← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 113

Sashe 109

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      ...★ Koda Kawu Tanimu ya shiga ya samu Nimrah na kula rurus Kulu na lallashinta. Da sassarfa ya ida shigowa inda suke yana tambayar “Miya faru?”.
      Kulu dake ɗan bubbuga bayanta tai murmurshi. “Kukan ganinka ne har yanzu dai”.
         Hawayen da shima suka cika masa idanun ya share. Kafin ya ƙaraso gab da su ya kamata ya ɗago daga jikin Kulu. Muryarsa na rawa ya ce, “Kiyi haƙuri Nimrah ki yafe min. Tabbas ni mai laifi ne a gareki, amma na dolene. Ya zame min dole nayi nisa dake in har ina son ki rayu cikin salama nima na rayu. Sannan inda kike nayi imanin yafi tsaro da kwanciyar hankali a gareki fiye da wajena. Na yarda da zuri'ar da kike ciki ɗari bisa ɗari”.
         Sam Nimrah ta kasa magana. Ga hawaye sun kasa tsaya mata. Sai da Kulu ta katse yanayin nasu da faɗin. “Inaga kuyi haƙuri daga baya duk a tattauna wannan. An bar su su kaɗai acan.”
      Cikin gamsuwa da maganar ta suka kwaso kayan abincin suka fara fitowa da su. Kawu Tanimu kuma ya ƙarasa inda su Mammah suke. Cikin girmamawa ya gaishe su. Sannan ya shiga jera godiya akan alkairin su ga Nimrah.
       Mammah ta katse shi da faɗin, “Ni gaba ɗaya kun sani a duhu ne ɗan nan. Kai waye a wajen yarinyata. Sannan kai waye a wajen Kulu?. Ranar juma'a ɗin nan fa Kulu ta tafi gida dan ta huta kamar yanda suka saba duk bayan sati biyu. Sai kuma nazo na ganta anan maimakon gidan dana sani take”.
        “Kiyi haƙuri Mammah. Ku ci abinci in sha ALLAHU komai zan warware muku yanda yake. Abinda kawai zance miki yanzu shine Nimrah jinina ce. Kulu kuwa MATATA ce”.
       “Mata!?”.
    Cewar Gwaggo Khadijah. Yayinda Nimrah dake taya Kulu shirya abinci a gabansu Mammah ta ɗago itama tana kallon Kawun nata. Sai kuma ta kalli Kulu dake murmushi cike da kunyar su Mammah.....

         \×\×\×\×\×\×\×\

    Anan ƙunguyar Duhu bayan kai ruwa rana da ka-ce-na-ce daya nema girgiza ƙungiya daga ƙarshe dai an zaɓi Mr Specter matsayin shugaba. A zahiri dai kowa yayi mubaya'a. Sai dai ta ciki na ciki kowa da nashi ƙullun. Sun amince ne kawai dan samun nasarar yaƙar su Zak-Shadow a yanzu. Acewarsu idan an gama da wannan wasan dolene ayi sabon wasan cikin gida.
        Bayan ƙaddamar da rantsuwa ga shugaba tare da alƙawarin daya ɗauka na bama kungiya duk abinda take buƙata da ƙarfinsa da basirarsa har ma da dukiyarsa aka bama Mr Iron Frong mataimaki. Daga haka akaci aka sha kamar yanda suka shirya. Sannan aka kashe fitilar na tsawon mintina goma ɗakin yay shiru. Wannan girmamwace ga Oga Jush dake a ƙaton hoto a bangon ɗakin. Dan fitilar hoton nashi ce kawai ke haska ɗakin a wannan lokacin.
      Bayan cikar lokaci aka kunna. Scythe ya tashi yay bayani kamar haka.
        “Yanzu ne yaƙi na gaskiya zai fara. Sabbin shirye-shirye ma zasu fara. Sai dai bamu da isashen lokaci. Dan kuwa abubuwa ne barjat a gabammu da bazasu lissafu ba. Yanzu dai na farko shine. Farautar Zak-Shadow ta hanyar yarinyar nan. Mun kammala shirya komai a yanzu haka. A yau kuma saƙon zai isa hannunta. Idan har ta saka masa abinda zamu aika matan dukkan motsinsa zai koma ne a tafin hannun mu. Ta hakanne zamu san duk wani ƙulle-ƙullensa. Sannan mu gano ainahin makircinsa, idan ma shine keda hannu a kisan Oga idan ma ba shi bane”.
     Ji kake taf-raf tafi na tashi. Bayan kusan mintuna goma aka miƙa ƙyaƙyƙyawan gift ga Dagger, suka tabbatar masa a yau ɗin nan ya isa ga Nimrah. Hannu biyu ya saka ya amsa babu gardama. Dan ya shirya yanzu duk abinda suka saka shi zai yi. Sai dai daga ƙarshe yana da nashi lissafin. Burinsa dai su dawo tafin hannunsa, sannan Nimrah ta dawo gare shi...

