Sashe 100
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Wai miyasa baƙya son kwana a gidan nan?”.
First Lady ta faɗa tana kallon Hajiya Hasiba dake saka wayarta a handbag. Murmurshi tayi tana zipping ɗin designer bag ɗin tata da aka saya da kuɗaɗe masu nauyi. Kafin ta juyo cike da salo irin na ƴan bariki ta dubeta. “Hajjajuna ba bana so bane. Kin san gobe akwai tafiya gabana. Ƙarfe uku jirgina zai tashi. Muna buƙatar kaya, ya kamata ai ƙoƙari a kawo”.
“Haka ne kuma. Shiyyasa bana jin ko ɗar, dan nasan ina tare da gwarzuwa a fannin sanin sirrin kasuwa. Ina ga ma idan kika dawo ɗin nan akwai wani business da nake son mu tattauna ko zamu gwada shi ma..”
“Mizai hana kuwa. Ai mu duk inda akace kuɗi bama wasa”.
Dariya suka sanya. Hajiya Hasiba ta miƙe tana mata sallama. Bata jira cewarta ba ta wuce. Dan tana son komawa ta bama driver mota ya ɗakko Mamawo a airport.
Sosai maganar First Lady akan sabon business ɗin nan tai mata daɗi. Duk da bata san wane kalar business bane ba. Gudun da tai ya sata isa gidan dan da nan. Maigadi ya buɗe mata gate ta shige. Kafin ya gama rufe gate ya zo ya mata bayanin baƙin da tayi har ta shige ciki..
Tana shigowa gabanta ya faɗi, sakamakon iske garadan maza har huɗu zaune, tsabar iskanci harda kunna television suna kallo.
“Su waye ku?”.
Ta faɗa a hasale.
Shiru babu wanda ya bata amsa. Zuciyarta ta ƙara zuwa wuya. Da mugun ƙaraji ta sake musu tambaya. Maimakon amsar su a yanzu ma sai sautin fito ta fara ji daga staircase. Cikin sauri ta ɗaga kai ta kalla wajen. Yayinda garadan duk suka miƙe suna gyara tsaiwarsu. Mamaki da tashin hankali a lokaci guda suka saukarma Hasiba. Tare da jin wani guguwar jiri mai tsinka jini har wuya. Kamar dutsi haka ta kasance tsaye har Adeel ya gama sakkowa. Wani mai irin kayan waɗanda ta tarar biye da shi da ƙatuwar akwatin documents ɗinta dama na Mamawo da yaransu kaf. Kai duk ma wani abu mai muhimmanci dake buƙatar ɓoyo a wannan akwatin Hajiya Hasiba ke saka shi. Dan harda kaf kayan adonta na zinari dana su Ismat.
Adeel ya kai zaune cikin kujera cike da izza. Kafin ya ɗage gira sama tare da bada umarnin buɗe akwatin yana kallonta.
Cikin ƙarfin hali ta yamutse fuska. Sai dai kafin tayi magana mai ɗauke da akwatin ya waskara mata mari. Sai gata ƙasa wanwar hannunta dafe da kuncin....
“Ki buɗe akace miki”.
“Mizai saka na buɗe tunda abinda ke ciki bai shafe ku b.....”
Bata gama faɗa ba ya kai mata shirun daya sakata sakin gigitacciyar ƙara. Dan hannun ta ya bi da takalminsa ya take. Sai ga ƙarar ƙashin yatsunta na fita alamar karaya.
“Har yanzu zaki cigaba da gardama?”.
Kanta ta shiga girgizawa hawaye na wanke mata fuska. Ga rawar jiki kamar wadda ke a gaban bindiga. Sunan Nabeeha ta saka, dan shine password ɗin. A take akwatin ta buɗe kuwa.
“Da kika ce kema shegiya ce”.
Yaron Adeel ɗin ya faɗa yana zuba mata harara. Akwatin yaja har gaban Adeel dake danna waya kamar bai san abinda ake ba.
“Sir gashi ta buɗe”
Batare da Adeel ya ɗago ba ko ajiye wayar ya ce, “Ka cire duk wani document dake da sunanta gefe kona ƴaƴanta”.
“Okay Sir”.
