← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 113

Sashe 62

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

........Idanu Dadah ya ɗan lumshe tare da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya sakamakon jinta a jikin nasa. Fuskarta ya ɗago. Duk yanda take mutsu-mutsu son maidawa ya hanata dama. Sai ma cije lips da yay kaɗan. Sannan ya ɗan ƙara matseta tare da faɗin, “Kina son tada rikici ko? Alhalin kin san bazaki iya ɗauka ba saboda yanayin da kike ciki gaki raguwa. Ki nutsu kada na kasa riƙe kaina zan iya aikata abinda zai saka a jigata fiye da farko, dan jiya komai tamkar wasan yara ne da sharar fage. Buɗe idanun ki”.
          “Dadah ALLAH ina jin kunya”.
      “Bayan kin gama ƙarar min da ruwan jiki jiya. Yanzu kuma kina tattaɓeni irin kina so aɗan baki ko kiss ko. Tom kawo lips ɗin”.
     “Naga Boni Dadah!! Ni wlhy ban faɗa ba”.
     Murmurshi yayi kaɗan, ganin tana fara maganar hawaye shaaa. Kwantar da ita yay kamar zai barta, sai yay mata rumfa. Rabin jikinsa ya ɗan kwanto a nata sakamakon hannunsa daya biyo takan jikinta yana shafa mata kai. Tamkar mai raɗa cikin zurfafa harshe ya bata amsa da, “Ba sai kin faɗa ba. Ina karantar kalmominki tun kafin ki furta......“
        Hannu ta saka ta rufe masa baki. Ya kama hannun ya riƙe tare da sumbatar sa.
           Baki ta tura tana sake runtse idonta dan sosai sumbar ta ratsa mata jiki. Dadah ya sake sakin ƙaramin murmushi tare da lakace mata hanci kaɗan.
     “Uhmm, thank you Baby”.
  Ya faɗa yana sauke lips ɗin nasa kan nata ya sumbata nan ma. Kaɗan ya ɗago ya kalleta, ganin yanda ta ƙanƙame jiki da runtse idanunta ya sashi sake maida lips ɗin da salo na musamman. Babu ko kunya ya shiga bata wani zazzafan sumba data saka mutsu-mutsunta dakatawa ta koma tsumar jiki. Babu arziƙi ta kai hannunta kan fuskarsa cikin son ceton kai. Sai kuma aka samu matsala kamar ta ƙarama Dadah ƙaimi ne. Dan wani salo na musamman ya shiga bi da ita da, ita kanta bata san akwai kalarsa ba. Shi karatun manya a kowane shafi da sabon salonsa ya yake zuwa. Nimrah ta shaida hakan a yau dan bata ma san ta sallama ba har hannun nata na kai-kawo a tsakanin wuyansa zuwa fuskarsa da kansa har kunne....
         Al-amarin neman rikicewa yayi, dan sai da takai Nimrah ta fara jerama Dadah kalmomin magiya da roƙo ga rawar jiki ta tashin hankali. Zufa ko duk da ac ya ta gama jiƙata sharaf. Da ƙyar ya iya janyewa daga gare ta. Ita ko sai uban hawaye take dan ta yamutsu a hanun manya. Ba kuma dan yana tausayinta ba, ba abinda zai hanashi kaiwa inda zuciyarsa ke ingiza shi.
      Tana samu ya barta zambar ta sauka a gadon, duk da zafi-zafi da take ji har yanzu bamai yawa ba ta daure, sai dai Alhamdullah jikinta ya daina uban ciwo irin na ɗazun. Tana jinta wani kalar fayau ne a jinta kamar takardar da iska zata iya ɗauka. Shi kam. Idanunsa na rufe har ta buɗe ƙofar bayi ta shiga ta maida ta rufe....

