Mangu zuba mata ido.
“Yaya dai Hajjaju ko ta samu ne?”.
“Zadai ta samu anan kusa kaɗan. Dan na sake samun wani makamin yaƙar Hasiba, sannan mabuɗin mallakar Nabeeha cikin sauƙi”.
“Kamar ya ban gane ba?”.
“Ba lallai ki gane ɗin ba duk bayanin da zan miki”.
“Ke dai bani ɗin tukunna”.
Hajja Mangu ta faɗa tana danna recording ɗin wayarta a kaikaice kamar yanda ta saba naɗe duk wata hirar ta da First Lady ɗin a ɗan tsakanin nan. Ita ko da bata isa sanin gaibu ba, ta saki baki tare da gyara zama ta zayyane mata duk yanda sukai da Nanah. Kafin ta ɗora da faɗin, “Ɗayan biyu, dole ne ɗaya ta faru. Kodai yarinyar na son mijin Nabeeha, ko kuma akwai wani ɓoyayen buri da take son cimmawa. Amma inada shiri a kanta...”
“Tab ɗin babbar magana. Ai ko idan haka ne akwai cakwakiya. Amma ni fa banga laifin su ba. Guy ɗin ne ya haɗu da haɗuwarsa. Irinsu haja ce mai tsada dake wuyar samu a cikin maza musamman na yankin nan namu baƙaƙen fata. Dan koni badan nasan ruwan kogin yafi ƙarfin ketarawata ba, babu abinda zai hanani shirya iyo a cikinsa. Amma dai bari mu zama koda ƴan kallo ne ƙila ma rage nauyin zukata”.
Dariya First Lady tayi mai armashi, ta ce, “Shegiya ƙawata badai zaki canja ba. Keda rijalun nan hummm”.
“Babu rana kam ta canjawar nan. Rijalu ai sai da mu, muma sai da su...”
“Hhhh Kuba. Mu kam mun wuce wannan mulkin mallakar”.
“Hhhhh Hajjaju bazaki gane karatun ba, a dai rufe rufau. A kuma dinga tunawa da al'ummar ANNABI LUƊU yanda suka ƙare. Yanzu miye naki shirin bisa ikon buwayi gagara misali”.
Tamau First Lady ta haɗe fuska. Rai ɓace ta ce, “Kinga abinda ke haɗani faɗa dake ai. An gaya miki mu a zamanin muke yanzu? Ko an gaya miki ba zamu tuba ba kafin tsufanmu da mutuwa.”
“Tuba kafin tsufa da mutuwa? To mi kuma ya rage ALLAH na tuba. Hhhh hummm Hajjaju na mai abin mamaki, sannan kuma mai abin baza haja. Shi fa ALLAH ALLAH ne. Ya kamata a dinga tunawa ana kuma shaidawa. Tunda baki so mu tsaya haka. Dama dai tunatarwa ce na zaman tare. ALLAH ya shiryemu baki ɗaya. A huce dan ALLAH.”
“Ai kuma kin ɓata wannan hirar. Jeki sai wani jiƙon”.
Hajja Mangu batai musu ba, ta miƙe tana ɗaukar handbag ɗinta kawai tare da sallama. Bata tanka mata ba kuwa, itama sai tai gaba kawai. Sai da ta shiga motarta har ta fice a gidan sannan ta saki dariya tare da saving ɗin recording ɗin nata. A fili ta furta, “Sai ni Hajja Mangu mai abin baza haja. Tabbas bana da sunan mu za'a kafe cikin masu kuɗin manyan matan wannan shekarar da zasu amshi award. Madam ki shirya, kaɗan ya rage mata su dire bisa kanki. Zan baki damar fara taka taki irin rawar ga Hasiba. Kafin ni kuma na canja kiɗan da nawa salon da dole kema fa sai kin taka koda a tsakiyar kasuwa ne babu ɗan kamfai”.......
×}}}}}}}}×{{{{{{{{{×
“Ina son ƙamshin nan Little One waya baki?”.
