← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 113

Sashe 58

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........“Uhmm Twiny! Wai kaga yaran nan kowanne yay bulum yini guda ko ƙeyarsu babu a wajen”.
      Ma'aruff ya tuntsure da dariya. Ya ce, “Hummm Twiny tun ɗazu nake gulma a zuciyata. Har Sherry na tambaya yau tsakanin Ammar da Bilal wata gani a sashen Mammah? tace su duka basu zo ba.”
            “Oh ni Ja'afar aiki gamai ƙareka. Karfa ƴaƴan Dadah su ɓaro aiki, kwana da wuni fa tabbb...”
         “Hummm inji mai ciwon haƙori. Shima BABBAN TORON ai yau a cikin alkairi yake dumu-dumu. Shiyyasa nace maka wlhy muma mu sabunta namu angwancin. Yau ba zuwa kasuwa dan ba'ayi bikin wannan rana mai albarka babu mu ba”.
      “Banga laifinka ba kuma naji daɗin shawara, dan wlhy sai Asr nabar Lailaty ta leƙa sashen Mammah yau. Ina zamu tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mana ƙafa.”
     Cike da shaƙiyanci suka kuwa kwashe da dariya suna tafawa. Daga haka suka nufi sashen Mammah dan dama daga massalaci suke sallar isha'i. Sai dai anyi shuka ne akan idon makwarwa, dan dukkan wannan hira tasu a kunnen Bilal ta kasance. Ya fito massalaci ya hangosu, shine yay ƙoƙarin biyo su su ya gaishe su dan yau baiga kowa a cikin ƴan uwan nasa ba hatta Ammar. Sai dai kuma jin hirar shaƙiyancin su Yaya Ja'afar ɗin ya sakashi jin nauyi ya koma bayan mota dake a wajen ya tsaya har sai da suka wuce. Fuskarsa da murmushi yana girgiza kai ya wuce sashensa. Dan gwara kawai a ƙarasa yau ɗin a haka ba'a ga junan ba gobe idan ALLAH ya kaimu a haɗe....

        Ƴan biyun Mammah kuwa da basu san ɗan ƙaninsu ya jisu ba tuni sun shige suna gaisawa da baƙi. Kafin su ƙarasa bedroom ɗin Mammah data shige tana waya da Dadah.
     Zama duk sukayi a gefe da gefenta suka sakata a tsakiya kamar yanda suke yi. Dan haka suka ji abinda take tattaunawa da Nimrah dake faman zuba mata shagwaɓa. Sai da ta yanke wayar ne cikin haɗa baki suke tambayar ina Nimrah ɗin taje ne? Kai tsaye kuma Mammah ta basu amsa da sunyi tafiya da Dadahn su tun a daren jiya...
     Kallon juna Ma'aruff da Ja'afar sukayi kuwa. Sai kuma Ma'aruff ya ce,  “To ALLAH ya tsare ya dawo mana da su lafiya. Ni dana gani a labarai ɗazun na ɗauka fa kawai sharrinsu ne yana gida ne yana hutu Mammah”.
          Murmurshi Mammah tayi kawai. Sannan ta bashi amsa da, “Nasan zai kira ku ai. Tafiyar tazo ne kawai babu shiri”.
       Ja'afar dake gimtse dariya ya ce, “Da alama kam Mammah, dan Dadah bai taɓa tafiya kota cikin ƙasa bace bai mana sallama ba. ALLAH dai ya dawo mana da su lafiya”.
      “Amin ya rabbi”.
   Cewar Ma'aruff. Daga haka kuma suka saki zancen kamar gaske. Sai dai suna fitowa bayan gama hira da Mammah Ja'afar ya ce, “Twiny kaga fa aikin manya. Wannan shi ake kira da BASU ƘAFA”.
       “Ai sai dai BASU ƘAFAFU Twiny. Dadah ya gama goge min hadda. Wayyo Ninah har na ji ma tausayinta”.
      “Uhmm ai dole a tausaya mata. Dan kuwa dai a hannun manya ta faɗa.”
           “ALLAH ya shirya min kai ni dai ba ruwa na”.
     “Au ALLAH! Naga tare mukayi”.
“Kadai yi”.
Cikin dariya Ja'afar ya kai ma Ma'aruff naushin wasa. Ai ko da gudu yabar wajen yana kwasar dariya....

