← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 113

Sashe 11

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Hhhhhh anayi muna shan shayi, to Adeel bari muga ko wasan naka zai zama abin kallo a gare mu🤣. Ƙasar dai idan bata tashi dan kai ba, to zata tashi da kai a ciki kuwa🥱🏃🏼‍♀️.
Received at 3:05 PM30

...........“Malam duk kabi ka rikita yaro da wannan kallon naka sai tsuma yake kamar mai tsutsar basir. ALLAH kai mugu ne”.
      Hararar Daddy Imran Dada yayi, tare da faɗin, “Kai ai duk duniya ba wanda ka raina sama dani. Ni ubansa ne da zai yi tsumar jiki a kaina? Tunda ni mugu ne kai ne na'ibina ai”.
      Dariya Imran ya shiga tuntsurawa. “ALLAH Serious a rikice yake. Ko Ammar ya sha jinin jikinsa ne shiyyasa yace suje.”
            “Su suka sani, amma tun wuri ka dakatar da shi zuwa gidan nan inba haka ba kuma huumm.....”
       “A'a yi haƙuri mu gara ka barshi yazo mu samu abinda muke so. Amma fa yanda Nabeeha ta razana yafi komai ɗaure mun kai, shima yanda yake kallonta kamar sun san juna.”
         Dada dake kallonsa ya ɗan ciza lips. Ga hannunsa ya dunƙule alamar fushi. Imran daya fahimci halin da yake ciki ya sauke numfashi da faɗin, “Relax! Zak... Mubi komai a sannu, in sha ALLAHU zan sabunta bincike akansa. Dan tabbas ina ji a jikina ba business ya kawo shi ƙasar nan ba kawai.”
       Idanu Dada ya lumshe tare da buɗesu a lokaci guda. Cikin ture zancen ya ce, “Ya ake ciki da yaran nan?”.
      Shima Daddy Imran sakin zancen yay kawai. Sai kuma ya miƙa masa takardu da ya ajiye gefensa. “Komai ya kammala. ALLAH ma yaso naje yau ɗin da an samu matsala. Dan gobe zasu rufe registration ɗin.”
      “Dama Auta ta faɗa ai. Yanzu dai tunda anyi Alhamdullah. Yaushe zasu fara exams ɗin?.”
        “Babu wani nisa nan da sati biyu ne”.
      “ALLAH yasa muna da rabon kaiwa. Haydar ya kira ka ne?”.
     “Humm kaga zan manta ba. Ya kirani yana sanar min kamar sun gano inda drivers ɗin nan suke fa, kuma suna zargin wanda muka sani ne Ogan su, bai wuce kuma Ojo ba. Sai dai basu tabbatar ba, gadai jami'an farin kaya zasu fita operation tare da Dabo”.
          “Ni bana jin wani shakkun shine.”
     “Kayi aiki a ɓoye kenan?”.
Murmurshi mai faɗi Dada ya saki amma bai ce komai ba. Imran dake murmurshin shima da jinjina kai ya ce, “Aljanancin ka na bani tsoro Haysam.”
        Dada bai ce komai ba nan ma. Dan haka Imran ya sake faɗin, “Malam Buba ya dawo ne?”.
       Kai Dada ya girgiza masa alamar a'a.
     “Kenan ta tabbata mutumin nan munafuki ne? Yanzu ta ina zamu fara?”.
         “Karka damu, zasu zo hannu cikin sauƙi. Yanzu haka akwai jami'an da nake son ya kasance kan aikin.”
       “Hakan yayi, sai office. Kasan dai ba fashi dole gobe idan ALLAH ya kaimu mu fara shiga”.
      “Humm wato Janar ko....?”.
   Dariya Imran ya sanya. “To ya muka iya, ya riga ya ɗaure mu, kuma tsarin yayi. ALLAH ya ɗora nasararmu akan tasu kawai....”
“Amin ya rabbi to”....