Dadah ya faɗa cikin kunen Nimrah data naɗe a jikinsa bayan ya barta da ƙyar. Bazata iya magana ba a wannan gaɓar, dan jinta take tamkar wadda aka zuƙema jini. Dadah ya iya salo na musamman dake karya garkuwar jiki fiye da cutar SIDA. Yana da wani salo dake saka ka manta da ko kai waye cikin ƙanƙanin lokaci....
“Uhmm Babie?”.
Ya faɗa cikin katse mata tunanin. Kanta ta sake turawa cikin ƙarjinsa, tare da sake naɗe jikinta da gaba ɗaya a nashi yake. Ya shafa mata baya zuwa ƙugu dake nan dai-dai wadaida. Ai ko saita sake ƙanƙamesa, cikin shagwaɓa da ƙanƙance murya ta ce, “Dadah ka daina magana”.
“Saboda mi?”.
“Kana sa wani abu na mun yawo a jiki”.
“Yunwa yake ji ne Little Shadow. Ki bari a bashi abinci yanzu nan zakiga ya nutsu”.
Cikin rashin fahimtar inda ya dosa ta ce, “Dadah dare ya fara, zan sha fruits kawai”.
“Shima wannan zaɓi ne na musamman ZAKAYANTA”.
Sunan ƙarshe ya motsa mata zuciya. Wani abu daya shuɗe yaso hasko mata kansa. Tadai danne bata nuna ba kamar yanda ta saba. Sai dai a gaban Dadah take. SOJA mafi ƙwarewa a fannin fiƙira da iya warware nakiya. Tsaff ya ga yanda sunan yay mata tasiri, yay mitsitsin murmushi, tare da ɗakko bowl dake saman table ɗin dake gabansu kusa da laptop ɗinsa. Buɗeshi yay ya ajiye gefe, ya ɗakko laptop ɗin sa yasa akan ƙafarsa dake ajiye ƙasa, dan Nimrah na'a tsakkiyar ƙafafun nasa ne lafe tamkar mage. Bai janye hannunsa dake yawo a bayanta zuwa ƙugunta ba, da hannun damansa yay amfani da cokali mai yatsu biyu wajen tsiro fruit ɗin yakai bakinta. Babu musu ta buɗe ya saka mata. Sannan ya fara sarrafa laptop ɗinsa a haka.
Idonta na akan laptop ɗin, yanda yake typing da hannu ɗaya na ɗaukar hankalinta da birgeta matuƙa. Ga fruits yana bata, dan data cinye zai dakata ya ɗauka wani ya bata. Fin awa ɗaya da rabi harta gama shan fruits ɗin tuni barci ma ya ɗauketa sannan ya gama. Ya rufe laptop ɗin yana sauke ajiyar zuciya da ɗan firzar da iska. Sai kuma ya kalla Nimrah dake barci cikin kwanciyar hankali. Fuskarta tayi masa fresh tamkar sabuwar ciyawar dake fita a farkon damuna. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa, sai kuma ya shafa fuskar kaɗan.
Yaja wasu mintina yana kallonta, abubuwa a kanta na masa tariya. Wasu na tausayi, wasu na sha'awa, wasu na burgewa, kai harma dana mamaki. Yanda ta sake ɗan naɗe jikinta a cikin barci ya sashi fahimtar sanyi take ji. Ga agogo ma ya nuna 11pm. Sai kawai ya ɗauka remote ya kashe television ɗin, ya ajiye. Camak ta miƙe da ita kai kace wata babyn tallar kaya ce ya ɗauka.
