Sashe 111
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........Kawu Tanimu ya jinjina musu kai da faɗin. “Kamar yanda na faɗa muku haka ne. A gabana komai ya faru. Dan bayan sakin mu da kuka yi ne naje gida na iske Yaya Hassatu ta tafi gidansu, kuma yayyenta ne suka zo suka ɗauke ta. Ko zama banyi ba nabi bayanta dan ina son naji gaskiyar yanda abubuwa suka kasance. Ashe babu rabon nayi sallama da su Inna da matata, dan ban kai ga shiga wajensu ba. Kokuma nace nima nawa kwanan basu ƙare bane shiyyasa, dan da gidan namu na fara shiga ba lallai na tsallake ba. Anan kuma na tarar har komai ya faru kun fito da su Yaya Hassatu daga gida. A kan idona aka kashe Malam. Hakama Yaya Hassatu. Banda wani ƙarfin iya taimakon su a wannan lokacin, balle ma gaku sojoji zagaye da su. Hatta amanar data baka ta Nimrah ina kallo duk da bana iya jiyoku saboda ina akan bishiya ne. Amma na karanci abinda laɓɓanta ke furtawa. Hatta tashin bomb da akai a gidan akan idona ne, dan na zabura zan sakko dan na sanar muku kawai bomb ɗin ya tashi. Ni kaina a lokacin na suma a bishiyar. Ban tashi farfaɗowa ba sai asuba. A lokacin kun bar wajen kun tashi sabon yaƙi da yan ta'addan zuwa cikin jeji. Bani da zaɓin daya wuce silalewa na gudu. Dan ina burin kaima Baba labarin komai ga garin namu kuma ya rikice shima. Na leƙa gidanmu na samu komai ya rushe duk an kashe su suma sai gawarwaki. Tsabar tashin hankali da ƙyar na samu na baro yankin mu, ALLAH ma ya soni akwai kuɗi a jikina. Haka na koma inda nake sana'a, sai dai babban burina haɗuwa da Baba ne. A lokacin kuma ya fara ɓoye min har sai idan shi yaso ganina yake samuna. Sai da na kwana labari ya gama karaɗe gari sai gashi. Jiki na rawa na bishi. Ban ɓoye masa komai ba daya faru ba ina kuka. Ciki harda amanarki da mahaifiyarki ta bayar, dan zuwa lokacin shima har ya samu Edited video ɗin nan a hannunsa. Shine ma ya nuna min, hankalina ya tashi nayi kuka sosai har ina roƙonsa kan ya kaini gidan rediyo ko ga sojojin zan faɗi gaskiya wannan videon ƙarya ne. Amma sai ya ce bazai yiwu ba. Dole wannan video ɗin sai ya zama tsanin ƙaddara a rayuwar ka. Dan wanda suka shirya komai suna da ƙarfin iko, kuma tunda suka shirya kaika prison sai fa sun aikata. Sai idan mutuwarka ce ta canja hakan, shima kuma yana ganin zuwanka prison ɗin zai taimake ka da abubuwa da yawa da baka fahimcesu ba, zai kuma baka sabuwar ƙwarin gwiwa. Amma zai yi abu ɗaya, shine baka kariya a cikin prison ɗin ta hanyar yaran sa. Sannan zai mallaki ainahin videon gaskiya.
Badan na samu salama ba na haƙura. Dan bayan rikicin garinmu da rasa ahali daya nema haukatani rufeka shine abu na biyu daya nema ƙarasa sabauta rayuwata. Sai da nayi jiyyar kwanakin daya saka har maganin ƙwaƙwalwa sai da na sha na kusan watanni uku kafin na dawo dai-dai. Daga nan ne fa Baba ke sanar min ka auri Nimrah kafin a kaika prison. Shawara ɗaya kuma da zai bani shine na koma makaranta. Ta hanyar samun ilimi da aikin yi ne kawai zan iya bama Nimrah kariya, sannan a watarana na fidda gaskiyar ainahin abinda ya faru ma duniya har a saurare ni. Na gamsu da shawararsa, dan kai tsaye ma nace masa soja nake so. Amma sai yace ɗan sandan farin kaya yafi dacewa dani. Domin ba Nimrah ce kawai ke butata ba, hatta ƙauyenmu na buƙata ta. Dole kuma sai na zama matacce a gare su sannan zan rayu akan bama garina kariya. Daga nan ne sabuwar rayuwa ta fara. Na fara karatu ina cigaba da bibiyar Nimrah musamman a makaranta. Koda yaushe ina yawo da cemara ina mata hoto. Dan tun abinda ya faru naima kaina alƙawarin bazan sake sakaci ba. A sanda wancan abin ya faru da ina da cemara kota waya ce ai da ba'a kaika prison ba...”
“Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kenan da gaske Umma ta rasu? Amma Kawu mi yasa su sukai min ƙarya?”.
A tare duk suka kalli Nimrah mai maganar tana rusar kuka. Kafin Mammah ta iya faɗin, “Su wanene?”.