💦💦💦💦💦💦

         “Momy wlhy na shiga uku.....”
    “Kamar ya kin shiga uku Nabeeha? Ba sallama ba gaisuwa sai zance shiga uku. Nifa matsalata dake rashin hankali”.
       “Momy dole nake faɗar haka, Adeel ne fa a gidana.....”
     Wani kalar rikitowa Hajiya Hasiba tai daga samon gadonta. Sai kuma ta kalla First Lady dake kallonta dan suna tare ne a saman gadon. Ɗauke kai First Lady ɗin tayi, itama Hajiya Hasiba sai ta haɗiye busashen yawin dake neman yanka mata maƙoshi. Cikin tsargawar zuciya ta furta, “Adeel! Nabeeha ya akai Adeel yasan gidanki? Miya kawo shi kuma?”.
           Nabeeha ta share hawayen dake mata gudu. “Momy ban sani ba. Tare da wannan ƙanin Haysam ɗin suke Ammar. Kuma Haysam na nan dan yanzu haka a wajensa na baro shi. Wlhy Mammah ina son mijina, ina son rayuwar aurena. Idan na rabu da Haysam mutuwa zanyi. Ki taimakeni Momy, ki taimakeni kada Adeel ya lalata min aure na”.
       “Ki kwantar da hankalinki. Zuwa anjima zan kiraki. Shima kuma zan samesa a masaukinsa kinji.”
     “Mammah hankalina bazai taɓa kwanciya ba sai naga Adeel ya bar ƙasar nan na har abada”.
      “Kar ki damu zai barta. Ki saurare ni”.
    Ƙitt ta yanke kiran, Nabeeha ta zube ƙasa hawaye na cigaba da zuba mata. Wani makirin murmurshi Rayhana dake laɓe ta saki. Dan tabbas wannan shine babban makaminta a yanzu. Dan haka yanzu wasan zai fara......

✨✨✨✨✨✨
Received at 3:05 PMKullum daga shinkafa, sai taliya da tuwo a gidanki. A'a Hajiya Balki ai an wuce wannan ƙarnin tuni. Mata sun gane yanzu. Idan kuma kin tsaya kallon ruwa lallai kwaɗo zai miki ƙafa, dan kina ji kina gani mijinki zai koma bin gidajen abinci. Daga haka a barbaɗesa kuma😝, to ni dai ba ruwana🥱, na nuna muku hanyar da zata fishe ku. Wato Ramadan class na Chef Yakudima, bama sai Ramadan ba, ko yaushe ajinta na koyon girki abuɗe yake. Nima dai Bilyn Abdull banga ta zama ba. Dole naje domin sake damƙe Bawan ALLAHn nan Malam Audu a hannuna🤤. Chef Yakudima zo mu saka labule🚶.

×××××××××××

          “Ruky dan ALLAH ga abincin nan ki miƙama Uncle Ammar. Yace a bama Mu'azz ya kai masa kuma ban ganshi ba”.
      Kallon Mammah Ruƙayya tayi, dan tasan in har Uncle's ɗin nasu na ɗaki bata aiken su ciki. Dama shara ce ta safe ke kaisu. Idan har ka gansu da yamma ko da rana to su suna falo ne suka aike su ɗakko abu ko basa gidan Mammah ta aikesu, mafi yawancin lokaci ma sunfi saka Mu'azz. Jin batace komai ba, kuma bata miƙe ba Mammah ta kallesu, dai-dai itama Kulu ta buɗe baki zata sake magana sai tai shiru.
        “Amsa ki kai masa”.
   Cewar Mammah tana kallon Ruƙayya. Mamaki sosai ya kama Ruky, amma babu musu tsakaninsu da Mammah dan haka ta miƙe ta amsa ɗin...........✍️

Jama'a, karfa ku bari ayi bikin shagalin girke-girken online class na Chef Yakudima babu ku😘💃.
Chapter 11 · 0% Book details