Sashe 64
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
............“Uhmm ina jinki”.
“Dadah ni fa sai dai na baka na Mammah, ko su Uncle Ma'aruff da su Ammy. Kona Trouble Buddy da Small Mom da Mu'azz”.
“Su ne labari mafi ƙayatarwa a duniyata ai Little Shadd. Idan kika bani nasu kin gama bani labari mafi daraja a wajena”.
Karo na farko tayi murmushi, murmurshin daya saka zuciyarsa jin sanyi. Cikin ɗan fara sakin jiki dan an taɓo mata abinda take so itama ta ce, “To Dadah zaɓa, dana wa za'a fara?”.
Kai tsaye ya ce, “Mammah. Faɗa min sanda bana nan idan kunyi rashin ji ya Mammah take yi da ku? Tana zane ku?”.
Yanzu kam dariya Nimrah tayi mai sanyi, dan sosai haƙoranta suka bayyana amma bata ƙyalƙyala ba. Ta yunƙura zata tashi cike da zumuɗi ya maidata ya kwantar a jikinsa.
“A haka nake so”.
Bata damu ba ta ce, “Dadah mu fa ƴan gatan Mammah ne. Ko hararanmu bata taɓa yi ba. Ko su Uncle bata bari su dake mu. Ita ɗin UWA ce mai daraja, mai bada tarbiyya a nutse bada hayaniya ba. Mai nuna soyayya ta ainahi da bata gogewa a zuciyar ƴaƴa. Dadah bazaka gane wacece Mammah ba duk labarinta dazan baka. Shiyyasa idan na girma, na samu yara kamar su Mom ina son na zama uwa kamar Mammah na, dan itace duniyar kwailwayona a komai na rayuwa. Dadah wlhy na rantse maka ban taɓa son wani da irin son da nake ma Mammah da Ummana ba.”
Gaba ɗaya Nimrah ta gama zare ƙarfin Dadah batare data sani ba. Dan ita shirmen ƙuruciya yasa kai tsaye abinda ke zuciyarta take fitar masa. Ya lumshe idanunsa tare da buɗewa a lokaci guda. Wani ɗan kyalli mai kama da hawaye ya bayyana a cikinsu. Fuskarsa da guntun murmushi da matuƙar tausasawa ya furta, “Ai kin girma Little Tiger. In sha ALLAHU ke da Mammah da Umma duk ƴan aljanna ne....”
“Har da kai zamu shiga in sha ALLAHU. Sannan ni fa ban girma ba Dadah. Mammah tace ni da Ruky da Mu'azz duk yara ne. Ƙuruciya ta mana yawa tana mana addu'a taga munyi hankali...”
“Sai yaushe kenan zaku yi?”.
“Randa Mammah ta faɗa, dan itace kaɗai zata gane munyi hankali”.
Ƙaramar dariya ta suɓuce masa. Nimrah ta tashi da sauri tana kallonsa da mamaki. “Dadah dariya fa kayi. Ya rabbi”.
Dariyar ta sake bashi, ya kuma yi kamar ta ɗazun yana ja mata hanci. “Tabbas har yanzu Kiddo ɗin Kiddo ce”.
Cike da farin ciki itama ta ce, “Shima Dadah na Dadah ne. Sai na bama Ruky labari naga kayi dariya”.
Idanu kawai ya zuba mata, komai tayi birgeshi take, sannan nishaɗi yake saka shi da mantar da shi kowa da komai. Musamman idan tana cikin farin ciki yakan ji nutsuwa ta musamman...
“Dadah dan ALLAH ka kira min su Mammah”. Ta katse masa tunani.
“Ba yau ba, yanzu zamu je kiga Dubai ko baƙya so?”.