        ....★Koda ta maida ƙofar ta rufe a jikinta ta jingina. Yanda ƙirjinta ke hawa da sauka zai tabbatar maka a tsorace take sosai. Sannu a hankali take bama kanta nutsuwa. Sai da ta tabbatar numfashinta ya gama dai-daita sannan ta buɗe su tana mai kai hannu ta share laimar hawayen fuskarta. Tabbas dole ne ta ƙirƙiri abinda zai saka Dadah maidata gida, idan ba haka ba kunyarsa kasheta zatayi. Sannan al'amarinsa na bata tsoro. Jifa abinda yake faɗa. Wai sharar fage, duk azabar nan data sha za'ace sharar fage. To aiko bazata ma yarda ta zauna ba balle akai ga inda yake nufin. Da wannan tunanin ta bar jikin ƙofar zuwa wajen wanka.
       Jiki a sanyaye ta fara wankanta a ƙarƙashin shower ita a dole ta gama samo dabara. Sai da ta gama haɗama fuskarta kumfa dan tana tsaka da goga soso Dadah ya shigo bayin. Oho bata ji ko motsinsa ba. Shi ko da dama kamar ya ƙulla mata ne. Kansa tsaye ya buɗe wajen wankan alamar dama nan ɗin yazo.
       Aiko kaɗan ya hana zuciyarsa bugawa. Dan sai da ta tsaya cak na sakanni tamkar wanda akama tsawa sakamakon tozali da yay da ita, duk da ɗazun ya gama ganinta a yanda taken yanzu. Nimrah da taji kamar motsi ta ɗan dakata da goga kumfar fuskarta, sai kuma taji shiru. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Dan dama a ɗarare take. Sai yanzu ma take jima kanta haushin mi yasa bata sakama ƙofar key ba kodan ta bama kanta kwanciyar hankali, duk da tasan Dadah bazai shigo mata ba. Amma dai gara a raka, a tsare, a jira badan tsoro ba.
          Shi ko daya gama ƙare mata kallo tsaff da ƙyar ya iya ɗaga ƙafarsa da tai masa masifar nauyi ya ƙarasa inda take. Yanzu kam dai sosai zuciyarta ta harba. Dan tabbas jikinta ya bata akwai mutum a kusa da ita, kuma kamar ma ƙamshin Dadah. A rikice ta fara laluben makunnar shower za ta wanke fuska. Amma ina ta kasa taɓowa saboda rikicewa. Dadah dake kallon yanda take lalube ya lumshe idanu a slowly ya buɗe, sai kuma ya warware hannayensa dake harɗe a ƙirji ya kai kan makunnar shower ɗin ya kunna mata.
        Ai da masifar sauri Nimrah ta ce, “Azubillahi... Na shiga ɗari wa...w...waye?”. tai maganar da in ina tana sharce ruwan dake wanke mata fuska. Itama kamar shi ɗin, zuciyar tata neman fasowa tai. Taja baya a birkice tana faɗin, “Da...d...d..” tama gagara faɗa. Shi dai kallonta kawai yake, sai da taja bayan ne ya motsa kaɗan yana tarota da hannu ɗaya. Hakan yasa shi komawa ƙasan shower ɗin towel ɗin jikinsa ya warware ruwan ya fara sauka a kansa.
      Nimrah ta gigice, tamkar mai cutar asthma numfashin yay sama yay ƙasa a lokaci guda. Hannayenta duk biyu takai a fuska. Wani masifaffen juyi tayi har kamar zata zube a wajen da ƙoƙarin fasa masa ƙara....
       Tattausan tafin hannunsa ya ɗora kan bakinta. Ya kuma saka ɗayan hannunsa ya tallafota sosai ganin ta tafi zata zube ƙasa. Dolenta ta cafki hannayensa duk biyu dake tallafe da jikin nata tana ƙanƙame shi. Sai dai da gaske jikinta rawa yake na bala'i tamkar mai vibrating. Abu ne da bata taɓa kawo shi a tunaninta ba. Ai ita kam ta gama ganin boni. Yo miya rage mata idan ba tsaga bango ta shige ba kawai kowa ma ya huta. Zuciyarta ce ta sake hargitsatsewa.
       Tausayi yaji ta bashi saboda jin yanda zuciyarta ke motsi da bugawa da ƙarfi. Shi kansa yasan dole abin yay mata girma da yawa fiye da ɗazun. Amma gara ya cire mata duk wani ɓurɓushin kunyarsa ta tabbatar da ita fa yanzu matarsa ɗin ce. Komai yazo da shi zata cigaba da amsa, har ma tai masa fiye da yanda yake so.
       Cikin salon son bata nutsuwa ya kai hannu ya kashe shower ɗin, komai ya koma shiru sai saukar ɗumin hawayenta daya fara ji a hannunsa da suke ɗigowa. Ya kai lips ɗinsa kan kunenta. Cikin softly voice da ta fara ji daga garesa a jiya ya furta, “Relax... Little Shaddd. Bana son kuka. Ko baƙya son na tayaki wankan muje aljanna?”.
       Kanta ta shiga jujjuya masa. Cikin shashshekar kuka ta ce, “Dadah ina son aljanna sosai. Amma ka tausaya min, Kiddon ka ce fa. Na rantse maka bazan iya ba. Kai mai girma ne da daraja a gareni. Kai fa Dadah ne......”
      Sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda tuna amsar daya bata a jiya da tace masa shi uba ne... Shima dai ƙirjinta dake sama da ƙasa alamar da ƙyar take tattaro maganar tana gaya masa ya zubama ido, yanda takai ƙarshen zancen nata da rumtse ido ta gagara ƙarasawa kuma sai tama bashi dariya. Amma sai ya dake abinsa kai tsaye ya ce, “Zaki iya Nimrah. Naga hakan a cikin idanunki. Sannu a hankali zan cigaba da miki jagora har ki gane gari. Kunya na ƙara miki kyau ne, sai dai kar ta hana ki jin daɗin kasancewa tare da ni. Idan kina jin kunya ki jingina da ni mana, ni kuma zan zama garkuwarki har sai kin daina tsoron komai.”
       “Amma Dadah....”
   “Shiiii!!!”.
Ya faɗa cikin katseta. Daga haka bai sake bata damar yin magana ba. Sai ma ya sake kunna shower ɗin ruwan ya cigaba da sauka a jikinsu. Da kansa ya mata wanka tamkar ɗazun, bai kuma barta ba sai da ya sake gasata yanda ya kamata sannan yasa sukai alwala suka fita.
        Tana takawa sannu a hankali yana nazartar tafiyarta cike da kulawa. Bata iya haɗe ƙafa har yanzu yanda ya kamata. Sai dai akwai banbanci tsakanin ɗanzu da yanzu, dan haka ya ɗan samu nutsuwa. Duk yanda taso zamewa a wajen shafa mai bai barta ba. Shi da kansa yake mata komai. Sai dai babu magana sai kallo dake kashe ta da raunana zuciyarta. Yanzu ma dai rigarsa ta ɗazun jallabiya ya saka mata da hijabi, shima ya kimtsa ya jasu sallar Azhar.........✍️
78
Chapter 62 · 0% Book details