← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 113

Sashe 96

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Rayhana na gama zayyane ma First Lady abinda ke faruwa a gidan dake nuna sakamakon aikin data sakata ta saki wata dariya. Wayar ta ajiye tare da miƙewa ta fara kai-kawo a katafaren ɗakin nata. “Lokaci yayi da Adeel zai dawo shima”. Ta faɗa a zahiri tana sake kwashewa da dariya.
     Sai kuma ta sake komawa bakin gado tai zaman ƙafa ɗaya kan ɗaya. Waya ta ɗauka tai kira. Ana ɗagawa cikin gaisuwar girmamawa ta ce, “Ranka ya daɗe na cika aikin ku. Shegen ya kai ƙasa tun a daren jiya. Sai muje next”.
Ban san mi akace mata daga can ba tai dariya da faɗin, “An gama, sai na jika”. Daga haka ta yanke tana dariyar dai. Kamar wadda ke magana da wani ta furta, “Wannan shine lokacin, lokacin da nake jira Hasiba. Nayi alƙawarin sai na mallaki abinda kikace yafi ƙarfina. Zan tabbatar miki ni ba kanwar lasarki bace, tun farko a bariki aka haifeni ba hayenta nayi ba kamar ke. Muje zuwa farkon wasa. Ni dake ɗan halak ka fasa.”
     Ta sake kwashewa da dariya. Tare da ware hannaye ta ce, “Barka da zuwa DUNIYATA NABEEHA. Barka da zuwa DUNIYAR HASIBA ADEEL. BARKA DA ZUWA DUNIYAR SU OGANA, HAYSAM”....

          Tofa munga Boni. Dole na kaima ƙawata gulmar nan yau. Gata ga uwataresa ga miji kuma duk a komar First Lady 🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🥱😂.

