Sashe 70
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
........Suna haɗa idon tai ƙoƙarin kauda nata. Bai hanata ba, amma kuma bai ɗaga daga yanda ya rufeta da ingarman jikinsa ba. Idanu ya zuba mata a hankali, yana kallon yadda take hawayen da laɓe baki cike da ƙuruciya da annuri.
“Ki kalle ni mana ko sau ɗaya. Ina son ganin yadda idanunki ke rawa saboda ni.”
Kafaɗa ta maƙe masa. Ya sake matsar da fuskarsa gab da tata. Da wata murya data ƙara shigewa ya ce, “Ki daina ɓoye min kanki haka Ruƙayya. Domin ni ɗin nan naki ne.
Ba zan taɓa kallonki da wani ido ba face na ƙauna. Samunki a matsayin mata ya saka ni jin cikamakon burukana na duniya sun kai maƙura. Ina sonki, so irin wanda idan baki ya zauna faɗa ma duniya zata iya masa kallon na cika kauɗi”.
“To ka daina bani tsoro. Bana son wannan abun ALLAH Uncle.”
Murmurshi yayi mai armashi da yalwa. Kafin ya kamo fuskarta cikin tashi ya juyo da ita inda tashi yake.
“Buɗe idonki Baby...”
Batai musu ba ta buɗe idanun. Cikin nashi da launinsu ya canja gaba ɗaya suka shige. A hankali wasu abubuwa masu nauyi suka dinga fitowa a cikin nasan suna shiga natan....
“Ba tsoro nake baki ba ƘAUNA. Wannan shi ne auren. Ko baki son ki haifa mana mai sunan Abiy?”.
Karo na farko ta saki murmushi. Yanayinta da alamun jin kunya ta ce, “Ina so mana.”
“Yauwa ƴar gari. Ki bada kai kawai mu tafi farautar sa..”
Bata fahimci ina ya dosa ba, dan haka tasa hannu biyu ta rufe fuska da faɗin, “Muje to”.
Dariya ya sanya mai laushi. Tare da janye hannun nata ya rungumeta.....
££££££££££
Anan kam hankalin Ismat ne ya tashi kan abinda ya faru tsakanin Nabeeha da Rayhana. Ta ɗauki waya har zata kira Momyn su ta fasa. Akalar kiran ta maida kan Jiddah. Ko gaisuwa basuyi ba ta shiga zayyane mata abinda ya faru. Ita kanta Jiddan hankalinta ya tashi. Tace Ismat taje ta bama Rayhana wayar.
Kai mata tayi, koda Jiddah ta kama mata faɗa ƙunƙuni ta fara. Har abin ma ya bama Ismat mamaki. Badai tace komai ba ta bari har suka gama ta amshi wayar ta. Ganin Jiddah bata yanke ba ta kaita kunne. Nabeeha tace ta kaimawa itama. Ta samesu da Amimah, da farko ƙin amsar wayar ma tayi, sai da Ismat tasa hansfree Jiddah tace su Ismat ɗin su fita a ɗakin su basu waje. Daga ita har Amimah babu wanda yay musu. Duk suka fita suka bar Nabeeha da wayar.
Da ƙyar Jiddah ta samu Nabeeha tai mata bayanin duk abinda ya faru tun daga farko. Cikin takaici ta ce, “Aunty mi ya kaiki magana ta ALLAH? Sai fa kin cirema kanki yarinyar nan a zuciya kinyi abinda ke a gabanki zaki zauna lafiya. Idan kuma kikace zaki cigaba da haka zata koya ta fiki iyawa. Kuma yanzu baki da tabbacin saboda itan ya kashe miki waya. Da yace ki saka taki a canji sai ki saka ki gani idan bai kirarin ba. Aunty sai kinyi kamar zaki canja kuma sai ki birkice haba ni na rasa ma wannan lamari”.
“Ke baƙya ganin laifin yarinyar nan sam”.
