Sashe 103
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
........A hankali Nimrah tai sallama tare da tura ƙofar. Aka Dadah idannunta suka fara sauka. Zaune yake a falon cikin kujera mai zaman mutum biyu. Jikinsa sanye da ƙananun kaya marasa nauyi, daga wandon har rigar duk baƙaƙe ne, hakan yasa hasken fatarsa bayyana sosai cikin idanun mai kallonsa. Tunda tai sallama ya kauda idanunsa a takardun dake hannunsa ya zuba mata su, hakan ya sakata ɗan son daburcewa, amma dai tai dauriyar dakewa tana mai cigaba da takowa inda yake.
“Sannu Dadah”.
Ta faɗa a hankali tana ajiye basket ɗin hannunta. Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya ɗauke idanun nasa a kanta ya maida kan wayarsa dake vibrating. Sai da wayar ta kusa tsinkewa ya ɗaga, a hansfree ɗin daya sakata yasa taji muryar Daddy Imran. Guri ta samu ta zauna, sai da ya kammala wayar ta gaishe shi.
Kansa ya gyaɗa mata kawai.
Hakan ya ƙara sata jin yau manyan aljanun miskilancin ne a kusa. Sai itama ta sake nutsar da kanta dan wargi ma waje yake samu. Batare data sake magana ba ta niƙe da basket ɗin data shigo da shi ta nufi dinning. Tsaff ta shirya komai sannan ta dawo inda yake. Yana ganin ta juyo ya janye idanunsa daga kallon da yake mata. Ita ko da bata san yanayi ba ta ƙaraso, kanta a ƙasa ta ce, “Dadah ga breakfast ɗin”.
Agogon dake a tsintsiyar hannunsa ya kalla. Sai kuma ya ɗago ya kalleta, addu'a take a ranta kar yace ba yanzu zai ci ba, dan yunwa take ji burinta kawai taje ta zauna cin ɗanwakenta. Kamar ya karanci abinda ke a zuciyar tata sai ya miƙe kawai. Ai da sauri tai gaba. Ta gyara masa kujera tun kafin ya ƙaraso. Kafin ta shiga zuba masa sauƙaƙaƙƙen breakfast ɗin na sauri. Amma abin mamakin ƙamshinsa duk ya gauraye falon. Koda ya zauna baiyi magana ba harta gama ajiye komai a gabansa.
“Dadah bismillah”.
Ta faɗa tana jan kujera ta zauna itama. Cikin ɗan rawar hannu ta jawo kwanon ɗanwaken ta kawai ta hau ci. Da mamaki ya tsaya yana kallonta. Itako ko sanin ma yanayi batai ba harta fara kai lauma. Kafin kuma ta haɗiye wata ta tura wata.
“Kiddo. Are you okay?”.
“Eh Dadah, mika gani?”.
Ta faɗa tana cigaba da cin abincinta. Rasa ma abin sake cewa yayi, ya cigaba da kallon nata kawai. Ganin fa abin nata na gaske ne sai ya fara cin nashin a hankali yana cigaba da kallon nata kamar ya samu television. A wannan gaɓar Nimrah bata gane komai sai abinda ke gabanta. Sai gata cikin ƙanƙanin lokaci ta cinye ɗanwaken tas. Sai da taja ruwa ta sha ta ƙara jinta ƙat sannan ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Alhamdullahi ya arrahaman.” tai maganar tana kwanciya a table ɗin da sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido kamar mai barci.
Dadah dai al'ajabi ya hana shi ma magana. Abincin nasa yake ci kawai yana kallon ta. Sai da kira ya shigo wayarsa ne ya janye yana maidawa kanta. Dabo ne, dan haka ya ɗauki tissue paper ya ɗan goge lips ɗinsa, cikin ɗan gyara murya daya saka Nimrah ɗaga idanunta kaɗan ta kallesa, sai kuma ta maida abinta ta lumshe. Shi dai ya ɗauki wayar dake gab da katsewa ya kai ta kunen.
Dabo ya gaishe shi da girmamawa, kafin ya ɗora da faɗin, “Alhamdullahi Komai yana tafiya dai-dai Sir. Yanzu haka gamu a wani guesthouse dake sabuwar anguwar lelorin. Kuma tabbas nan ya shiga. Da alama kuma maigadin gidan ya sanshi. Dan yana knocking gate ɗin ya leƙo yaga shine naga ya bashi hanya”.
“Good. Bamu da isasshen lokaci ka kira Faro zasu zo su sameka yanzun nan”.
“Okay Sir”.
Wayar Dadah ya ajiye, haɗewar fuskarsa na sassautawa. Wayar ya ajiye, hakan yayi dai-dai kuma da turo ƙofar da akai burum. Firgigit Nimrah ta farka daga ɗan barcin daya figeta, ta kai dubanta ga ƙofar. Yayinda Dadah yayi tamkar baiji ba.
Wani mahaluƙin baƙin ciki ya turniƙe Nabeeha. Tamkar wata kububuwar macijiya ta ƙaraso dinning ɗin kai tsaye. “Eh lallai abin naki ya fara kaiwa inda yakai yarinyar nan?. To na kula kam baki san zuru ba. Dan Kinga na miki kawaici ɗazun shine zaki cigaba da yi kenan?”.
Tamkar wata Baby doll sai Nimrah ta zubama Nabeeha dake masifa ido. Sai kuma ta tura baki gaba da faɗin, “Kai Aunty wai mi nayi?”.