ππππππππππ

      Sam Nimrah ta kasa cin abincin da aka kawo daga sashen Mammah. Tadai cirema Dada ruwan lokacin da taga ya ƙare har ya fara ja masa jini. Tun tana zaman kallonsa da tune-tune iri-iri akansa musamman akan zantukan Dagger dana mutanen da sukai kidnapping ɗinta kwanaki har barci ya ɗauketa a bazata. Ƙasa take zaune saman carpet a gaban gadon, sai dai ta saka ƙaramin fillo na kujera yanda yay mata ɗan tudun da har take iya ganin Dadah da ƙyau. Hannunsa na dama data cire masa ruwa ta saka ƙaramar plaster yatsun riƙe a cikin nata. Kanta kwance akan katifar tana fuskantar shi.
       Daga yanda yake kwance ya buɗe idanunsa da sukai matuƙar nauyi a hankali. Cikin sa'a kuwa suka sauka akan fuskarta datai yanayi kamar mai shagwaɓa. Hakan na nuna kodai mafarki take, ko kuma ta kwanta da wani tunanin a ranta. Idanun ya runtse da ƙarfi, saboda wani irin kartawa da cikinsa yayi na ciwo, ga zafi da yake jin jikinsa na ƙara ɗauka. Sake jin matsar cikin ya sashi damƙe hannunta sosai cikin nashi. A zabure ta farka da faɗin, “Wayyo hannuna Ruky miye hak.....”
      Maganar ta maƙale ganin saɓanin Ruky data ambata dan mafarkinta take. Cikin ƙarfin hali da jarumta Dadah ya buɗe idanunsa yana sassauta mata riƙon. Idanunta data ɗan zuba masa ta kawar dan har wani yarrr take ji a jikinta sakamakon kallon da yake mata ga idanunsa jazur. Muryarta da sanyi da kuma rawa-rawa ta ce, “Sannu Dadah ya jikin?”.
          Kansa ya ɗan jinjina mata alamar da sauƙi, a ransa yana mamakin yaushe tazo ɗakin? Rashin mai bashi amsar ya sashi buɗe baki da ƙyar ya furta, “Bani ruwa”.
      Kamar abinda take jira kenan ta miƙe zaram tana cire hannunta dake cikin nashi har yanzu. Hannun nasa ya kalla shima. Cikin lumshe ido da cizar lips ya yunƙura ya tashi zaune. Sai dai gaba ɗaya cikinsa a takure yake a ɗaɗɗaure, har takai ya kasa zama da ƙyau, ya kuma kai hannunsa na haggu ya riƙe shi tare da ɗan duƙewa daga yanda take zaunen. A haka Nimrah data fita ta ɗakko ruwa a falonsa ta dawo ta sameshi, dan hankalinta ma bai kai a ƙaramin fright ɗin bedroom ɗin ba. Cikin ɗari-ɗari ta iso gabansa, sai dai a kallo ɗaya ta fahimci halin da yake ciki. Da sauri ta kai durƙushe a gabansa tana mai ɗora hannunta ɗaya a cinyarsa tare da leƙa fuskarsa da yanayin damuwa.
         “Dada har yanzu baka da lafiya?”.
     Bai iya bata amsa ba tsahon sakanni, sai ma sake runtse idanunsa da yake yi. Hankalinta ya sake tashi. Sai ta miƙe tana faɗin, “Na shiga uku Dadah bari na kira Daddy, dama yace idan ka farka na kira shi ya daw....”
          Bata kai ƙarshen zancen ba da barin wajen ya riƙota da ɗayan hannunsa. Kusa da shi ya zaunar da ita. Sai dai baiyi magana ba saboda halin da yake ciki. Hankalin Nimrah ya ƙara tashi, ganin yanda ya dafe ciki kawai takai hannunta saman cikin itama. Kamar jira yake sai ya kama hannun nata ya ɗora saman cikin nashi sannan ya maida nashi akan natan ya danne.
       Karan farko ta saki kuka tana ƙara matsowa jikinsa sosai. Cikin rufewar ido ta ɗora ɗayan hannun ta saman fuskarsa tana ƙoƙarin ɗagowa. Ita a dole sai taga yanayinsa. Jikinsa kawai ya ƙara jawota ya ɗora kan nasa a kafaɗarta. Kuka ta ƙara saki da ɗora hannunta akan bayansa tana faɗin, “Dadah dan ALLAH ka bari na kira Daddynmu ko Mammah. Wlhy jikinka zafi sosai. Na shiga uku Dadah mike damunka?”.
        Yanda sautin kukanta ke shiga har tsakkiyar ɓargon jikinsa da tsokar jini ya sashi sassauta mata riƙon yana aro jarumtar dole ya yafama kansa. Cikin dauriya ya ce, “Bani ruwan na sha..”
      Da sauri ta matsa daga jikinsa ta yakito ruwan ta ɓalle murfin. Dama bata ɗakko kofi ba, dan haka ta miƙa masa gorar. Shiru yay yana kallon ruwan kamar mai nazari. Sai kuma ya basar. Maimakon amsa sai ya buɗe mata baki alamar ta bashi. Babu musu ta saka masa akan baki. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama zuƙeshi tas yana sakin ajiyar zuciya. Itama ajiyar zuciyar take saki tamkar ita tasha ruwan. Sai kuma ta koma jera masa sannu. Fuskarta ya ɗan tsare da idanunsa yana sakar mata ƙaramin murmushi, sai kuma ya kai hannu ya share mata hawayen..
        “Kiddo bana son kuka. Kimin addu'a kawai na samu sauƙi”.
     Kanta ta jinjina masa. Sai kuma ta ce, “Dadah a kira Mammah?”.
      Kansa ya girgiza mata. “Karki kira kowa”.
          “Amma Dadah baka da lafiya fa. Jikinka kuma zafi sosai.”
     “Zai bari kimin addu'a kawai”.
Yay maganar yana zamewa ya sake kwanciya. Dai-dai nan wayar Nimrah ta hau tsuwwa alamar shigowar kira. Jiki a saɓule ta miƙe ɗaukar wayar. Shi kuma ya bita da kallon ƙasan ido.
     Yanda tai sallama da ambatar “Daddy....” ya sashi fahimtar Imran ne. Sai kuma ya ɗan kallo shi. Kamar zatai kuka ta ce, “Daddy jikinsa kawai zafi sosai. Kuma yana riƙe cikinsa ban sani ba ko yana masa c....”
     Alama yay mata akan ta bashi wayar. Babu musu ta tako inda yaken ta miƙa masa. Dai-dai Imran na faɗin, “Nimrah baƙya jina ne?..”
      Gyaran murya Dadah yayi, hakan ya sashi fahimtar shine ya amshi wayar. Dan haka yace, “Zakina ka tashi kenan? ya jikin?”.
          “Alhamdullah”.
    Dadah ya bashi amsa a hankali.
“Kayi haƙuri gamu nan zuwa da Doctor. Dama yace zaka tashi da zazzaɓi mai yiwuwa ma da ciwon ciki. Nima na ɗan fita kan wani case ne.”
        “Basai ka wani zo da Doctor ba, shrmenta ne kawai. Nasan da nayi wanka zan ware”.
     “Ba zancen shirme Haysam. Duk wanda ya sanka yaji muryarka yasan baka da lafiya. Kai dai gamu nan”. Bai jira amsarsa ba ya yanke kiran kawai. Wayar Dadah ya kifa akan cikinsa yay shiru. Dan tabbas baida lafiya, sosai kuma yake jin jikinsa..........✍️
111

