Sashe 98
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Koda Mole ya gama sanarma Dagger gafa dama sun samu akan tafiyar Sanda da bin bayansa da Malam Almu zai yi gobe sai Dagger ya ce, “Ai da wuya mu samu damar dama wannan damar nan a gobe Mole. Dan babbar matsala ce ta taso daga sama”.
“Matsala kuma Oga! Tami to?”.
“Kai matsalata da kai kenan har yanzu kanka a duhu yake. Sam kaƙi ajiye ƙauyancin nan naka. Shike nan idan ba muna tare ba bazaka bibiyi labarin da ƙasa da duniya ke ciki ba. To Oga Jush aka kashe. Labaran kwanaki na kisa a Dubai da yayta trading a duniya to shine”.
“Mun shiga uku mun lalace”.
“Kadai shiga uku ka lalace ɗan ɗaƙiƙiya. Wannan ai abun mi farin ciki ne. Ina da manyan sirrikan Oga Jush da wawayen nan basu sani ba. Dan haka zanyi amfani da su na wawashi rabona. Sannan na bar aikin kawo min Nimrah a hannunsu. Yanzu haka zaɓen sabon shugaba zasuyi, kuma ni ne nake son zama shugaban”.
“Kai kuma? To ta yaya? Haba Oga ka dinga magana irin ta masu hankali mana ba bugaggu ba. Duk waɗan nan ɗika-ɗikan masu faɗa ajin ne zaka kayar ka zama shugaban bayan kana a matsayin yaron su ne. Kaini raba ni, wani lokacin fa kaima daƙiƙin ne irina”.
“Kam babbar ...uban can, Mole ni kake kira daƙiƙi?”.
“Oga dan ALLAH kayi haƙuru, ALLAH na zata fa kalmar yabo ce ashe zagi ne”.
Rasa ma abin faɗa Dagger yayi saboda takaici. Anya ya taɓa zama da wawa irin wannan mutumin. Gashi ya zame masa kamar wani mayen karfe ko yaso rabuwa da shi sai ya kasa. Ya sha yi masa laifin daya kamata ace ya kashe shi amma baya iyawa. Kodan yana matsanancin son ƴarsa ne oho. Tsaki yaja faɗin, “Zamu haɗu zaka min bayanin waye daƙiƙi. Kuma ka jira goben zan kawo saƙo kaba Nimrah”. Yana gama faɗa ya yanke kiran ma gaba ɗaya. Mole ya kwashe da dariyar iskanci. Daga haka ya saka wayarsa aljihu ya koma ciki......
{∆}{∆}{∆}{∆}{∆}
A lokacin da su Ja'afar zasu fito Nimrah ta zaro jikinta ta biyo su. Dan taga ya dace tabar Dadah da matarsa, dan in har ta cigaba da zama tare da ita ga Dadah a tsakkiyarsu zuciyarta zata iya babbakewa. Musamman ganin take-taken Nabeeha ɗin. Dan yanzu babu kunya yana cikin gaisawa da ƴan uwansa ta wani je bayi ta ɗakko ruwa da towel wai na goge jiki.
Babu dai wanda ya tanka mata a cikinsu balle nuna mata ya fahimceta suka fito, shiyyasa itama taga ya dace ta bisu ta koma nata sashen. Dama ɗazun ta saki jiki ne ta zauna bisa umarnin Daddy Imran. Sannan kuma taga Nabeehan bata zo ba. Bai kuma dace ace sun barshi shi kaɗai ba.
Cikin sa'a suna fitowar ma sai ga Ruky. Rungume juna sukai sannan suka shige sashenta. Cike da zumuɗi Ruky tace, “Muje ciki da labari nake tafe. Dan Uncle Ammar ya bani bayani jiya”.
Ai Ruky ma bata ko rufe baki ba Nimrah ta ja hannunta suka shige. A bakin gado suka zauna.
“Ya akai bani nasha”.
“Humm Ninah da gaske fa Dadah yayi zaman prison, har na shekara takwas. Amma an kaishi ne bisa munafunci da sharri”.
Nimrah da zuciyarta ke bugawa da sauri ta ce, “Sharrin mi?”.
Tiryan-tiryan Ruky ta shiga bata labari kamar yanda Ammar ya bata. Tun daga yaƙin da sukai da ƴan ta'adda a wasu ƙauyuka har zuwa rasa rayuka, rikicinsa da Nabeeha da mahaifiyarta akan zuwa da ita. Da hukuncin daya yanke na aurenta, da yanda aka kama shi a munafunce, har zuwa kama Daddynsu shima. Kai-kawo da faɗi tashin da aka dinga yi na fitarsu. Shigar Janar siyasa da samun nasarar farko da fidda Daddy, cigaba da faɗi tashi har Janar ya sake zama shugaban ƙasa da fitowar Dadah. Bayan ya fito ne aka kaishi ƙasar waje.
“....ina ganin a lokacin ne yay jiyyar poising ɗin nan kenan. Kuma na fahimci da gaske suma basu san komai akan hakan ba.”
Nimrah ta zama kamar butun butumi, duk da Mammah ta taɓa bata labarin dalilin dawowata hannunsu amma banda na zaman Dadah a prison da haukan Nabeeha daya zama silar aurenta da Dadah... Sai da Ruky ta girgizata sannan ta kawo ajiyar zuciya.
“Mi kike tunani kuma?”.
“Humm babu komai. Mamaki ne ya gama kashe ni da tausayin Dadah. Ruky kenan akwai abinda ya kamata mu sani. Sannan ƙauyenmu yanzu babu kowa nawa dana sani a ciki? Shiyyasa ban taɓa ganin wani nawa ba a zahiri?”.