      ....★Da lalube Hanoon ta dafe bango. Zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri. Hawayen da suka ciko mata idanu suka shiga rige-rigen faɗowa. Haysam ɗinta, ya ɗauki wannan shegiyar yarinyar datai masifar tsana a rayuwarta suka tafi wata ƙasa wai? Honeymoon fa kenan?. Kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata. Ta zube a ƙasa kawai ta hau rerawa.
       Tun jiya bata da lafiya. Kai koma tace tunda aka fara shagalin bikin nan. Babu yanda su Afeef basuyi ba ta bisu suje gida taƙi. Dan tun washe garin walima Abbasu ya koma, shine suka bishi. Ita kuma bazata iya barin gidan nan a wannan gaɓar ba. Dan babu inda ya taɓa mata daɗin zama irinsa. Duk da Dadah yama idannunta nisa a kwana biyun nan saboda cikowar mutane gidan ambatonsa kawai da akeyi na sauke damuwarta. Ashe ma baya ƙasar tun jiya ita bata sani ba.
      Ta jima sosai tana kuka, har sai da taji kanta na juyawa ta miƙe da ƙyar. Ta kitchen ta bi ta shige ciki. Kai tsaye kuma ɗakin Biebah da take zaune ta shige. Kayanta ta shiga haɗawa, dan wlhy bazata iya zama a gidan nan ba a wannan lokacin. Gara taje wajen ƴan uwanta na wasu kwanaki kafin ta dawo. Maybe hutun zai bata damar samo mafitar mallakar Dadah a matsayin miji kamar yanda take fata......

          ««««««««•»»»»»»»»