(Ai tun daren jiya naga Dubai) Ta faɗa cikin ƙunƙuni. A zahiri kam fuska ta shagwaɓe masa. Sarai ƙunƙunin ta sun shigar masa cikin kunne, yay dariya a zuciyarsa yana faɗin (Yarinyar nan bata ji. Wato ita taga Dubai daren jiya. Zako ki cigaba da ganinta dan na kawoki nan ne dan na sanar dake ita yanda ya kamata)..
Nimrah ta cigaba shagwaɓe ma Dadah kan ya kira mata Mammah da Ruƙayya. Amma ya ƙi kulata sai ma sakata yay ta shirya cikin kayan daya yay musu shopping ta online tare aka kawo. Tayi ƙyau sosai har ya kasa ɗauke ido a kanta. Duk da dai kallon ana yinsa ne cike da iko da basarwa. Ita kuma sai faman tura baki take a dole tayi fushi..
Komai bata ɗauka ba, daga ita sai wayarta data fitar a bag karo na farko, dan tana son tayi hotuna..
“Muje”.
Ya faɗa yana kama hannunta. Sai da suka fito ya rufe ɗakin har ma suka shiga lift sannan ya kalleta. (ALLAH yay miki albarka) Ya faɗa a zuciyarsa yana sake kauda idanunsa. Suna fitowa waje suka sami lafiyayyar mota na jiransu. Dan kai tsaye gabanta Dadah ya iso da ita, driver daya buɗe musu da sauri ya shiga gaishe su. Dadah ne kawai ya amsa masa a taƙaice. Boss Lady dai an kame fuska dan ana cikin guguwar fushi.
Koda ya shiga jikinsa ya matsota. Batare da ya kalleta ba ya ce, “Idan wannan fuskan bai saki ba sai na ajiye ki a hanya na wuce abina”.
Baki ta kuma turawa tare da lafewa a jikinsan. Daga nan shiru ya ratsa motar. Driver ya harbata a hankali saman lafiyayyen titin....
....★Tabbas Nimrah ta sake yarda Dubai ɗin Dubai ce. Dan wani gidan abinci daya gama haɗuwa suka fara zuwa. Kai da ganin yanda aka shirya musu kilataccen wajen acan sama dama tarbar da suka samu kasan yayi booking ne tun kan su iso. Wajen irin acan saman gini ɗin nan ne da suke iya ganin garin Dubai kusan gaba ɗayan sa. Takawa tai a hankali jikin glass da akaima wajen tamkar katanga ta tsaya, hannayenta duk biyu ta dafe a kansa ta lumshe idanu ta buɗe tare da sauke ajiyar zuciya saboda iska data buso mata mai ni'ima. Idanu Dadah dake bayanta can tsaye ya ɗan zuba mata, sai kuma ya tako har zuwa inda take ya tsaya a bayanta gab shima. Zabura ta ɗan so yi dan taji saukar nunfashinsa akan wiyanta ne kawai a bazata. Amma ya tareta da jikinsa yana sauke nasa hannun shima akan galashin yana kallon abinda take kallo. Ruwa ne daga fountain dake can gefe yana tashi sama da komawa cikin bada sautin. Bai ce komai ba ya ɗauke idanunsa.
Hakan yayi dai-dai da sake tsallen ruwan a jere sama sosai. Cike da ƙarfin hali Nimrah ta furta, “Beautiful…” tai maganar a hankali tana wani lumshe idanu.
Dadah ya ɗan saki mitsitsin murmushi tare da matsar da fuskarsa kan wiyanta. Lips ɗinsa kusa da kunenta hannunsa na sauka saman ƙugunta cike da basarwa ya bata amsa da,
“Yeah… very beautiful.”
Bazata iya jurema salon nasa ba, dole ta juyo gaba ɗayanta, ta koma fuskantarsa bayanta ya jingina da gilashin. Dadah da shima yanda tai ɗin yazo masa a bazata sai ya zuba mata wani kalar kallo. Ganin kallon da yake mata ta ɗan daburce, gashi babu wajen fita saboda ya tare ko ina. Kanta ta kawar cike da kunya zata sake juya mata bayan, dan kai tsaye ta fahimci shi da ita yake ba ruwan ba.