Kasancewar takardun da yawa dole ya zauna dirshan a carpet ɗin ya fara tantance su ɗaya bayan ɗaya. Hajiya Hasiba ko abu goma da ashirin ne ya mamaye ta. Ga azabar hannu gata tashin hankali. Tana son ta ciro waya ta kira First Lady tana jin tsoro......
««««∆»»»»
Tsohon sakanni Dadah na kallon Sanda cike da nazari. Kafin ya ɗauke kansa. Cikin bada umarni ya furta,
“Miye sunan ka?”.
“S.. s.... Sanda ne yallaɓai”.
“Ina ne garin ku?”.
“D... Dangarama”.
“Mi kaje yi cikin zuri'ata?”.
“Aikin bama flower ruwa”.
“Saɓanin abinda ka faɗa wane hukunci zan maka?”.
Shiru Sanda ya kasa magana yanzun kam. Cikin tsawa Faro da bai jima da zuwa ba ya ce, “Ba dakai ake ba? Ko sai kaji a jikinka?”.
“Ayi haƙuri ranka ya daɗe basai an kai nan ba. Duk abinda na faɗa haka yake”.
“Faro a cire masa mask ɗin fuskarsa”.
Dadah ya faɗa yana miƙewa tsaye. Hannayensa duka ya tura cikin aljihu. Ba Faro da su Dabo ba, hatta Daddy Imran sai da ya kalla Sanda. Dan harga ALLAH su kam babu wanda ya kawoma ransa hakan. A ɓanagaren aiki Faro mai jiran umarni ne da cikawa. A take ya bama Yusuf umarnin shima ya kawo masa kayan aiki..
Babu jimawa kuwa sai gashi da box babba. A gabansu ya dire, tare da bajesa a ƙasa wasu kalolin wuƙaƙe da almakashi dama nau'in ƙarfuna iri-iri suka bayyana. Kai daga gani kasan badan aikin lafiya aka ajesu ba. Sai dai azaba ga duk wanda ƙaddarar rashin gaskiya ta kawo shi hannunsu. Zaram Sanda ya miƙe. Zai yi magana Faro yasa kafa ya kwashe sa. Sai gashi a ƙasa wanwar.
“Kuyi haƙuri zan muku dukkan bayanin da kuke so na rantse”.
“Damarka ta riga ta ƙare ai”.
Faro ya faɗa yana liƙe masa baki. Yusuf kuwa ya bazar da shi. Dan in dai ƙarfi ne yaran Zak-Shadow babu rago. Duk da shima dai Sanda ɗin Masha ALLAH a girkensa yake.
Zama Dadah ya koma yayi, ya ɗauki system dake gefensa ya cigaba da aiki. Kusan mintina ashirin su Faro suka kammala.
“What!!!”.
Kalmar farko da Imran ya ambata ta saka Dadah dakatawa daga danna keyboard ɗin system da yake, sai dai bai ɗago idanunsa ba. Yayinda Yusuf da Dabo suka daka uban tsalle gefe suma suna faɗin, “Innalillahi...”
Faro kuwa kamar wanda aka dakama tsawa haka ya kasance shiru yana kallon Sanda da ya kasa motsin kirki. A hankali Dadah ya ɗago nashi idanun shima dan ganin mi suke ma wannan shirmen haka. Dan in ba shirme ba shi baiga abinda zai kira yanda sukai ɗin ba. Sai dai me, shi ma fa nashi idon na sauka akan Sanda ɗin komai ya tsaya masa cak. Girman idanunsa suka shiga zuƙewa saboda tsabar mamaki da yanda abin ya dake sa a zuciya...........✍️
Hummm tofa mutane na, waye wannan Sanda haka da ya zama mai abin mamaki har a wajen Dadah?
115
..........Sanda yay wani kalar ƙame jiki, tare da salute ɗin Dadah. Sai kuma ya sulale a hankali ya durƙushe ƙasa yay kneeling tare da rissinar da kansa, hannayensa duk biyu a bayansa.
“I'm sorry Si...r!”.
Ya faɗa da ƙyar muryarsa na rawa da kakkarwa. Ba Dadah kawai ba, hatta su Imran sun kasa magana tsahon lokaci. Dan tabbas idan suka ce al'amarin bai dake su ba sunyi ƙarya ma..
