← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 113

Sashe 101

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Koda Dadah ya dawo gida Nimrah ta jima da yin barci. Ya dai samu Nabeeha na jiransa da bala'in ta. Sai dai itama yanda ta ganshi yasata shiga taitayinta. Dan ta tabbatar a irin yanayin nan taɓashi babbar matsala ce. Dole ta koma lallaɓawa suka kwanta lafiya...

     Da asuba yana fita massalaci tabar masa ɗakin. Sai dai kuma tana zuwa sashen nata ta iske mummunan labari. Maigadin su ya kira Ismat a waya yana sanar mata gidansu babu lafiya. Wasu mutane sun zo sun amshi wani abu har Momynsu ta biyo su tana kuka da ihun su bata. Amma basu saurareta ba sun wuce abin su. Shi ne ta yanke jiki ta faɗi a sume. Tun daren kuma har yanzu bata farfaɗo ba.
        Gaba ɗayan su hankalinsu yayi masifar tashi. Bama su nemi yin sallar asuba ba suka fito har Nabeeha ɗin. Mota suka shiga kawai suka fice a gidan da asubar nan. Koda yake an idar da salla. Dan su Dadah ma sun fito massalaci kenan motar ke fita a gidan. Su duka da kallo suka bita. Sai dai kuma babu wanda yay magana. Dan yanzu su Ja'afar sun sakama ransu mantawa da Nabeeha na rayuwa a gidansu. Tunda sun samu irin wadda suke ma Dadan su fata taita haukanta har a busa ƙaho.
       Shi ko Dadah ransa ne ya ɓaci. Dan haka ya basar. Koda suka shiga suka gaida Mammah da Gwaggo Khadijah kowa nasa sashen ya nufa. Sanin halin Nimrah na nauyin barci ya saka Dadah nufar sashenta. Dan kaɗan daga aikinta ma ya samu bata tashi ba. Sai dai yana taɓa handle ɗin yaji a rufe. Shiru ya ɗan yi na sakanni, sai kuma yabar wajen batare da yace komai ba...
        Koda ya koma sashensa wayarta ya kira. A bugu na uku ta ɗaga. Cikin sanyin murya tai sallama. Idanu ya lumshe ya buɗe. Koda ya amsa mata sai ta ɗora da gaisuwa. Maimakon amsawa sai ca yay, “Kin tashi?”.
      Ta ce, “Uhmm nasa alarm”.
  “Good”.
Ya faɗa a hankali. Itama sai ta ɗan shagwaɓe murya ta ce, “Dadah miyasa baka son amsa gaisuwa?”.
       “Saboda ba irinta nake so ba?”.
   “Wacce kake so to?”.
“Ta mata da miji”.
“Humm Dadah ni dai ba ruwana”.
Murmushi yayi da har taji sautinsa. Itama ta ɗan murmusa tare da faɗin, “Dadah zan yi barci sai anjima”.
     Kafin ma yayi magana ta yanke wayar ƙit. Dan hawaye ma take jin na neman ciko mata ido. Kai kishi masifa ne ALLAH. Ta ayyana a ranta tana kashe wayar gaba ɗaya. Duk da tasan da wuya ya ma sake kiran...

