Sashe 63
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........Tunda suka shiga domin kwanciya gabanta ke faɗuwa. Tana dai dakewa ne, amma sai take ji kamar Uncle Bilal ya gane tayi wanka ne fa. Koda ya fito wanka yace taje tayi sumi-sumi ta wuce tana ɗan satar kallonsa ta gefen ido. Amma sai taga shi hankalinsa ba'a wajenta yake ba. Sai dai abinda bata sani ba ta cikin mirror yake binta da kallo. Sannan tun suna falo ya tsargu da yanda take ya faman ƙunshe gashi. Sai da ta shige ne ya juyo ya ɗan zubama ƙofar idanu.
“Yarinyar nan kamar tana ɓoye wani abu”.
Ya faɗa yana jinjina kai cikin jin gamsuwa da nazarinsa. Sai kuma ya juya ya fara gyara jikinsa kawai.
Asma'u na wanka tana addu'a, bayan ta kammala kayan data maƙalo ta saka tun daga bayin bayan ta goge jikinta da ƙyau. A hakan ma ta jima gaban mirror dake bayin tana kallon kanta da gyara wuyan rigar duk da ƙarami ne, kuma kayan basu matseta ba. Hasalima wando da riga ne masu faɗi sosai ta yanda babu inda ake iya ganin jikinta. Amma rashin sabo yasa ta kasa fitowa. Faɗan da wani sashe na zuciyarta ke mata ya sata ajiye komai ta fito kawai. Ganin babu Bilal a ɗakin ta sauke ajiyar zuciya da fatan yama koma ɗayan ɗakin ya kwanta. Sauri-sauri ta saka turare ta haye gado ta kwanta. Tama fi mintuna biyar da kwanciyar sannan taji motsin buɗe ƙofa. Ido ta runtse tana mai jin bugawar zuciya, dan tasan dole abinda bata son dai kenan. Wato kwanansa a ɗakin.
Tana wannan tunanin ya hawo gadon. Ai hatta nunfashinta riƙe shi tai ta yanda baya fita da sauri. Jin shiru bai matso kusa da ita ba yasa tai tunanin ya kwanta ne. Sai ta ɗan buɗe ido kaɗan. Tamkar ya shirya mata ne kawai ya haske ta da fitilar wayarsa. Babu shiri ta maida idanun ta rufe, shi kuma ya ajiye wayar yana kaiwa kwance...
“Sorry na zata kina barci ne ai”.
Kasa masa magana tayi, shima kuma bai damu ba, dan matsowa ma yay fuskarsa gab da tata. “Kiyi mana addu'a”. Ya faɗa cike da raɗa. Kanta ta jinjina masa. Batai musu ba ta fara addu'ar yanda ya buƙata, sai da ta shafa a jikinta sai kuma ta rasa shin ya zatai da shi? Tana wannan tunanin kawai taji ya kamo hannun nata yana shafama jikinsa. Kunya ta kamata, sai dai bata ƙwace ba har ya kammala. Yana sakar mata hannun ta sauke numfashi, sai kuma ta riƙe shi a ƙirji jin saukar nashi hannun kan hular dake kanta. Zare ta yay a hankali, ya tura yatsunsa cikin gashin ta yanda zuciyar Asma'u tai tsallen tsalli watsanga kamar zata zubo.
“Baki tsoron mura kikai wanka a shower ba hula?”.
A yanda yay tambayar sai Asma'u taga kamar bai gane abinda take gudun ba. Sai ta kama hannun nasa zata janye da faɗin, “Na manta ne, amma ai bai shiga ma ciki ba”.
“Karki damu, yanzu zan samar da dalilin da zai sa ya ƙara shiga ɗin da ƙyau.”
“Kamar ya?”.
Ta faɗa a tsorace.
“Kamar haka Asmah”.
Ya bata amsa yana kaima lips ɗinta cafka. Hannu tai saurin kawai zata tare. Ya riƙe shi kawai yana sauke lips ɗin nasa a kan nata.