........Kukan Nimrah ƙasa-ƙasa ya sashi buɗe idanunsa dake jazur kamar garwashi, ya ɗan ja numfashi da miƙa mata hannu alamar tazo. Takowa tai a hankali ta inda yake a baki-bakin gadon. Sai ya nuna mata kusa da shi. A ɗofane ta zauna, sai kawai ya maida idanun nasa ya lumshe yana faɗin,
       “Kukan ya isa haka”.
    Dole ta shanye kukan ta shiga share wayen nata. Babu wani jimawa akai knocking ƙofar. Kallon ƙofar tayi, shi ko bai motsa ba balle buɗe idonsa dake rufe. Kai tsaye tace a shigo batare da tunanin komai ba. Sai ko ga Daddy Imran Doctor biye da shi.  Miƙewa Nimrah tayi tana gaishe su. Dukansu amsawa sukai hankalinsu akan Dadah....

         ∆~~~~∆~~~~∆

   Zuwa yanzu hankalin Malam Almu ya fara tashi da rashin samun wayar Sanda. Bai san miyasa ba tun fitar daya dage sai yayi jiyan nan yake jin zuciyarsa na rawa. Ga shi kuma tunda ya tafi ɗin yake kiran wayar tasa yaji ko ya isa gida amma yaƙi shiga. Har Ogansu ya kira shi kuma ba'a ɗaga ba. Yay ƙaramin tsaki tare da zuba tagumi.
         “Wai lafiya kuwa Malam Almu?. Ko har yanzu damuwar Sanda ɗin ce da?”.
        Mole ne ke tambayarsa cikin tsaresa da idanu. Malam Almu yaja numfashi mai nauyi ya fesar, tare da faɗin, “Wlhy hankalina a tashe yake Malam Buba. Sanda bai san ko'ina ba fa a garin nan. Na tabbatar kuma a sanda ya tafi ko yaje tasha bazai samu motar ƙauyenmu ba. Sannan abokina ɗaya dake tashar yayi tafiya dan na kira shi ko Sanda ɗin yazo yace min ai shi yaje gida matarsa ta haihu”.
      “Eh lallai dole hankalinka ya tashi. Amma nake ganin ai Sanda ba yaro bane ƙarami. Ka ƙara masa lokaci mu gani, idan bai dawo ba ko baije gidan ba saika nema alfarmar masu gidan kabi bayansa. Ni sai na riƙe maka gate ɗin idan sun yarda. Tunda kaga yanzu basu wani damu da fita da driver ba zaman banza kawai nake yi”.
         “Aiko na gode malam Buba. Indai haka ne bari ma na kimtsa. Zuwa anjima sai na samu Hajiya da maganar, da safe kawai na kama hanya”.
      “Shike nan, ALLAH yasa a dace”.
  “Amin”.
     Malam Almu ya faɗa yana miƙewa ya shiga cikin ɗaki. Shima Mole miƙewa yay da waya a hannu ya fita wajen gate ɗin yana neman layin Dagger.....

            (((((((@)))))))))
Chapter 96 · 0% Book details