Bai barta ba, sai ma sake matse ta da yay tare da kamo haɓarta ya maido fuskar inda take. “Da ace duniya biyu ce, da tuni na ɗauke ki na gudu dake a mafi zama sirri mu rayu mu kaɗai”.
Kanta ta kife a ƙirjinsa tana murmurshi. Cikin dauriya ta ce, “Ga aljanna Dadah”.
Idanu ya wani lumshe da sauke hannunsa a bayanta. Cikin ɗan bubbugawa ya ce, “Yess AMANAR HAYSAM. In sha ALLAHU can ta musamman ce. Oya zo kici abinci ƙar ya huce, ko yawon a iya nan ya isa?”.
“A'a ina son naje da yawa”.
“Uhmm Babyn shagali. Anya sati biyun nan basu mana kaɗan ba ma?”.
Yay maganar yana sumbatar kanta. Dariya tayi kaɗan tana ɗagowa. Bata yarda ta kallesa ba ganin ya bata hanya tabar wajen zuwa inda aka shirya musu abincin. Sai da ta zauna da fin mintina uku sannan ya tako ya iso. Abincin take bubbuɗewa, shi ko ya zauna kawai ya zuba mata idanu ƙasa-ƙasa...
Sun ci sun sha cike da farin ciki, daga nan suka baro wajen. Wani ruwa suka iso matuƙar ƙaton gaske. Wajen yayi sanyi, duk da akwai mutane jefi-jefi babu yawan hayaniya sam. Nimrah ta sake susucewa sai faɗin, “Woow” take. Tana son ruwa matuƙa. Balle kuma irin wannan da bata taɓa gani ba. Dadah dai na tsaye kawai can nesa kaɗan da ita hannayen sa duk a aljihu yana kallon ta. Irin ɗan turowa baya ruwan yayi, sai ta tsillo da gudu. Dadah ya ɗan kauda ido a kanta yana murmurshi. Bayansa taje ta shige, sai kace tana ɓoyema ruwan ne.
Har gaban inda Dadah yake sai da ruwan ya iso. Abin sai ya ƙara birge Nimrah, a hankali ta baro bayan sa ta tsuguna tana taɓa ruwan. Murmurshi mai armashi na ƙara ƙayata fuskarta. Hannunsa dake cikin aljihu ya cire ɗaya, ya ɗan rankwafa kaɗan ya ɗiba ruwa ya watsa mata...
“Dadah!”
ta faɗa tana zabura da sauke ajiyar zuciya.
Kaucewa ya ɗanyi kamar bashi yayi ba cike da basarwa.
Ta bishi da kallo. Sai kuma ta ɗibo itama cikin dariya ta yarfa masa kaɗan. Zata gudu ya damƙota.
Dariya take yi sosai tana faɗin, “Wayyo Dadah! kai ne fa ka fara tsokanata.”
Ya ɗan karkata kansa yana kallonta. Maimakon bata amsar zancenta sai ya furta. “Ki daina gudu.” ya faɗa a hankali tare da sakin hannun nata ya zagayeta yabar wajen. Sai da ya gota ta sannan ya saki murmushi.
Fuskarta ɗauke da murmushi itama ta bishi da kallo. Kamar ance ya juyo ya ɗan waiwayo, suna haɗa ido ta saka hannu ta rufe fuskarta cike da jin kunya.
“A tafi?”.
Kanta ta girgiza alamar a'a.
“Kar ruwan ya sa ki kamu da mura fa”.
“Dadah basai ka bani magani ba”.
“Kin san ko ina da magani na musamman”.
Cikin rashin fahimta ta ce, “Dadah ka zama likita kenan”.
“Likitan Little Shadow kawai ba”.
Sam Nimrah ba fahimtar inda kalaman Dadah sukai tayi ba. Dan haka tai dariya kawai.........✍️
80