“Ba laifinta bane bana gani, ina son ki riƙe mutuncinki ne da girmanki kawai. Sannan idan zaman su Rayhana zai zame miki damuwa ki tattarasu su koma gida mana. Ni banga amfanin wannan zaman nasu ba sam wlhy. Sunƙi fidda mijin aure ke kuma sunzo sun tare miki a gida har rashin kunya ya fara shiga. Badan mutanen gidan ma ba masu kawaici bane hatta shi Yaya Haysam ɗin sai ya nuna miki ai. Ko yaran nan sa hanaki zaman lafiya da daidaita al'amarinki.”
“Kin san dai Momy ce take sakawa su zo su zauna idan zatai tafiya. Idan inta barsu a gida basu da aiki sai kwana a club”.
“Hummm to ba haka suka zaɓa musu ba. Ƙiri da muzu Aunty Mamawo da Momy sun jingine aure da ƙuruciyarsu sun zaɓi yawon business ƙasashe-ƙasashe. Tunda sun fahimci matsalar yaran duk su maida su gaban iyayenmu maza mana. Ismat ba'an samu ta koma ba kuma yanzu ta sake dawowa”.
“Shi ke nan ki bari za muyi magana. Bari na saka wayar a canji naji kamar maganar mijinki”.
“Shike nan ai zan shigo dubaki ma nama su Mammah barka da tashin baƙi suma. Mu kwana lafiya”.
Bata tanka batun yima su Mammah barka da tashin baƙin ba ta yanke wayar kawai. Jiddah ta girgiza kanta. Tana mamakin irin wannan kishi na ƴar uwarta da take harda uwar miji. Ita gata nan ma tata uwar mijin sai abinda tace za'ayi akeyi amma abin bai taɓa damunta ba, a ganinta ta isa ne, koba komai taci darajar sunan uwa, itama kuma gasu nan a gabanta ta haifa. Bata fatan tayi abinda za'ai mata watarana....
%%%%%%%
Da ƙyar Dadah ya iya riƙe kansa saboda ƙamshin turaren da Nimrah ta saka yay masifar masa tasiri da tada ƙura. Dan kusan ƙarfe biyu dole yabar mata gadon yaje yay alwala yazo ya fara salla. Bai kuma kwanta ba har asubahi. Da ƙyar ya tadata saboda nauyin barcinta ya rakata har bayi tayo alwala. Shi ne ya jasu jam'i. Sun idar sukai azkar. Kusa da shi ta matso ta miƙa masa hannu da faɗin, “Barka da aduba GARKUWAR Little Shadow”.
Dadah ya saki murmurshin da bai shirya ba, tare da kamo hannun nata ya jawota jikinsa gaba ɗaya ya rungume. Cikin sake bashi wani mamakin ta sumbaci fuskarsa dai-dai kan gashin sajensa. Sai dai da sauri ta fice a jikinsa ta gudu a wajen tana dariya. Saman gado ta haye, taja bargo ta shige ciki har kanta.
Dadah ya bita da kallo murmurshinsa na ƙara faɗi da yalwa. Sai kuma ya ɗan cije lips kaɗan yana miƙewa shima ya nufi gadon. Wutar ɗakin ya kashe batare da yay magana ko yaɓata ba ya kwanta. Cikin ƙanƙanin lokaci barci yay awan gaba da shi.
Cikin barci wayarsa dake vibrating ta tashe shi. Hannu ya miƙa ya ɗauka tare da buɗe idanun da ƙyar. Ganin mai kiran ya sashi ɗagawa yana kaita kunne sa.
“MIJIN KWAILA”.
Kalmar da Nabeeha ta fara faɗa kenan cikin suɓutar baki. Dan duk yanda taso yi kamar yanda Jiddah ta faɗa sai da taso kwafsawar dai. Sai da kalmar ta fita ne ta rumtse ido tana dafe kanta. Shima juyawa yay ya kalla inda Nimrah ke kwance a kusa da shi gab. Idanunta a rufe suke dan haka ya yunƙura ya tashi da tunanin barci take. Sai dai abinda bai sani ba ta farka tun sanda wayar ta fara vibrating ɗin, kuma sarai taji abinda Nabeehan ta faɗa. Kai har ma kallon da Dadah ya juyo yay mata ta maze ne kawai.
