← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 113

Sashe 22

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

      Yau ta kasance juma'a ne. Rana ce da Nimrah take cika shekara sha bakwai. Da yake ba wani biki suke ba ko'a jikinta. Hasali ma tama manta da wani cikar shekararta. Yau mai lassing bata zo ba, dan haka suka sha barcinsu. Monday in sha ALLAHU zasu fara exams ɗinsu kuma.
     Birthday cake na bazata mai ƙyau Ruky ta shirya ma Nimrah. Dan haka ta gudu sashen su Lailah acan tayi shi. Sai da zasuyi sallar magriba Nimrah tace zatai wanka tana jin zafi Ruky ta saka su Kulu suka tayata shirya komai a falo. Dama tayi hakan ne saboda dawowar Uncle's ɗinsu. Dan sai Lahadi su Uncle Ja'afar zasu wuce suma. Abin kamar wasa sai gashi ɗan kwalliyar ɗin da sukayi yayi ƙyau sosai. Su Afrah sai murna suke dan basu taɓa gani anyi a gidansu ba. Wannan ma Ruky sai da taita lallaɓa Mammah ta yarda, kuma badan komai tayi ba sai neman magana. Babu wanda ya sani ta aiki Abees da Aheel sashen Nabeeha wai ya faɗa musu 8:30 Mammah na kiransu..
      Koda su Abees suka je sashen Nabeeha banda kallon tsana babu abinda yaran suka samu. Haka kawai take jin baƙin cikin yaran. Yanda bata shiga harkar iyayensu suma ba shiga tata suke ba. Dan tunda ta dawo gidan ko barka bataje ta musu ba. Hakan yasa suma suka nuna bama su san da ita ba a gidan. Dada dai uba suke kallonsa, kuma girmansa na musamman ne a garesu. Ita kuma tunda ta kasa riƙe nata girman sai taji da matsalarta can. Dama kuma mazansu sun musu gargaɗi akanta, hakan ma ya ƙara basu lasisin riƙe kansu.
Received at 6:25 AM       Ismat ce ta amsa yaran, suko dama ba wajen zuwansu bane, suna gama faɗa suka baro sashen batare da sun damu da abinda akai musu ba abinka da yara. Sai da akai sallar isha'i kowa ya shigo sannan sukaga mi Rukyn tayi. Ma'aruff ya riƙe baki da faɗin, “Yaushe aka fara bikin birthday a gidan nan bamu sani ba?”.
       Kunne Ruky ta kama tana shagwaɓe fuska da faɗin, “Uncle Ninah kawai namawa, kuma ALLAH na roƙa Mammah”.
        Gefe Ammar yay da kansa yana runtse idanunsa. Dan yanda tayi sai da yaji kamar ya kamata ya rungume bakin shagwaɓar ya... Uncle Ma'aruff ya girgiza kansa kawai da faɗin, “Shike nan sai a yanka mana cake muci to”.
     Daɗi ya kama Ruky jin basu yi faɗa ba. Tasan kuma da Uncle Ma'aruff yayi Uncle Ja'afar ma zai yi. Ana haka su Shariffa ma suka shigo. Ruky nata kallon hanya amma babu Dada babu su Nabeeha. Ba haka taso ba, dan haka ta kama leƙe-leƙe. Mu'azz abokin daba tsaf ya harbo jirginta, dan haka ya matso yana mata magana ƙasa-ƙasa.
         “Uwar mi kike shiryawa?”.
    Harararsa tayi da masa nunin yay shiru. Kafin ta sake rage murya ta sanar masa. Sai yay murmurshi da faɗin, “Shine zaki shirya wannan plan ɗin ba gayyata? Ai dole dani za'ai wannan sabgar. Jeki ki fito da Ninah zan ƙarasa sauran.”
        Tasan Yaya Mu'azz zai yi, dan haka cikin farin ciki ta wuce. Ja'afar ya kalla Ma'aruff dake wasa da Naseer daya amsa hannun Shariffa. “Twiny mi yaran nan suke shiryawa ne?”.
        Kallonsa Ma'aruff yay da tambayar “Kamar ya?”.
     “Bakaga Mu'azz da Ruky na ƙus-ƙus ba. Sannan Ninah bata a falon”.
        Fuskarsa da murmurshi ya ce, “Bari mugani dai to. Ni kaina na fara fahimtar wani rashin jin zasuyi......”
    Maganar tasa ta tsaya saboda shigowar Dada falon riƙe da hannun Mu'azz. Dai-dai nan kuma Ruky ke fitowa da Nimrah idanu a rufe. Tsayawa Dada yay yana kallonsu. Hakama su Biebah duk sun maida hankalinsu kansu. Sai ga su Ismat sun shigo. Nabeeha sai cika take tana batsewa dan da ƙyar Ismat da Amima suka sakata ta taho. Rayhana kuwa da manufa ta biyosu jin ance Mammah ke kiran, tasan koba komai za taga Dada da ganinsa ke musu wuya yanzu a gidan fiye da kowa.
       Suma tsaye sukai cirko-cirko, sai da Ruky ta kawo Nimrah tsakiyar falon kawai Mu'azz ya dawo kusa dasu ya fara mata waƙar birthday. Su Ayyan kuwa suka hau tayashi suna tsalle. Shi Dada ma abin nasu girmar kansa yayi, dan haka ya gagara magana. Sai ma zaune da ya kai kusa da Mammah dake cema su Nabeeha su ƙaraso mana suka tsaya. Dan ita bata san miya kawosu ba. Tunda bata san Ruky ta zabga mata ƙarya ba.
       Ismat dake jin kamar taje ta rungume Ja'afar ta ja hannun Nabeeha dake shirin ja baya. Ganin haka itama Amima ta tare ta, dole badan taso ba suka ƙarasa ɗin. Lokacin Ruky ta buɗe fuskar Nimrah da mamaki ya kamata tana bin komai da kowa na falon da kallo. Sai kuma ta tsaida idannunta dake cika da ƙwalla akan Ruky, tare da rungumeta. Yanda tayi ɗin ya bama kowa dariya banda su Nabeeha. Dan alamu sun nuna itama bata san an shirya abin ba. Dada ma kamar baya falon yama maida hankalinsa kan Khadijah da ya saka Ammar ya kawo masa. Yana son yara sosai, yau kuma su Abees ba tashi suke ba uwarsu na shagali.
      Nabeeha tana son tace ma Mammah gata tana tsoron Dada, dole ta dake tana jiran Mammah ɗin ta fara magana da kanta. Amma wani irin tafasa zuciyarta keyi da kallon su Nimrah dan haka ta ɗauke kai, wani sashi na zuciyar tata kuma najin daɗin ganin yanda Dada ko kallonsu bayi yake ba shima...