    “Nimrah!”.
Dadah ya faɗa zuciyarsa na tsargawa. Sosai kansa ya masa wani irin nauyi ne da ciwon kai mai tsanani. Dan haka ya sake kai hannu da ƙyau ya ɗaga nata. Yaraf ya koma alamar numfashinta fa baya tare da ita.
         “Ya Arrahman”.
    Ya faɗa a hankali yana lumshe idanunsa da gaba ɗaya basu da siffar daɗin kallo a yanzu. Ya fahimci ta suma ne. Dole hakan ta faru, dan shi kansa a jikace yake balle ita. Duk da yanda yake jin yanayinsa dole ya daure ya tashi zaune da ƙyar. Idanu ya ɗan zubama fuskarta datai kaca-kaca da busassun hawaye da majina yay na sakkani. Sai kuma ya kai hannu a hankali ya murza goshinsa da cije lips.
     Bai ce komai ba ya miƙe yana kallon agogo. Lokacin sallar asuba ma ya rigada yayi, dan haka ya nufi bayi bayan ya gyara mata kwanciya. Yana wanka a ƙarƙashin shower abubuwa na dawo masa tamkar mafarkin daya saba ko almara. Yau dai ALLAH yayi. Labarin ya fara masa tun daga MAFARI. Ranar farko na haɗuwa da MACE mai ciki. Abinda ya faru har zuwa alƙawarinta. Alƙawarin da ayau yake kallonsa a matsayin wani rubutaccen al'amari daga UBANGIJI. Gashi dai bata haifi SOJA ba, amma ta haifi MATAR SOJA.
        Wani guntun murmurshi mai sanyi ya suɓuce masa. Hannu ya saka ya sharce ruwan fuskarsa. Yayinda tunaninsa ke sake zurfafa. Yarinya mai wayo da shiga rai. Ƴar shekaru bakwai kacal da bakinta baya iya shiru. Ta bashi babban sirri da ƙyautar ɗiyan itacciyar dabino ta zama sanadi, sirrin da ya buɗe masa abubuwa da yawan gaske tun a wancan lokacin. Eh bazai yi musu ba, daga wannan ranar ne babban labarin ya fara, sai zuciya taƙi amsa da sabon batun da ya dingama kallon daga shirmen zuciyar ne kawai da sakarci mara tushe balle makama. Haba dai ƴar shekara bakwai fa. Wadda da haihuwa ya samu yana da wada suka fita kamar uku a lokacin. Taya ma za'ai ya yarda da wannan shashancin. Kasancewar sa jarumin dannewa sai kawai ya ɓarar atake anan. Ya kuma saka ƙafa ya take sannan ya nuna jarumtar mantawa na har abada.
      To ashe dai labarin zai sake maido kansa sabo ne. Sabo a gaɓar da matar aurensa ta jingina AMANAR BAZATA a matsayin ɗiya ta jini. MAFARKI mai ruɗarwa ya tabbata tamkar a hikayar marubuta. Ya mallaka a matsayin da zuciya ta fara ayyanawa tun a farkon gani. Oh-oh a wannan ranar fa ya shiga ruɗani, ruɗanin da shi da zuciyarsa kawai sukai kiɗansu sukai rawarsu. Dan ko AMINI na gaskiya bai yarda ya nunawa ba. Haka ya cigaba da shanyewa, rayuwa a prison shi kaɗai a zahiri, sai dai a mafarki kullum da ƴar shekara bakwai ɗin nan yake barci. Al'amarin na firgitar da shi, dan ya kasa fassara waɗan nan firgitattun mafarkai kasancewarsa ba mai ilimin fassara mafarkin ba. Haka ya cigaba da roƙon UBANGIJI mafita da hanyar ɓullewa akan abinda yake kallon son zuciya.
     Tabbas UBANGIJIN ya amsa, dan kuwa bayan fitowa da jiyyar jiki tun a filin jirgi wajen tarba tsumammen SIRRI ya motsa. Kaf siffar mafarki ta bayyana kanta a zahirance. Ƴar shekara bakwai ta girma. Ta mallaki komai na mata da zasu iya mallakar abokin halitta. Sai dai kuma abin da kunya, wai a raka baƙo ya ruga. Dan haka ya cigaba da dannewa da yaƙin zuciya. Wani lokacin al'amarin yakan so kwaɓewa idan tana a gabansa, dan da ƙyar yake ƙwatar kansa a hannun rikicin ZUCIYA da GANGAR JIKI. Har dai a yau UBANGIJI ya kaishi ga bigiren DA ƘYAR AKA SHA yafi DA ƘYAR AKA KAMA NI...
      Murmurshi ya sake suɓuce masa mai matuƙar yalwa. A saman laɓɓa ya furta “Dana rasaki dana lalace.”
   Ya sake lumshe idanunsa yana sake buɗewa. “Nabeeha kin cancanci tukuycin haƙuri da dukkan halayen ki, sakamakon ta SANADIN shirmenki na MALLAKETA a gaɓar da sallamawa ta tabbata saboda rashin mafita. Wlhy hakan ya ƙara miki DARAJAR da baki sani ba”. Ya sake faɗa cike da yanayi mai muhimmanci. A kuma dai-dai nan ya kammala wankan nashi ya kashe shower ɗin. Towel yaja ya ɗaura. Tare da ɗaukar ƙarami ya fara goge kansa zuwa gashin fuskarsa dake ɗigar ruwa. Fitowa yay a bayin gaba ɗaya. Dan gara ya fara gabatar da salla kafin aje lavel 2 na rikicin wannan Little trouble ɗin tashi. Saboda ya tabbatar yau sai abinda ya gani, abinda ta manta ne kawai bazata aikata masa ba. Sai dai ko'a yaya ne zai ɗauka, zai ɗauka batare da gajiyawa ba ko ƙosawa kamar yanda itama ta ɗauke rikicin shekaru tara cikin amincin UBANGIJI.............✍️

       Ina fatan zaku fahimci tunanin DADAH bada rikici ba🥱🤤🤏🏃🏼‍♀️.

    74
Chapter 58 · 0% Book details