Kallon Mammah tayi, sai dai ta kasa magana. Ga kuka yaƙi tsayawa. Kawu Tanimu da Dadah da Imran hankalinsu ya tashi matuƙa. Sai dai bazaka taɓa iya gane hakan a fuskar Dadah ba. Sai ma wayarta da Ruƙayya ce ya shiga dawo masa a rai dalla-dalla a randa ya bata aro a Dubai. Dan abinda bata sani ba wayarsa ba haka kawai take ba. Sannan tana da alaƙa mai ƙarfi da agogon hannunsa. Hatta kiran da taima Ruky ya gani, bai bibiye su bane a sanda suke magana saboda yana meeting. Hakama kiran Mammah datai, shi ne ya katse kiran ya hanata samunta. Daɗewar datai a cikin WhatsApp ɗinsa ma duk ya gani. Sai da bai nuna mata ba sai daga baya ya saurari hirarta da Ruƙayya ɗin, dan gaba ɗaya wayar ta naɗe komai ta ajiye masa. Tun ma bai nisa ba ya fahimci abinda ta daɗe a WhatsApp kenan ta nayi, wato charting ɗinsa da Doctor ta bibiya. Alwashinta na ƙarshe datai a hirarsu da Ruƙayya ya sashi murmushi a ranar. A yau kam ya ƙara tabbatar da wautar yarinyar nan da rashin jinta. A tunaninta abinda take jin zata iya tunkara ɗin wasan yara ne kenan. Ita a dole ga manyan mata. Murmurshi ya sake suɓuce masa. Dan hatta wayarta ta jiya yaji, ya barta ne kawai yaga inda wasan zai tsaya. Sai kuma ya ɗan ciza lips yana kawar da kansa daga kallonta....
Tambayoyin da su Kawu Tanimu da Daddy Imran ke jera mata ya sata faɗin, “Sun ce idan na faɗa zasu kashe Ruƙayya da Mammah. Ni kuma bana son a kashe min su”. Ta sake rushewa da kuka. Hannunta Kawu Tanimu ya kamo ya matso da ita kusa da shi sosai. Cikin shafa kanta da lallashi ya ce, “Nimrah ki nutsu kinji ki mana bayani. Babu abinda suka isa su miki. UBANGIJI na tare dake. Hakama ƙarya suke bazasu kashe mana Mammah da Ruƙayya ba in sha ALLAHU. Kalleni nan fa ɗan sanda ne. Kawunki ɗan sanda. Ga Daddynki soja, sojan ma shugaba mai muƙamin NSA. Ga mijinki tsohon soja, sannan sirrintaccen ma'aikaci a yanzu. Gefe kuma Cheff of staff. Kin san minene girman Cheff of staff kuwa?”.
Kanta ta jinjina masa.
Ya ce, “Yauwa. Kar kiji wani kin damu. Ga mijin Small Mom ɗin ku shima Soja. Kinga ke yar gata ce. Runduna guda ce a zagaye dake. Ga kuma babban mai bada tsaro UBANGIJI. ga addu'ar su Mammah.”
Nan ma sai ta jin jina kai. Tana share hawaye ta fara basu labari tiryan-tiryan akan mu'amularta da Dagger. Har zuwa saceta ɗin nan a ranar sunan Naseer, da bomb daya kusa tashi da su. Video nan na bogi. Tare da sirrika masu yawan gaske da mutanen suka nuna mata. Yaran ƙauyensu da mutane da yawa. Yanda suka ɓata Dadah a wajenta matuƙa da Daddy Imran. Halin data tsinta kanta a ciki na firgici da rashin hankali har zuwa lokacin da Daddah ya dawo gida. Yanda ta dinga bibiyar abubuwansa batare daya sani ba. Yanda ta haɗa alaƙa tsakanin Dagger da Malam Buba driver. Da aron wayar Sanda da take yi. Hatta hotunan su Dagger data gani a ɗakin Dadah ɗin ta gayama Malam Buba ya sanarma Dagger. Yanda Dagger ke zuwa school ɗinsu su haɗu, har ranar da ya saceta tare da Ruky da Malam Buba. A ranar kuma ta fara ganin wani mai kama da Kawu Tanimu, sai kuma ta suma. Daganan ne dai bata san ya akai ba aka amso su, ta daina ganin Malam Buba sai daga baya ya sake dawowa. Ta kuma daina jin Dagger gaba ɗaya sai a kwanan ya dawo. Abinda yasa kuma take saurarensa tana son ya kaita ga Ummanta ne da yace tana raye. Sai kuma don sanin gaskiya akan Dadah kamar yanda Ruƙayya ta bata shawara. Dan zuciyarta da hankalinta sun fara rabuwa a randa taga hirar doctor da Dadah......
Dadah da baya son ta faɗi abinda ya gani ɗin yay gyaran murya. Dan haka tai shiru tana share hawayenta. Dan ko baiyi hakan ba dama bazata faɗa ba tunda baya son a sani. Ko a labarin da Daddy Imran ya bayar shima taga bai faɗa ba.. kwarai-kwarai da gaske sun girgiza da labarin nan nata har takai sun ma gagara yin magana. Musamman Mammah da mamakin duniya ya isheta da jinjina taurin zuciya da wayo irin na Nimrah. Tabbas ta tsargu da abubuwa da yawa a lokacin daga Nimrah ɗin, amma bata taɓa kawowa a ranta girman sa yakai haka ba. Shi kansa Dadah daya jima yana zarginta da karantar lamarinta bai kawo girman abinda taji kuma ta gani ya kai haka ba. Lallai mutanen nan shaggu ne. Yanzu kamar ƴar yarinyar nan suke yunƙurin birkitama tunani haka dan zalunci da mugunta. Aiko sun kawo kansu ramin da bazasu iya fita ba. Dan sun taɓa abinda bazai iya kauda kai ba. Lokaci yayi kuma da zai tabbatar musu da hakan. Lallai a wannan gaɓar ne zai cika alƙawarinsa na saka su RAWAR ƘOROSO da SARƘA a ƙafa.........✍️
🤣🤣Dama mu ranar muke zaman jira ai Dadah.
126