      Oho su masu birthday bama su san tanayi ba. Dan Kulu na kawo cake su Ma'aruff da su Lailah suka biye su Nimrah suma. A take suka je aka zagayeta akace ta yanka. Ita ta riƙe wuƙar Ruky ta ɗora hannunta kan nata da su Afrah gaba ɗayansu. Suka ko yanka cake suna farin cikinsu. Ga video Mu'azz na musu da hotuna. Sai lokacin su Hanoon dake ɗaki suka fito dan hayaniyar ta ishesu. Hanoon na ganin Dada a falo zaune yau Available taji farin ciki ya kamata. Shi ko Afeef tsaki yay ciki-ciki ya koma. Dayyan dama barci yake ko sallar magrib da isha'i bayi yay ba.
Received at 6:25 AMReaction       An yanka cake Nimrah ta cira ta nufi Mammah. Sai da ta durƙusa gabanta cike da so da ƙauna tana ruƙunƙumeta ta kai cake ɗin bakinta. Su Ammar suka saka dariya wai ko zata koma ciki ne irin wannan kanainaye Mammah haka. Dariya aka sanya, Mammah taci cake tana taya su. Saura data gutsira ɗin ta amsa itama ta bama Nimrah tare da shafa mata kai. “ALLAH ya ƙaro shekaru masu albarka Auta. Yasa daga yau kun ƙara hankali ke da Ruƙayya.”
      Sosai su Biebah ke dariya. Dada kansa sai da yay wani gajeren murmurshi da furucin Mammah ɗin. Amma yanda basu yake kallo ba sai ka rantse hankalinsa baya wajen. Nan ko sarai kallesu yake ta gefen ido. Musamman yanda Nimrah ta rungume Mammah sai da yaji wani sanyi da nutsuwa ta musamman na ratsa jikinsa. Yana son Mammah, yana kuma son wanda ke sonta.
        Nimrah ta sake ɗibar cake zata bama sauran Mu'azz da Ruky suka kalla juna. Dan anzo inda suke so ɗin. Aiko sai kawai Ruky ta kama hannun nata ta jata har gaban Dada. Nimrah ta waro idanu waje, Ruky ta harareta. Hakan kuma yayi dai-dai da ɗagowar Dadan ya kallesu jin suna tsaya masa a kai........✍️KIƊA A RUWA 3

40
Chapter 22 · 0% Book details