Sauka a gadon sai ma ya tashi ya fita a ɗakin gaba ɗaya. Bai kula furucin farko datai ba ya amsa gaisuwar data koma yi. Yaji daɗin yanda tai masa gaisuwa cikin kwanciyar hankali, hakan na nufin ta fahimci abinda ta faɗa ɗin tayi kuskure kenan. Ya amsa mata da kulawa. Saboda shi mutum ne mai basar da abu. Ita ma kuma tasan hakan..
Yafi mintuna goma sha biyar yana wayar sannan ya dawo ɗakin.. Yana shigowa da Nimrah ya fara cin karo. Tana zaune a saman gadon hannunta dafe da kanta alamar yanzu ta farka. Inda take ya ƙarasa, ya zauna kusa da ita yana kama hannunta fata dafe kan nata da shi, ya maye gurbinsa da nashi. Kan yayi zafi sosai kuwa.
“Kan na ciwo ne?”.
Ya faɗa yana shafa mata shi a hankali. Jinjina masa kawai tayi, dan bata son yin magana. Bai damu ba ya kwantota jikinsa. Amma mi sai taja baya zaram har tana ture hannunsa. Mamaki ya kama shi, ya riƙota yana tambayar lafiya?.
Kanta ta kauda idanunta na cika da ƙwalla. Sai dai taƙi yin magana. Haushin kalaman Nabeeha dake cizon ransa ya sashi kausasa harshe wajen faɗin, “Bada Nimrah nake magana ba”. Dan a ƙarshen wayar dai faɗa sukayi ya dawo.
Duk da taji tsoro sai ta dake. Ta tura baki tana matso hawayen drama. “Dada babu komai fa, ciwon kai kawai na tashi da shi, zanje nayi wanka ya tafi.”
Rasa ma abin faɗa yay sai kallonta yake cike da nazari. Sai da ta yunƙura zata bar gadon ya sake riƙota. Zai ƙara rungumeta tai saurin ɗaukar filo ta saka a tsakkiyarsu. Cike da fitina take faɗin, “Ni wanka nace zanyi fa Dadah”.
Sai kuma tai shiru saboda yanda ya zuba mata idanu. Ya saki hannunta zai cire filon data saka masa a jiki dan bama ya son yin magana kasancewar ransa a ɓace yake kawai ta dira a gadon, sai hangota yay taje ƙofa bayi. Tsaki kawai yaja da dafe kansa. Sai kuma ya miƙe ya cire filon data bar masa yay wulli da shi........✍️
Hhhh anya Nimrah. Irin wannan kishi haka jama'a 🤣🤣🤣🚶🥱.
Karku damu mutane na, in sha ALLAHU daga yau nima zan fara wani shagwaɓaku da pages da izinin ALLAH. 💃💃
86
.........Ganin yanda Dadah yay wirgi da fillo Nimrah dake laɓe tana leƙensa ta ƙyalƙyale da dariya.
“Su Dadah mijin ƙwaila”.
Ta faɗa tana ƙara kwashewa da dariya, sai kuma ta nufi gaban mirror tana kallon kanta, tamkar mai magana da wani ta saki murmurshin takaici. “Zaki tabbatar da Mijinki MIJIN KWAILA ne Hajjaju Momy Nabeeha. Badai irin wannan wasan kike so muyi ba. Wlhy sai na rikita duniyar MIJINKI ta yanda sai kin raina wayonki. Da kince ai girma da arziƙi ne da na baki mamaki, dan zan girmamaki da matsayi na matar Dadah amma yanzu muje zuwa mai sa'a ya ɗauki wannan GWARZON...” ta sake sakin murmurshi...