Tamkar baya so yake sauke ta a gadon, kai sai ka ɗauka wani ɗan jinjinri yake ma wannan lallaɓar. Ƙamshin turarenta daya gama kashe masa jiki na sake bugarsa. Da ƙyar ya daure ya kwantar da ita ɗin ya gyara mata duvet tare da sumbatar goshinta sannan ya nufi bayi. Shirin barci yayi cikin ƴan mintuna sai gashi ya dawo. Komai ya kashe, ya dai-daita sanyin acn yanda bazai damesu ba sannan ya nufi gado shima ya kwanta a ɗayan gefenta. Ajiyar zuya ya sauke tare da godema UBANGIJI daya kaisu wannan lokaci......
~~~~~~~~~~~
“Wai yarinyar nan bazaki tsaya ba ko? Kin san kika bari na kamaki sai kin gayama mutanen garin ku”.
Cikin dariya Ruky dake ƙara tsallakawa bayan kujeru ta ce, “Sai ka yarda zakaje da ni to”.
Rasama abin cewa yayi. Ya jice lips yana sakin murmurshi. “Shike nan na yarda kawo”.
“Kuma ni zan buɗe”.
“Duk naji muje”.
“To ka jira anan na ɗakko hijjabi”.
Ta faɗa tana nufar bedroom da sauri. Baya ya take mata, kasancewar tana sauri ko ƙofar bata rufe ba. Da wannan damar ya samu ya shige ya maida ƙofar a hankali ya rufe. Cikin sanɗa ya isa gaban wardrobe da take tana neman hijjab mai tsaho da zata saka dan rigar jikinta tayi ƙarama sosai. Bazata iya zuwa sashen Mammah a haka ba.
Jin tsaiwar mutum a bayanta ta juyo da sauri. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta tura baki. “ALLAH naji tsoro”.
Cikin ɗage gira da muryar raɗa Ammar ya ce, “Tunda kin iya tsokana ba dole ki iya jin tsoro ba. Yanzu zaki bani kona cira?”.
“Ka cira fa?”.
Ido ɗaya ya kashe mata cike da shaƙiyanci ya amsa da, “Ba kayana bane?”.
Da sauri tai ƙoƙarin juya masa baya da faɗin, “Ni dai ba ruwa na”.
Riƙeta yay ya hanata juyawa, sai ma ya mannata a drawer ɗin sosai yay sama da hannayenta duk biyu a cikin hannunsa ɗaya. Duk da bata san mi yake shirin mata ba ta fara magiya cikin shagwaɓa.
“Daga baya kenan yarinya. Ke ce fa kika gayyatoni”. Yay maganar yana sauke ɗayan hannunsa a jikinta. Tafiyar tsutsa ya fara mata a hankali. Fahimtar inda ta saka key ɗin yake nufin isa da hannun nasa ido ya fara raina fata.
“Uncle ALLAH ban gayyato ka ba. Na tuba zan baka da kaina. Nama fasa binka ALLAH na haƙura”.
“Kin makaro ai”
Ya bata amsa hannunsa na sauka cikin rigar ta. Jikin Ruky ya fara rawar tsoro. Dan ita tunda abin can ya faru bala'in tsoron Ammar ɗin take. Shiyyasa bata yarda ko kwakwkwaran kiss ya sake mata ba.... Tunaninta ya tsaya cak, sakamakon saukar lips ɗinsa kan nata dai-dai hannunsa na gama shiga a rigar. Amma kuma maimakon ɗaukar key ɗin da yaje sai ya canja tasha.
Safiyar waccan ranar da ta shuɗe ya shiga dawo mata. Ta fara mutsu-mutsun son ƙwacewa. Amma ina tazo hannun maza. Dan sai da ya tabbatar ya mata tilis a wajen harta fara bada kai sannan ya ɗauketa suka bar wajen. Rawa jikinta yaso farawa ganin inda ya direta. Tai saurin yunƙurawa zata tashi yay mata rumfa da jikinsa.. Da gudu ta rufe idannunta dake cika da ƙwalla. Murya na rawa ta ce, “Uncle banfa da lafiya”.
“Nace zanyi wani abu ne?”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta kufce mata. Sai ta buɗe idanunta hawayen ciki suka zirara ta gefen kunne........✍️
85