          Shi ma wayar ya ajiye kawai yana ɗan furzar da huci. Zai miƙe sai ga kiran Imran. Kira a irin wannan lokacin mai muhimmanci ne, dan haka baiyi jinkiri ba ya amsa. Sun gaisa da tambayar juna iyali. Kafin Daddy Imran ya ɗora da faɗin,
      “Wai mi ya fusaka ne jiya? Ga Faro shima ya hau fuuu”.
       “Humm wannan idan ya harzuƙa koni ya buge ai”.
    “Haba shi ya fara buge suruki. Kawai dai zuciyar tasa a kusa take”.
    “Ni kaina al'amarin yaron ya rikitani. Dan ba ƙaramar mamaya yay min ba”.
          “Kana ganin ba gaskiya ya faɗa bane?”.
      “Bana ce ba. Amma al'amarin ba buƙatar nazari”.
    “Haka ne. Amma karka manta mahaifiyarsu dama tace su biyu ne. Kuma ai ta bamu alama na abinda ya bambanta su”.
        “Humm Imran. Wanda ke da ƙarfin halin canja kansa zuwa soja na tsahon shekaru mi kake tunanin zai gagareshi canjawa. Ina son na gansu a gabana su biyun, ta hakanne kawai zan iya nazartar su. Dan duk yarona na amana halayyarsa rubutacciya ce a zuciya ta. Amma a wannan gaɓar akwai abu biyu masu ban mamaki. Ojo baya jin Hausa, duk da nasan zai iya koya, sai dai yanda take fita da ƙyau a harshensa na nufin dama can yana ji ɓoyewa yake. Ya canja addini zuwa wanda ban sani ba, duk da shima nasan idan UBANGIJI ya so shi da shiriya hakan mai sauƙi ne”.
      “Na yarda da hakan nima, hujjojinka duk abin a duba ne da mahangar gaskiya. Sai dai kaji mi yace. Shi ne kawai zai iya kama shi. Kaga ko sai idan ta gidan Soja zamu kamashi mu ke nan”.
          “Hakan zai ja hankalin waɗanda bama son hankalinsu ya kai?”.
     “To miye mafita?”.
   “Ita muke buƙatar nema. Dan haka kaje kai nazari. Shima Faro yayi. Daga nan zuwa awanni goma idan ba'a samu ba ku barni zan kama shi da kaina”.
          “Amma Zak....”
      “Karka damu komai normal”.
  “Shike nan ALLAH ya bamu sa'a. Ya maganar kai Daughter ɗin?.”
     “Zamu je. Ka shirya kawai”.
  “Okay ALLAH ya kai mu”
      Suna yanke wayar Dadah ya miƙe. Gaban window ɗin ɗakin yaje ya tsaya. Ya zuba ma duka compound ɗin gidan ido. Kafin ya sauke akan Mole dake zaune da Malam Almu. Yanda sukai ɗin zai tabbatar maka magana suke mai muhimmanci. A take kansa ya kawo wani haske. Wajen ya bari ya sake komawa inda wayarsa take ya ɗauka. Kai tsaye layin Mammah ya kira. Alamar tana kusa da wayar babu jimawa ta ɗaga. Sun riga sun gaisa, dan haka bayan gaisuwa cike da girmamawa yay mata tambaya.
        “Mammah waye ya kawo yaron nan Sanda tsakanin Driver da maigadi?”.
      “Malam Almu ne Muhammad. Ƙaninsa ne ma kamar yanda yace. Wani abu ya faru ne?”.........✍️
116

..........“A'a na tambaya ne kawai”.
    “Oh. Dama yanzu yake zuwa ya sanar min zaibi bayansa. Dan jiya yaje wajen wani abokinsa har yau bai dawo ba. Ya kira abokin kuma baije can ba. Sai yake tunanin ko gida ya gudu ne”.
          “Sai kace wani yaro ƙarami”.
      “Yaro ne mana Muhammad. Kai yanzu ƙannenka a gabanka ba jin kansu suke kamar jinjiraye ba”.
      Murmurshi yayi kaɗan. “Shike nan Mammah. Tunda an fara zuwa nan sai anjima”.
      Itama ƙaramar dariya tayi. Daga haka wayar ta yanke.

         Wayar Imran ya sake kira. Yana ɗagawa Dada ya ce, “Inaga mun samo makama”.
    “Woow tami?”.
“Yanzun nan Malam Almu zai fito ka saka Dabo ya bibiye shi. Ko wane motsinsa ya dinga sanar maka da gaggawa”.
       “Okay”.
   Imran ya amsa masa. Shima sai  ya yanke wayar....