Hawaye masu zafi suka zubo mata. Itama Ruky hawayen tausayin ƴar uwar tata ne suka zubo matan. Ta ce, “Bazamu yanke hukunci ba Ninah. Ina ganin ki tambayi Dadah muji amsar da zai baki. Ni yanzu bara naje Uncle bai san na fitoba wlhy. Uncle Billa ne kawai ya kira shi nima na samo na gudo. Amma anjima zan dawo. Ko kuma mu haɗu a sashen Mammah”.
Tana gama faɗa bata jira amsar Nimrah ɗin ba ta miƙe ta fita da ɗan gudu. Sai Nimrah ɗin ma ta kasa tsaida ta. Da ga ƙarshe ma ta miƙe tai sallar azhar da ake kira. Koda ta idar sai ta zame ta kwanta a wajen tana hawayen da bazata iya tantance na minene ba.....
...★Sosai Nimrah tasha barci, dan bata tashi farkawa ba sai la'asar. Ita kanta tayi mamakin barcin nata, duk da dai dama akwai bashin na kwanaki da suka ci a Dubai, ga gajiyar yawon da suka sha da gurzar data dinga sha a hannun Dadah. Zafi taji cikinta na mata na yunwa, ta dafe shi tana yamutse fuska da tuna yau fa tea ne kawai a cikinta. Ɗazun Dadah har cewa yay ta zauna taci abinci tace zataje taci a falo, daga nan ne ma ta gudo daga sashen nasa tare da su Uncle's.
Wanka ta fara yi da alwala tai sallar la'asar, koda ta idar a wajen ta cigaba da zama tana cigaba da tunane-tunane ita kaɗai, tunanin kuma duk ya ta'allaka ne akan yanda zata tunkari Dadah yanzu da tambayoyi akan zuriyarta. Dan bata son ɗaga ma Mammah hankali. Wannan wasan tsakaninta da Dadah ne kaɗai. Kuma da shi zata buga shi. Sai batun shan ƙwaya, ya zama dole ta saka ma Nabeeha ido kenan itama. Tare da wannan Rayhana ɗin da ganin datai mata jiya ya kasa fita a ranta. Dan ba rami miya kawo rami to?..........✍️
113
........A anan ɓangaren Mammah kam baƙuwar bazata suka samu wato Hanoon. Dan kwatsam suka ganta babu zato babu tsammani. Kasancewar su Mammah ɗin ne a sashen kawai ta samu ƴar tarba. Dan su Ruky kowa na sashenta da mijinta kowa na shoshalewarsa weekend.
Mammah ta tambayeta ɗan uwanta Uncle Tasi'u da ƴan uwanta su Dayyan. Tace duk suna lafiya suna ma gaishe su. Daga haka ta shige tsohon ɗakin Biebah inda ta zauna wancan karon. Da kallo Mammah ta ɗan bita, dan sosai Hanoon ɗin ta rame mata a ido. Sannan tayi baƙi. Komai batace ba dai tai kiran Kulu tace su haɗama Hanoon ɗin abinci. Daga haka suka cigaba da hirarsu da Gwaggo Khadijah.....
))))))))))+((((((((((
A ɓangaren Dadah ma jikinsa Alhamdullah. Dan ya samu kulawa sosai daga Nabeeha. Duk da dai saida suka kusan haurawa sama saboda mitar mizai saka Nimrah ta rigata sanin baida lafiya data dame shi da shi, sai kuma laifin asuba dai da shima yaƙi barin ranta, sai batun Daddy Imran. Ita ta lura Imran munafuki ne. Dama ai ba ƙaunarta yake ba. Miye miye...
Sai da Dadah da yake jin tana neman ƙara masa ciwon kai yay mata tsawa da gargaɗin idan fa ba abinda ya dace tayi tazo yi ba zata iya kama gabanta baya buƙar hayaniya. Shi da ta tafi ta bari duk da tasan baida lafiyar baiyi mita ba sai shine zata zo ta dama. Taje ta samu Imran ɗin ko Nimrah ɗin suyi mana can tsakaninsu.
Wannan zantuƙa nashi sun sake ƙona mata rai da zuciya. Dan sai take ganin kamar ya goyi bayan Imran da Nimrah ne. Kuka ta sanya masa da faɗin, “Kaface haka tunda yanzu baka ganin kowa sai ita. Shi kuma bafadenta. Kuma da kake maganar na tafi na barka ai kai ne ka jawo naga. Tsabar son ka wulaƙantani da asubar fari dan zaka tashe ni a barci ka kama tashina da sunan yarinya. Saboda ni gangar jikina ce kawai a kusa da kai bana cikin zuciyarka. Waya sani ma ko tarayyar da kai da ni ita kake tunawa...”
“Nabeeha tashi ki fita a ɗakin nan kafin ranki ya ɓaci”.
“Wlhy ko zaka kasheni bazan fita ba. Dan nasan so kake na tafi ku kirata.”
Shiru yay mata daga nan bai sake magana ba. Itama sai ta share shi. Duk abinda dai yace yana buƙata tana tashi tayi masa. Har dai ALLAH yasa Magriba ta gabato. Ta taimaka masa yay wanka ya shirya. Dan sosai yana jin ƙarfi a jikin nasa, ciwon kan ma da sauƙi, sai dai can yake jinsa ƙasa-ƙasa.
Daga sallar magriba har isha'i a massalaci yayi su. Sai dai ana idarwa ya shigo gida saboda bawai ya gama jinsa normal gaba ɗaya bane.