Duk da a tsorace take da farko ta ɗauka iya irin na jiya za'a tsaya. Duk da shima ta sha wahala mai sauƙi ne ai. Amma ina hasashen nata bai gama kaiwa ƙarshe ba taga labarin ya fara canja salo. Dan sam tafiyar ba irin ta jiya bace ba. Wannan salonta na manya ne, kuma da zafinsa yake.
Ture shi ta fara yi jin ana neman rabata da rigarta. Ya riƙe hannun a cikin nashi, kafin ya rungumeta tsam-tsam yana cigaba da bata sumaba a waya. A haka yaje cikin kunenta yana faɗin, “Ki bani damar zama mutumin da zai cire miki wannan kunyar, ba da gaggawa ba, sai da tausayi.”
“Uncle ina fa...f..fash...”
“No Asma'u. Ki daina ɓoye min kanki haka, ni ɗin nan naki ne. Ba zan taɓa kallonki da wani ido ba face na ƙauna da gaskiya. Ki yarda nasan kinyi free”.
“To Amma ai....”
Bai bari ta faɗa ba ya sake rufe bakin ruf. Cike da nutsuwa da kulawa yake sarrafata. Ita ko jiki na ɓari na tsoro da tashin hankali. Sanda ya gama rabata da kayan jikinta ai takai wuya kuka kawai take shirin saki. Wani salon daya kauda kukan nata da hankalinta a ƙanƙanin lokaci ya fara mata, sai kuma ta fara miƙa wuya da sallamawa. Sai da ya bari ya gama karɓe dukkan ƙarfinta ta sallama masa ya maidata a ajin dake bada muhimmin darasi mai wargaje komai. Daga nan fa aka koma neman ceto sai dai bakin alƙalami ya rigada ya bushe. Uncle Villah ya rantse yau sai ya mallaki ƴar Asamah.
Alƙawarin ALLAH kuwa ya cika. Dare mafi daraja ya shiga cikin tarihin da zukata bazasu iya mantawa ba ga Asma'u da Uncle Bilal......
^^^^^^^^^^^^
Kamar yanda Mammah ta bada umarni su Ma'aruff basu tsallake ba. Dole suka ɗauketa ita da Gwaggo Khadijah da su Shariffa zuwa asibitin da aka kwantar da Nabeeha. Da su Ismat suka tafi, saboda anyi sa'a suma sun fito da shirin tafiya asibitin ne. Ai ko tamkar Ismat ta zuba ruwa a ƙasa ta sha yau gata ya Uncle Ja'afar. Sai wani biyayya take ma Mammah.
Ita ta fara gaishe su kafin su Amima dake yatsine-yatsine. Mammah bata nuna tama san mi suke yi ba balle Gwaggo Khadijah. Su Ma'aruff kam takaici kamar zai kashe su dan haushi. Sai dai sun san sunayin magana yanzu nan Mammah zatace ba haka ba, dan haka suka ja bakinsu sukai shiru.
Yanda Ismat ke bin Ja'afar da kallon ƙurilla yasa Lailah tsarguwa. Sai dai batai magana ba har suka iso asibitin. Kusan tare suka fito. Su Amimah ɗin a gaba su kuma biye da su tunda basu san waje ba. Amma sai Ismat ta koma kusa da Ja'afar dake ɗauke da Baby Khadijah suka jera a kaikaice. Da ƙyar ta danne, cikin dabara itama ta koma kusa da mijinta sai kuma Ismat tasha jinin jikinta tai ɗan baya kaɗan. A haka suka ƙarasa ɗakin da Nabeeha take.