      {{==}}{{=}}{{==}}

             Ba ƙaramin firgicewa su Nabeeha sukai da yanda suka iske Momyn su ba. Da ƙyar suka iya kin kimarta suka saka motar. Suna ƙokarin fita motar mijin Jiddah ta iso. Sai kawai suka juya asibitin gaba ɗaya. Cikin gaggawa aka karɓe su. Bayan an shige da ita domin bata taimakon gaggawa su kuma sukai cirko-cirko. Kowanne tambayoyi fal ransa da tunanin su waye wannan suka je wajen Momyn tasu? Mi suka amsa haka a gareta da har ya jefata a wannan halin?.
      Rashin mai basu amsa ya saka su cigaba da zaman jira. Kusan awa ɗaya kafin likitan ya tabbatar musu ta farfaɗo. Sai dai sun mata allura mai ƙarfi ta barci dan jininta ya kai ƙololuwar hawan da zuciyarta zata iya bugawa ma. Hankalinsu ya ƙara tashi, nan suka shiga roƙon ya taimaka musu kar su rasa Momy ɗin su.
       Yace suyi addu'a. Shi nashi yin abinda ya dace ne kawai. Rayuwa kuwa na'a hannun UBANGIJI.

     Sam hankalin Nabeeha bai bata ta amshi waya ta kira Dadah ba. Kawai suka share uwawu zaman jiran farkawar Momyn su. Sai wajen sha biyu ne ma mijin Jiddah yace shi zai je gida ya dawo. Ko a lokacin ya kamata itama Nabeeha ta tuna da bata fa sanar ma Dadah ba. Amma ina. Mijin Jiddah ya wuce babu jimawa Mamawo ta iso. Acewarta tana zuwa gidan ne maigadi ya gaya mata abinda ke faruwa. Shine taho tunda tasan babu asibitin da suke zuwa sai wannan.....

         <%><%><%><%>

      Nimrah da batasan wainar da ake toyawa ba sai yanzu ma take tashi a barci. Ita kanta mamakin barcinta take yanzu. Tashi take kawai badan ya isheta ba sai dan yinwa dake tada ita. A gurguje tai wanka, ta shirya cikin wando falazo da ƙaramar riga mai guntun hannu. Duk rashin son kitsonta gashinta ya fara damunta a tsefen nan, dan haka ta fara tunanin yima Ruky magana su je saloon. Da wannan tunanin ta fito falonta. Ta ɗan gyara shi sama-sama dan babu wani datti sosai tunda ba zama ake ba ta wuce kitchen. Dan ji take kafin taje sashen Mammah yunwa ta kayar da ita. Gara ta fara cin wani abu sannan.
       Tana ƙoƙarin fidda tukunya a store tana kiran wayar Mammah. Dan tana son ta gaisheta kafin taje. Ai ko tana ɗagawa ta fara gaishetan da girmamawa. Cike da farin ciki da kulawa Mammah ta amsa, sun ɗanyi hira kaɗan suka gaisa da Gwaggo Khadijah itama. Daga haka sukai sallama. Harta ajiye wayar kuma ta ɗauka ta rubuta text na gaisuwa ta turama Dadah. Daga haka ta fara aikinta.

      Anan kuwa cike da farin ciki Gwaggo Khadijah ta ce, “Rayuwa kenan mahaƙurci mawafaci. Shiyyasa akace duk wanda bai ci ribar haƙuri ba kaɗan yayi. Tabbas yanzu muka san Haysam ya samu matar data dace da shi. Ita ko wannan shashashar yarinya ALLAH yasa ta gane ta gyara kafin waje ya ƙure mata.”
      Mammah dake saurarenta tai murmurshi da faɗin, “To Amin Yaya. Nima ina mata wannan fatan. Amma sai kin saka ido akan Muhammad. Dan ni dai ɗazun abinda muka tarar ya sani jin tsoron kada ya karkata ga abinda zai sa ya halaka ya halaka min yarinya. Bana son ya ɗora rayuwar aurensa da Nimrah akan zaluntar Nabeeha. Koma mi yake tunanin ta masa tsakaninsa da ita ne can su ƙarata. Kada ya samun yarinya a ciki”.
        Ƴar dariya Gwaggo Khadijah tayi da faɗin, “Ni kuma Kinga ban kawo komai a raina ba. Duk da nasan ɗan adam mai iya canjawa ne akoda yaushe bana jin hakan ga Haysam. Yaro ne shi mai halin manya, mai addini mai ƙoƙarin adalci. Ko abinda yayi na ƙin kulata bayan fitowarsa na tabbatar yana da dalili tunda sai da ya dawo ta dawo gidan. Amma duk da haka zan duba saboda ajizanci”.
         Cikin gamsuwa Mammah ke gyaɗa kai...
Chapter 101 · 0% Book details