“Uwarki kika yi, nace uwarki kaji min ƴar iskar yarinya. Koda yake ba laifinki bane ba. Laifin shi ne shi dake ɗaure miki ƙugu da biye miki. Kinga ga hanya nan kama gabanki. Kuma wlhy daga rana mai kama tayau kika ce zaki cigaba da shiga min hanci sai na fyatonki. Ki bari sai na gama rama kwanakina da kuka je kukayi kafin ki samu damar yin duk iskancin da kike jin kin iya ɗin. Dan haka ga hanya oya kafin raina ya ɓaci...”
Kallonta Nimrah tai cikin ido a karo na farko. Sai kawai tai wani ɗan mitsilin murmurshi batare da tace komai ba ta fara tattara kwanikan cikin basket ɗin. Sai dai banda wanda Dadah ke cin abinci. Sai da ta ɗauki basket ɗin curkuɗaɗɗiyar muryar Dadah da su dukansu ta nema saka su rikicewa ta daki kunnuwansu. Batare daya kalla kowacensu ba ya ce, “Koma ki zauna inda kike”.
Ba Nabeeha ba hatta Nimrah sai da taji zuciyarta ta tsarga. Ai ba musu madam Nimrah aka koma aka zauna. Wani mashahurin shakkar Dadah na kaɗa mata zuciya. Nabeeha kuwa data gama kaiwa wuya cikin ƙunar rai da sake aro jarumtar data tabbatar ma kanta yin ƙawance da ita a yanzu dan Dadah ya daina ɗauka tsoronsa take ji ta ce, “A gabanta kake so muyi kenan?. Amm.....”
Wani kalar kallo daya watso mata sai ga lips ɗin ta na rawa tama kasa ƙarasawa. Nimrah da ba ita akaima kallon ba kanta jitai hantar cikinta na ƙara kaɗawa. Tuni tai ƙasa da kanta barcin da take jin ya cika mata ido na rige-rigen guduwa. Ta zata Nabeeha zata cigaba da hayaƙin nata. Amma abin mamaki tayi tsitt tamkar wadda ruwa ya cinye a wajen. Shi ko ya sake maida hankali gacin abincin nasa tamkar ya manta da wanzuwar su su duka......
<<<<<%>>>>>
“Hubby abinci fa kusan kala goma ka lissafa. Su fa huɗu ne baƙin namu duk ina zasu kai shi?”.
“Duk cikin cikin su gimbiyata. Sannan abinda duk na lissafa miki abinda Zakanya ke matuƙar so ne kema kin sani. Tunda bayan wanda na sani ke kike gaya min sauran ai ko?”.
Cikin murmushi ta ce, “Haka ne. Bari muga ayi komai to yanda bazai yi yawa ba. Sannan dole shi Oga ai masa nasa dan nasan ba lallai yaci wannan ɗin ba. Dukkan abincinsa yana da tsari a sanin da nayi gaskiya”.
“Manya kenan iyayen gayya. Ai su dama nasu daban dana saura. Muje dan dole na taya ki waɗan nan aikin dan waje na ƙara ƙurewa. Duk da yace sai sunyi la'asar zasu fito”.
“Ai har a gama komai ma a nutse. Yanzu fa sha biyu saura ne”.
“To Alhamdullah muje.”
Sosai farin cikin mijin nata ke ƙara sakata jin zumuɗin yin komai fiye da yanda yake so. Babu ɓata lokaci suka fara komai a tare tana masa labarin da yafi so a rayuwarsa. Sai ko dariya yake cike da nishaɗi. Basuyi wani nisa ba kiran Faro ya katse shi. Yana ɗagawa abinda ya sanar masa ta sashi ajiye wuƙar daya ɗauka yana faɗin, “An gama Oga gani nan yanzun nan”.
Yay maganar yana cire rigar girkin daya sanya.
“Wani abu ya faru ne?”.
“Na gaggawa ma kuwa Maijiddah. Kinga bara naje ki cigaba kawai. In sha ALLAHU na tabbatar zan dawo kafin lokacin isowarsu”.
Sanin aikin nasu yasa bata damu ba. Musamman mijin nata da a yanzu ya sake samun sabon tsarin sirri da har yanzu bai buɗe mata komai a kanshi ba. Amma ta fahimci a ƙarƙashin wa aikin yake....
×=×=×=×=×=×=×
“Oh my God mutanen nan fa sun riga sun zagaye mu. Malam Almu. Baka da hankali ne kasan ana binka ka shigo gidan nan?. Ka manta gargaɗin da Oga yay maka a randa zaka fara aiki da mu?”.
Cikin rawa da karkarwar jiki Malam Almu ya shiga rantsuwa da faɗin, “Wlhy ban san da su ba Oga. Dan nima hankalina a tashe yake ne da tahowar Sanda. Na kira wayarka kuma a kashe shiyyasa nace bari nazo na sanar maka kada abin yayi nisa. Kuma wlhy har aka ajiyeni inda nake sauka ni banga kowa ba....”
Gaba ɗaya Oga yama kasa magana. Dan yasan kuma dai yau ƙarya ta ƙare. Wasan dila ya kai ƙarshe. Dan kalmar nan ta zame-zame baya hana mutuwa ta tabbata a gareshi. To amma ina Ojo ya shiga? Ko shima sun kama shi ne dai? Lallai dole ya sanar ma Ogansu kafin ya miƙa wuya. Dan bai sani ba ko bashi da buƙatar asan su ɗin na tare da shi a yanzu. Baya jin Baba. Dan yanzu haka idan yasan duk abinda ke faruwa da su bazai yi musu ba...........✍️
Tofa, bayan Baba akwai wani Oga kuma kenan? Ko kuma Oga da Baba duk abu ɗaya ne an sani a ragadada gaskiya🥱🏃🏼♀️.
118