Hajiya Hasiba ce kawai zaune, sai Nabeeha kwance idanunta a rufe. Tun suna hanya Rayhana ta turama Hajiya Hasiba text message. Dan haka suna yin sallama ta sake haɗe fuska. Da ƙyar su Shariffa da su Ja'afar suka danne zukatansu. Dan tun a sallamar farko suka fahimci hakan. A daƙile ta amsa musu gaisuwa. Koda suka tambayi mai jiki sai tace barci take yi. Alhalin duk wanda ya kalla Nabeeha ɗin ya san ido kawai ta rufe ba barci take ba.
Gwaggo Khadijah taso yin magana Mammah ta riƙe hannunta alamar kar tace komai. Dole tai shiru badan taso haka ba. Su Ma'aruff ma dai sai gargaɗarsu take da ido. Tasan su Lailah daman bazasu yi abinda bata so ba. Sun ajiye abincin da suka zo da shi sukai mata fatan samun lafiya sukai musu sallama suka fito....
“Munafukai”.
Nabeeha ta buɗe idanunta tana faɗa da raka bayan su Mammah da harara.
Cike da son tunzurawa Rayhana ta amshe da, “Ƙara da ƴan sa ido. Dole dai sai anzo an miki kallon ƙwaf. Kurwarki kurr, dan ni wlhy kama ma da mayya wannan baƙuwar tsohuwar tasu ke min (Gwaggo Khadijah 😭).
“Wama ya sani ko mayyar ce”.
Cewar Hajiya Hasiba. Sai itama ta shiga zagin su Ma'aruff da aibanta Mammah. Amimah da Rayhana kawai ke tayata, ita kuma Nabeeha na binsu da tsaki. Ita dai Ismat tayi shiru sai dai ta ɓata fuska. A haka Jiddah ta shigo ta same su. Jin suna ta faɗe-faɗe ta tambaya lafiya? Dan bata ga su Mammah ba ita. Da farko su Rayhana sun so ɓoye mata, amma sai Ismat ta gaya mata. Ran Jiddah ya ɓaci sosai itama. Ina laifin wanda suka zo duba ka to?. Komai batace ba saboda bata da farin jini wajen Momyn tasu. Ita kuma bata son zama sanadin ɓacin ran kowa sai tace, “ALLAH ya ƙyauta. Yanzu ya kukai da Doctor ɗin?”.
Ta kawar da zancen. Suma basu sake tayarwa ba suka maida hankalinsu ga mata bayanin yace nan da gobe zai sallameta idan ta kwantar da hankalinta. Dan jinjin nata ya hau sosai sosai.....
∆∆∆∆∆∆∆∆∆
Anan Dubai bayan sun idar da sallar la'asar kamar yanda sukai Azhar Dadah ya miƙama Nimrah hannu alamar tazo gare shi. Babu musu ta matsa inda yake, dama ba wani nisa ne da su a zaman sallar ba. Hijjab ɗinta ya cire, ya jiginata da jikinsa. Kaɗan ta sauke ajiyar zuciya, dan tana matuƙar son shiga wannan jikin mai bata tsoro, ita babbar tafiya ce bata so.
Hannunayenta da take cuɗawa a cikin na juna ya kamo ya riƙe, idonsa akan fuskarta mai ɗaukar hankali da shiga rai.
“Ki min labari mana, bana son na ganki shiru ɗin nan Little One..”
Kafaɗa ta maƙe masa. Fuskarsa ta ɗan motsa kamar zai yi murmurshi amma baiyi ba. Sai shafa tata fuskar da yay tare da sumbatar goshinta.
“Shike nan, tunda bazaki min labarin ba na fasa kai ki yawon...”
“To zanyi”.
Ta faɗa a sanyaye tana ƙara shige masa jiki cike da shagwaɓa. Yanzu kam murmurshi yayi sosai, ya sumbaci hannunta dake cikin nashi.
“To bani labari”.
“Dadah ban san nami ba ai?”.
“Na komai ma ina so”.
Shiru ta ɗanyi alamar tunani. Sai kuma ta ɗan ɗago ido ta kallesa. Ganin shima kallonta take ta janye natan da sauri..........✍️
79