Faro da ke jin yafi kowa shiga rikici da jin an raina musu hankali ya kai ma Centre table wani kalar harbi tare da zaro bindiga yaja kunamarta kawai ya sauke saman kan Sanda. Sanda ya runmtse idanunsa da sukai mugun kaɗewa. Cikin ƙaraji Faro ya ce, “Mu kake tunanin zaka yaudara?”.
“Ba yaudara bace Oga”.
“You are very stupid”.
“I'm sorry, Sir”.
“Waye kai?”.
“Ojo”.
“You are lying. Waye kai da zakai mana wasa da hankali”.
“Wlhy Oga ni ne Ojo”.
“Shi kuma wancan fa?”.
“Jeo”.
“Taya ya zama Ojo?”.
“Makirci ya shirya min”.
Faro ya kai masa naushin da sai da ya zube ƙasa, bakinsa ya fashe. Binsa yay ya take, tare da maida bindigar kan ƙirjinsa.
Imran da yasan Faro ma akwai zuciyar tsiya ya miƙe a hankali. Inda suke ya ƙaraso, cikin lallashi ya kama Faro ɗin ya miƙar. Bayansa yake bubbugawa a hankali yana kallon Sanda ko muce Ojo dake huttan wahala. Ga gefen baki a fashe da jini.
Tsam Dadah ya miƙe, duk suka bishi da kallo. Batare da shi ya kallesu ba ya nufi ƙofa yana faɗin, “Ku bashi abinci. Ku tabbatar daga nan zuwa gobe an kama wancan”.
Cikin rawar jiki Ojo ya ce, “Boss Please ka saurare ni, kada kai fushi. Sannan wlhy ni kaɗai ne zan iya kama muku Jeo. Please Boss 20 minute....”
Sauran maganar ta maƙale saboda ficewar Dadah da ko kallonsa bai sake yi ba. Jikin su Dabo ya ƙara yin sanyi, dan sun tabbatar ran Boss a ɓace yake kam da gaske. Sai dai basu san miya ɓata masa ran ba. Musamman da suka san irin son da yake ma Ojo a baya. To amma idan ta gaskiya za'ai ko su a cikin ruɗani suke. Dan zuciyarsu ta kasa banbanta musu tsakanin wannan da wancan ɗin waye Ojo?. Duk da shi Dabo binciken Ojon a hannunsa yake ƙamanin sun sashi ƙaulani. To amma idan bai manta ba, mamansu tace akwai tabo daya banbanta su. Tabbas anyi haka. Ya kuma tabbatar da shi zasu banbanta Ojo da Jeo ɗin. To amma bari ya dakata yaga miye shirin Boss ɗin tukunna. Dan yasan komai yayi yana da dalili....
Kamar yanda Dadah ya bada umarni a bashi abincin shima Imran yace su Yusuf su kawo masa. Faro kam tunda ya koma gefe ya zauna bai sake magana ba....
>>>>>>%<<<<<
“Humm wai ka fahimci mutumin nan shugabancin nan yake so shima?”.
“Tunda ya fara magana na fahimci hakan Viper. Kai nifa zuciyata ma ta fara zarginsa gaskiya. Dan na jima da fahimtar Mr Specter yana son kujerar Oga. Ka manta randa mukai zaman nan da shi mu uku.”
“Ban manta ba, to amma miyasa kai kake zarginsa?”.
“Abunuwa da yawa. Kaima kuma inda zaka zauna ka nazarce su zaka gane abinda nake nufi. Yanzu dai kaima mizai hana ka fito a candidate ɗin?”.
Wani murmushin basanci Mr Scythe ya saki. Sai kuma ya ɗan karyar da kansa gefe. “Hakan zai iya tada ƙura. Dan Iron Frang ma kujerar yake hari. Ka barsu kawai muga nasu takun. Idan bai mana ba sai mu fito a mutum.”
“Tsoron su kake ji ne?”.
“Ba wani tsoro kai ma ka sani. Mu dai bi wannan tsarin dan akwai ƙura da zata iya biyo baya”.
“Shike nan, yanzu mu wa zamu zaɓa?”.
“Mr Specter mana”.
“Yayi”.
Viper ya faɗa yana haɗiye abinda ke riƙe da maƙoshinsa....
•===•==•==•===•