       Ana tashi daga meeting ɗin kai tsaye ya canja shiga zuwa ta ɓurtu ya nufo gidan su Dadah. Yana daga can nesa da gidan a mashin ɗin masu delivery Dadah ya fice da su Nimrah gidan Kawu Tanimu. Da wannan damar ya ƙaraso gate ɗin wajen. Yay knocking gate ɗin aka buɗe masa. Mole na ganin shine ya rikice. Amma sai Dagger yay masa raɗa da faɗin, “Dalla wawa ka nutsu”.
      Badan Mole yaji gamsuwa ba ya nutsun. Dagger ya bashi saƙon hana ciro littafi irin kamar na masu delivery ɗin da gaske yace ya saka hannu. Dariya ya bama Mole. Amma ya dake ya amshi biron ya zana haukarsa ya miƙa masa. Daga haka babu wata magana ya koma kan mashin ɗinsa ya haye.
       A fili Malam Buba ya furta, “Shege Oga an iya makirci.”
      Daga haka ya ƙarasa sashen Nimrah. Knocking yayi har sau uku. Har zai juya sai ga Nanah ta zo ta buɗe. Bayan ta gaishe shi a ɗage bai damu ba ya miƙa mata. “Saƙo ne ki ajiye ma Hajiya Nimrah”.
      Kamar Nanah tace baza amsa ba sai kuma dai ta amsa. Koda ta maida ƙofar ta rufe sai ta ajiye shi anan babban falo taje ta cigaba da aikinta. Daman abinci ne Hajiya Nabeeha tace tai mata zata je asibiti da shi, dan su Ismat ba nan gidan suka zo ba can suka je yin wankan kamar yanda Jiddah ta basu shawara saboda yafi kusa da asibitin. Nabeeha kam gargaɗin Dadah na ɗazun ya hanata komawa asibitin. Duk da dai tayi shiri bayan tasha maganin zazzaɓi ta je dan ta sanar masa Nanah ke gaya mata ya fita, sai dai da yake bata san da Nimrah da Mammah ya fita ɗin ba bata sanar mata wannan ba. Daga nan ne ma tace tai mata abincin ita kuma ta koma ta kwanta tana tsumayen dawowar Dadan.

        <<<<<%>>>>>

   Duk betar nan ta abinci da aka shirya musu bata ciyu ba saboda yanda su Mammah ke a matse da son jin yanda aka faɗi a ragaya, musamman zaman Kulu a gidansu. Da yanda bata taɓa nuna akwai alaƙa tsakaninta da Nimrah ba.
     Dole Kawu Tanimu ya gyara zama. “Zan fara muku daga tushe domin kusan wacece Nimrah itama tasan wacece ita.”
       Cikin gamsuwa Daddy Imran yace, “Hakan shine dai-dai.”
     Zama Kawu Tanimu ya gyara, hakama Nimrah da take jin zumuɗi fiye da kowa.
      “Kamar yanda kuka sani asalinmu ƴan garin Bankaura ne dake wata ƙaramar hukuma a jihar Sillire. Anan aka haifi kakanin mu, suka haifi iyayenmu. Sunan kakanmu Muhammadu ne, ya haifi yara biyar a duniya duk maza. Mahaifinmu Dalha shine babba. Sai dai suna kiransa da suna Tsalha. Sai ƙannesa huɗu. Kamar yanda al'adar ƙauyenmu take yaro nakai wasu shekaru da basu wuce ashirin ba ake masa aure, kuma yakan ja ɗaki ne a gidansu ya ajiye matar. Shiyyasa da yawanmu muka kansace muna rayuwa ne a family house. Hakance takasance da iyayenmu suma. Sunyi aure a ƙarancin shekaru su duka huɗu. Kuma duk anan gidan suke da iyalansu. Sai dai kowa da sashensa. Sai autansu daya rage. Sun fara haihuwarmu kusan bi da bi, sai dai mahaifiyarmu itace ta fara haihuwar ɗan uwana. Daga nan bata sake ba shiru kusan shekara biyar sai ga cikina nima. Kowa yayi farin ciki mara misali musamman ma mahaifinmu da kakaninmu. Dan kullum facalolonta cikin mata gori suke. Ciki ya girma, an kuma haifoni tubarkalla Masha ALLAH. Gida ya sake ɗaukar farin ciki biyu, dan lokacin ana shirin auren autan su Babanmu ne. Dan haka aka haɗa da shagalin biki da sunana rana ɗaya. Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin farin ciki duk da Inna bata sake haihuwa ba daga nan. Haka ma matar autan su Babanmu da muke kira Kawu Nura shiru kake ji. Har ALLAH yasa nakai shekara goma. A lokacin ne Kakanmu yace dole fa Auta ya sake aure, amma sai yaƙi. Acewar sa ai Babanmu shekara nawa bai haihu ba babu wanda ya takura masa sai shi. Gaskiya bazai yi ba yana son matarsa. An zauna an masa bayani ita Inna ai ta haifi yayana sannan haihuwar ta dakata, kuma shekara biyar ne, shiko tashi matar ko ɓatan wata bata taɓa ba shekara goma sha ɗaya da aure. Gata ƴar jaraba ta addabi kowa a gida da gulma da munafunci da neman faɗa..........✍️
124
Chapter 109 · 0% Book details